Ƴancin Falasɗinawa da samun kujerar na-ƙi: Buƙatu huɗu da Najeriya ta gabatar wa MDD

Asalin hoton, Reuters
Najeriya ta gabatar da buƙatu huɗu da take neman cimmawa ga Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) yayin babban taron majalisar karo na 80.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya gabatar da jawabin ranar Laraba a madadin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Jawabin mai tsauraran kalamai ya ƙunshi gargaɗi ga majalisar kanta, inda Najeriya ta nemi ta aiwatar da wasu sauye-sauye "ko kuma tasirinta ya ragu yayin da lamurra ke faruwa a kan idonta".
Kazalika, shugaban ya soki MDD game da rashin ɗaukar matakai kan "wahalhalun da mutane ke sha" a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran yankuna, yana mai cewa hakan "na nuna gazawar al'umma baki ɗaya".
Wannan ne karo na biyu da Shettima wakiltar Tinubu a babban taron na MDD tun bayan kama mulki a watan Mayun 2023.
Daga cikin waɗanda suka yi wa mataimakin shugaban rakiya akwai Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar, da sauran jami'an gwamnati.
Bai wa Najeriya kujerar dindidin a Kwamitin Tsaro

Asalin hoton, State House
Yayin jawabin nasa, ana iya cewa mafi girman buƙata da Najeriya ta gabatar a gaban takwarorinta ita ce ta neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD.
Wannan buƙata ba sabuwa ba ce ganin yadda masu fafutika suka dinga neman a bai wa Afirka kujerar. Ƙasashe kamar Masar da Afirka ta Kudu da Habasha, duka suna da irin wannan burin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Dole ne Najeriya ta samu kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD," in ji Shettima.
"Ya kamata a aiwatar da hakan a matsayin wani ɓangare na gyaran da za a yi wa majalisar. MDD za ta dawo da martabarta ne kawai idan tana kallon duniya yadda take a yanzu, ba wai kamar a baya ba."
Shugaban ya kuma bayyana Najeriya a matsayin wadda ta sauya daga "ƙasa mai mutum miliyan 20 da aka yi wa mulkin mallaka ba tare da neman shawararta ba" zuwa mutum miliyan 236 da aka ƙiyasta za ta zama ta uku mafi yawan al'umma a duniya".
Kwamitin sulhu na da mambobi 15 jimilla. Biyar daga cikinsu (Amurka, Rasha, China, Faransa, Birtaniya) na da kujerar dindindin da ke ba su damar hawa kujerar na-ƙi kan duk wani ƙudiri. Sauran 10 ɗin kuma, akan zaɓe su ne duk bayan shekara biyu.
Ƙasashen 10 su ne Algeria da Denmark da Greece da Guyana da Pakistan da Panama da Korea da Saliyo da Slovenia da kuma Somalia.
Duk da cewa Najeriya ba ta da kujerar dindindin a kwamitin tsaro na MDD, amma ta taɓa zama mai kujerar je-ka na yi-ka har sau biyar a cikin kwamitin.
Shekarun da Najeriya ta samu irin wannan dama su ne 1966 zuwa 1967, da 1978 zuwa 1979, da 1994 zuwa 1995, da 2010 zuwa 2011, sai kuma 2014 zuwa 2015.
Ɗaukar mataki kan yaƙin Gaza

Asalin hoton, State House
A ɓangaren rikice-rikice, Tinubu ya nemi a kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, inda ya ɗauki matsaya takamaimiya.
A cewarsa: "Muna bayyanawa, ba tare da wata tantama ba, cewa kafa ƙasa biyu ne hanya mafi dacewa wajen samar da zaman lafiya ga al'ummar Falasɗinawa.
"Falasɗinawa ba ababen zubarwa ba ne a matsayin asara wajen neman rayuwa mai tsari. 'Yan'adam ne daidai da kowa a daraja, da ke da 'yanci da mutuncin da wasu daga cikinmu ba su ɗauka da muhimmanci."
Ƙudirin kafa ƙasa biyu manufa ce da akasarin ƙasashen duniya, ciki har da Amurka - kafin Trump ya hau mulki - suke goyon baya a matsayin daftarin da zai kawo ƙarshen rikici tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.
Najeriya ba ta taɓa sauya matsayarta ba kan wannan batu.
Yafe bashi

Asalin hoton, State House
A ɓangaren tattalin arziƙi, Shugaba Tinubu ya bayar da shawarar ɓullo da gyare-gyare a ɓangaren yadda ake hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen duniya.
Ya nemi a fito da sabon tsarin da zai dinga saka ido da kuma hukunta laifukan da suka shafi ci da kuma biyan bashi a tsakanin ƙasashen.
"Ina kira da a ƙirƙiro wani tsari na doka da zai dinga lura da bayar da bashi, kamar irin Kotun Duniya ta harkokin kuɗi, wadda za ta dinga bai wa ƙasashe masu tasowa damar guje wa wahalhalun tattalin arziki a fannin kayayyakinsu da suke samarwa kuma ake sarrafawa a wasu ƙasashe," a cewarsa.
Shugaban ya kuma jaddada buƙatar ɗaukar "matakin gaggawa domin yafe wa ƙasashe bashi - ba wai a matsayin sadaka ba sai domin hawa turbar da za ta amfane mu baki ɗaya".
Iko da albarkatun ƙasa
A gefe guda kuma, Tinubu ya nuna cewa albarkatun ƙasar da ke jibge a nahiyar Afirka su ne kan gaba wajen cigaban duniya baki ɗaya, abin da ya sa ya nemi ƙasashen su dinga samun iko kan ma'adanansu.
"Afirka - da ma Najeriya - na da ɗumbin ma'adanai masu muhimmanci da za su taimaka wa cigaban fasaha a nan gaba," in ji shi.
"Zuba jari a harkar haƙowa, da haɓakawa da ma sarrafa waɗannan ma'adanai a Afirka zai taimaka wajen hada-hadarsu zuwa ƙasashen waje, su rage rashin jituwa tsakanin manyan ƙasashe kuma su tallafa wajen samar da zaman lafiya.
Ya jaddada cewa ƙasashen da ke samar da ma'adanai masu muhimmanci "dole ne su dinga amfana daga ma'adanan - kamar a ɓangaren zuba jari, da aikin haɗin gwiwa, da samar da ayyukan yi".
A cewarsa: "Duk lokacin da muka fitar da kayayyakin haɗa abubuwa zuwa ƙasashen waje, sai a shiga faɗuwar gaba, da rashin natsuwa, kuma a yi ta shiga rashin tabbas."










