Hotunan yadda Musulmi suka yi bukukuwan Sallah a ƙasashen duniya

China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu matasan Musulmi a birnin Beijing na ƙasar China bayan kammala salalr Idi.
Lokacin karatu: Minti 2
Tehran, Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɓangare na mata da ke sallar Idi inda suka ɗaga hannayensu suna addu'o'i a birnin Tehran na ƙasar Iran.
Malaysia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu Musulmi ƴan ƙabilar Rogingya ke kokawa da wani bijimin sa domin su kayar da shi a yanka a matsayin layya, a birnin Kualar Lumpur da ke ƙasar Malaysia.
China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda Musulmi a birnin Beijing na China suka fara da ɗaga tutar China tare da rera taken ƙasar kafin fara Sallar Idi a ranar Sallah.
Beijin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sahun masallata a birnin Beijing ke gudanar da sallar Idi.
Tehran, Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗaruruwan masallata a ranar idi ke ɗaga hannu domin yin addu'o'i a birnin Tehran da ke ƙasar Iran.
Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu yara a Gaza ke murnar Sallah duk da halin yaƙi da suke ciki.
Niamey, Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda ake banƙare da gasa raguna a kan titunan birnin Niamey da ake kira Tareni a jamhuriyar Nijar.
Istanbul, Turkiye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmi sun taru a dandalin Sultanmahmet domin bikin ranar Sallah a birnin Istanbul na Turkiyya.
St. Petersburg, Russia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban Musulmi a sahun Sallar Idi birnin St. Petersburg na ƙasar Rasha.