Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa birnin Goma ke da muhimmanci ga ƴan tawayen M23
- Marubuci, Kaine Pieri
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo da ya kwashe gwamman shekaru yana fama da fada a lokuta mabambamta, ya sake zama cibiyar yaki tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen M23.
Yaki tsakanin bangarorin biyu ya munana a farkon shekarar nan, hakan ya tilasta wa farar hula sama da 400,000 tserewa daga muhallansu a cikin shekarar nan kawai.
Shin wane muhimmanci birnin na Goma ke da shi a ƙasar?
Su wanene ƴan tawayen M23?
Sama da shekara 10 ke nan da kungiyar masu dauke da makamai ta M23 suka balle daga cikin sojojin gwamnatin Congo, kan ikirarin bai wa 'yan kabilar Tutsi kariya wanda suka jima su na korafi akansu, wajen nuna musu wariya da yanke musu hukuncin zalunci.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce gwamnatin Rwanda da ke makoftaka, na bai wa 'yan tawayen M23 kariya, amma Rwanda ta musanta hakan.
A baya-bayan nan Rwanda ta ce hukumomi a Congo na aiki tare da wadanda suka kitsa kisan kare dangin da kabilar Hutu suka yi wa kabilar Tutsi a Rwanda a shekarar 1994,
A shekarar 2012, 'yan tawayen sun mamaye birnin Goma na kwanaki 10, kafin daga bisani su fice daga ciki bayan matsin lambar kasashen waje.
Wannan ya janyo 'yan tawayen M23, su ka sha akaye aka ci su da yaki wanda dole suka tsere suka bar sojojin Congo da dakarun wanzar da zaman lafiya da yin nasara.
Daga nan mayakan M23 su ka amince su koma cikin rundunar sojin kasar kan alkawarin za a bai wa kabilar Tutsi dukkan kariyar da suke bukata.
Sai dai a shekarar 2021, lamura suka sauya inda 'yan tawayen suka sake daukar makamai, suka fake da cewar an karya alkawarin da ke tsakaninsu da sojin gwamnatin Congo.
Tun daga wannan lokacin 'yan tawayen M23, ke ci gaba da mamaya da karbe iko da yankuna, da kauyuka d garuruwa daban-daban na kasar. Kwararru a MDD sun ce sojojin Rwanda 4,000 ne ke taimakawa 'yan tawayen M23 a yammacin Congo.
Wurin da Goma yake
Birnin Goma mai iyaka da kogin Kivu a arewacin Congo, ya kasance wurin da idanu ke kai ko dai ta fuskar 'yan siyasa da 'yan kasuwa da sauransu.
Birnin mai dauke da sama da mutum miliyan daya, ya kasance fitacce a yankin baki daya. Kasan wurin na da albarkar noma, kuma ta na da daddaen tarihi a matsayin hanyar da fatake ke amfani da ita wurin gudanar da kasuwanci tsakanin ta da makofciya Rwanda.
Birnin Goma cike ya ke da albarkar ma'adinai, akwai garuruwa da dama da ake gudanar da hakar ma'adinai a sassan shi. Ma'adinan sun hada da danyen gwal, da tama da karafa da ake tsananin bukata a kasuwannin duniya. Akwai hanyoyin mota da na jirgi da ake gudanar da safarar ma'adinan, ko da yake MDD ta samar da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin, lamarin da ya ja hankalin kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje da ofisoshin diflomaisiyya suka bude ofisoshinsu a birnin.
Arzikin da ke a Goma
Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ita ke samar da rabin Kobat (Cobalt) da ake samarwa a duniya, da sinadarin lithium da ake yin batiran wayar salula, da motoci masu aiki da lantarki da yawancin taba sigari na zamani.
Ya yin da duniya ke kokarin rage gurbataccen hayaki, ta hanyar komawa amfani da makamashi mai inganci, ana samun karuwar bukatar ma'adinai irin wannan domin inganta fannin.
Barazanar da ake fuskanta a yanzu ta barkewar sabon yaki a kasar, hakan zai shafi fitar da ma'adinan zuwa kasashen ketare, hakan na janyo karancin abubuwan da ake amfani da su a fannin kimiyya da fasaha da samar da makamashi maras gurbata muhalli ga masana'antu.
Me zai faru idan birnin Goma ya faɗa hannun ƴan tawayen M23?
A shekarar 2023, Shugaba Félix Tshisekedi, ya ce ''Goma ba za ta taba fadawa hannun 'yan tawaye ba." Alkawarin da ya dauka ne ya ci gaba da rike birnin na Goma da katange shi daga 'yan tawayen M23, hakan na nufin idan Goma ta kubuce daga hannun shi to zai janyo nakasu a sake zabensa a matsayin shugaban kasa.
Harwa yau, babu kyakkyawar alakar diflomasiyya tsakanin Congo da makofciyarsu Rwanda, hakan ya sa babban magatakardar MDD Antonio Guterres gargadi kan yakin na yanzu ka iya janyo tashin hankali da rashin tabbas a yankin baki daya.
Ya yin da mayakan 'yan tawayen na M23 ke ci gaba da dannawa gabashin Goma, dubban farar hula a kauyuka da dama na ficewa daga gidajensu, inda suke nufar asibitin Goma, domin neman mafaka wanda kawo yanzu ya yi cikar kwari.
A bangare guda, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta yi gargadi kan karin hadarin da farar hula za su fada idan aka ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin Congo da 'yan tawayen M23.
Kungiyar ta kara da zargin dukkan bangarorin biyu da take hakkin dan adam, da cin zarafin farar hula.