Ba za mu lamunci tsoma bakin ƙasashen waje a zanga-zanga ba - Gwamnatin Najeriya

Yusuf Maitama Tuggar

Asalin hoton, @YusufTuggar

Bayanan hoto, Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ne ya jagoranci ganawa da jakadun ƙasar waje a Najeriya game da zanga-zanga kan tsadar rayuwa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta amince da katsalandan ɗin ƙasashen waje ba a zanga-zanagr da ake yi a kasar kan adawa da tsare-tsaren gwamnati.

Masu shirya zanga-zangar sun ci alwashin ɗaukar kwana 10 suna gudanar da ita a duka faɗin bayan farawa ranar 1 ga watan Agusta.

Da yawa daga cikin masu zanga-zangar a jihohin arewacin ƙasar sun dinga ɗaga tutocin Rasha, inda suka dinga kira ga ƙasar ta kawo musu ɗauki kan tsadar rayuwa kamar yadda ta yi a ƙasashen Nijar - mai maƙwabtaka - da Mali, da Burkina Faso.

Tuni rundunar sojin ƙasar ta bayyana ɗaga tutar Rasha a matsayin "cin amanar ƙasa".

Gargaɗin na baya-bayan nan ya fito ne daga Minista Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar, inda ya ce "babu wata ƙasa da za ta amince da wannan".

"Gwamnati ta yi iyakar ƙoƙari don ta ga an yi zanga-zangar nan ta lumana, amma abin takaici hakan ba ta faru ba saboda akwai wasu a gefe suna neman su yi amfani da 'yancin ɗan'adam wajen gurguntar da ƙasar ko kuma gwamnati," a cewarsa yayin taron da ya gudanar da jakadun ƙasar waje a Abuja ranar Laraba.

Ministan ya fara ne da yaba wa haɗin kan da jami’an kasashen waje da ke aiki a Najeriya suke ba su, sannan ya fito ƙarara ya yi bayani cewa gwamnatin Najeriya za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk kasar da aka samu da hannu wajen taimaka wa masu zanga-zangar.

Sai dai ƙasar ta Rasha ta nesanta kanta daga masu ɗaga tutarta da kuma neman ta shiga batun siyasar ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yake amsa wasu tambayoyi daga jakadun, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta gama sanin jagoroin zanga-zangar ba ballanatana ta fara tattaunawa da su.

"Mun yi ta bayani cewa gwamnati na son ta san ko su wane ne, amma kuma wasu ƙalilan da suka fito ai ka ga gwamnati ta tarɓe su," a cewarsa.

Da wakilin BBC ya tambaye shi ko ina aka kwana game da tattaunawar da suka ce suna su yi, sai ya ce: "Shiri yana nan, tun kafin a fara muka fara shiryawa. Da a ce sun zo an tattauna da ƙila ba a yi wannan zanga-zangar ba ma."

Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya, Peter Afunanya, ya ce sun rufe asusun bankunan wasu ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare da suke zargin suna ɗaukar nauyin masu zanga-zangar.

Yayin taron, wakilin Amurka a Najeriya ya nemi a ba su bayanan ‘yanƙasar da ke zaune a ƙasashen waje da gwamnati ta ce tana sa musu ido saboda zargin ɗaukar nauyin masu zanga-zanga, a nan ma sai Ministan yada labaran ya ce:

"Ni ban ma san su ba, kuma bincike ake yi a kansu saboda haka ba zan zo nan na faɗi sunayensu ba."

Zuwa yanzu rundunar sojin Najeriya ce kaɗai ta amince cewa wani sojanta ya kashe wani matashi bisa kuskure yayin zanga-zangar da aka yi a garin Zariya na jihar Kaduna, yayin da babban sufeton 'yansanda ya ce dakarunsu ba su harba harsasai masu kisa ba.

Sai dai rahoton ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ya ce an kashe aƙalla mutum 13 yayin zanga-zanga.

Kazalika, kamfanin tsaro na Beacon Cunsulting ya ce an kashe masu zanga-zanga akalla 24 daga ranar 1 ga watan Agusta lokacin da aka fara zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Mun kama 'yanƙasar Poland bakwai - Jami'an tsaro

Jami'an tsaro na farin kaya a Najeriyar sun ce sun kama 'yan ƙasar Poland bakwai bisa zargin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zangar a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Peter Afunanya, ya faɗa yayin taron na ranar Laraba cewa sun kama su ne lokacin da jami'ansu ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro.

Sai dai bai yi ƙarin bayani ba game da ko su wane ne, yana mai cewa amma ba farautar 'yanƙasar ta Poland a Najeriya suke yi ba.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito jakadan Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski, yana tabbatar da kamen yayin ganawar.

"An kama su kwana biyu da suka wuce a Kano, abu na ƙarshe da na ji shi ne ana shirin kawo su Abuja a jirgi," in ji shi.

Sai dai ya ƙi yin ƙarin bayani lokacin da Reuters ya tuntuɓe shi.