Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ake samun yawan fashewar tankar man fetur a Najeriya?
Aƙalla mutum 33 ne suka mutu a fashewar tankar man fetur ta baya-bayan nan bayan kifewarta a titin Agaie zuwa Bida cikin ƙaramar hukumar Katcha a lardin Essa na jihar Neja.
Rahotanni sun ambato Aishatu Sa'adu, kwamandar hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar Neja na cewa tankar ta zame a kan titi, lokacin da direbanta ya yi ƙoƙarin kauce wa wani rami.
Bayanai sun kuma ce aƙalla mutum 40 ne suka ji raunuka a gobarar da ta tashi, yayin da aka taru domin kwalfar man fetur da ke tsiyaya daga tankar da ta faɗi.
Babban Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba-Ara ya ce da safiyar Larabar nan ƙarin mutum uku suka cika a asibiti, abin da ya sa alƙaluman mamatan ya kai 33 yanzu.
Ya ce tankar da ta faɗi ta taho ne inda ta gogi wata 'yar'uwarta da take giftawa a lokacin.
BBC ta ga hotuna da bidiyon da ke nuna mutanen da suka rasu sanadin raunukan ƙuna, wasu kuma na kwance a gadajen asibiti suna jinya.
Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na ranar Talata a Essan, nisan kilomita huɗu daga garin Badeggi.
Titin Bida a cikin jihar Neja ya yi ƙaurin suna kan lalacewa da yawan ramuka, ga kuma yawan ababen hawa da ke zirga-zirga.
A watan farko na shekarar nan ma, irin wannan fashewar tankar mai ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 98 a garin Dikko na ƙaramar hukumar Gurara a jihar ta Neja.
Haka zalika, aƙalla mutum 55 sun samu raunuka inda aka kwantar da su a babban asibitin Suleja da babban asibitin Sabon Wuse da cibiyar lafiya a matakin farko da ke garin Dikko.
'Kwasar ganima'
Hukumomi a jihar Neja sun ce lamarin ya ritsa da mutane da yawa ne saboda al'adar wasu mutane ta zuwa ɗiban man fetur da ke tsiyaya a duk lokacin da aka samu faɗuwar tankar mai.
Abdullahi Baba-Ara ya ce duk da dai "an yi ta faɗakarwa, an yi faɗakarwa a kan in haka ta faru mutane su daina zuwa kusa. Su daina zuwa kusa. Ba su ji ba!"
Babban daraktan ya ce mutanen yankin sun riƙa kwaso bokitai da baho da sauran mazubai, don ɗiban man fetur.
Ana cikin wannan al'amari ne, in ji shi, sai tankar ta kama da wuta.
Irin wannan kwasar mai wadda wasu suke kira "Cin ganima ko kwasar ganima" ta janyo mutuwar fiye da mutum 180 a watan Oktoban 2024, lokacin da gobara ta tashi a garin Majiya cikin ƙaramar hukumar Taura.
Mutane da dama a Najeriya suna fama da talauci, abin da kan sa wasu jefa rayukansu cikin hatsari a kan wani ɗan samun da ba zai kashe ƙishirwa ba.
Lalacewar hanya
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga al'ummar yankin Essa, inda ya bayyana lamarin da cewa wani abin takaici ne mai wahala da kuma tayar da hankali ga al'umma da gwamnatin Neja.
Sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Bologi Ibrahim ya fitar ta ce lamarin ya ritsa mutane da dama ne lokacin da suka tunkari motar a ƙoƙarinsu na kwalfar mai.
Shugaban ƙungiyar direbobin tankokin mai na jihar Neja, Faruk Mohammed Kawo ya ce fashewar tankar lamari ne mai tayar da hankali da ya ɗaiɗaita rayuka amma ana iya kauce masa.
Tankar man ta taso ne daga Lagos a kan hanyarta ta zuwa arewacin Najeriya lokacin da ta hatsari, ya ƙara da cewa sun ƙidaya haɗurra guda 30 da suka faru a wannan hanya kaɗai cikin wannan wata Oktoba.
Faruk Mohammed Kawo ya alaƙanta ƙaruwar haɗurran motocin da ake samu a kan tsananin lalacewar hanyar.
Jaridar Daily Trust ta ce irin waɗannan haɗurra sun faru a kan wanan hanta a baya.
Ta ce fashewar tankar da ta faru sakamakon taho-mu-gama da wata tirela da ta ɗauko matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 48 bara.
Rashin safarar man fetur ta bututu
Ƙasashen da suka ci gaba, hanyar sufuri ta bututun da ake shimfiɗawa a ƙarƙashin ƙasa ita ce hanya mafi inganci da sauƙin hatsari da ake amfani da ita wajen sufurin man fetur.
Sai dai a Najeriya, akwai ƙarancin bututan safarar man fetur musamman a tsakanin sassan ƙasar kamar kudu da arewaci.
Don haka, an fi amfani da motocin dakon mai wajen sufurin man, wanda yakan zama mai matuƙar hatsari a duk lokacin da aka samu tangarɗa ko hatsari a kan titi.
Rashin haƙurin direbobi
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Neja ta ce hatsarin na Essa ya faru ne lokacin da direban tankar man ya yi ƙoƙarin kauce wa rami a kan hanyar.
Babban Daraktan hukumar ya ce titin wanda ya lalace har yanzu yana fuskantar aikin sabuntawa daga hukumomi, don haka akwai buƙatar masu ababen hawa su yi matuƙar taka-tsantsan kuma su kasance masu haƙuri a wannan tsakanin.
"A maimakin a shiga rami a hankali, a fita, amma su suna ganin ai za su ɓata motarsu, to in suka kauce wa rami haka, yawanci sai ka ga motarsu ta faɗi," in ji Abdullahi Baba-Ara.