Ma'aikatan jinyar ƙyandar biri a Kongo na aiki cikin gajiya da fargaba, kamar yadda BBC ta gani

MPOX

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Bayanan hoto, Ma'aikatan asibitin da ke Lwiro, wanda a yanzu ya zama cibiyar kula da cutar mpox, sun yi matuƙar gajiya
Lokacin karatu: Minti 6

Ma’aikatan lafiya da ke kan gaba a yaƙin da ake yi da cutar ƙyandar biri ta mpox a gabashin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kongo, sun shaida wa BBC cewa sun ƙosa su samu alluran rigakafi domin daƙile yaɗuwar cutar.

A wata cibiyar kula da lafiya a lardin Kivu ta Kudu da BBC ta ziyarta a yankin da cutar ta ɓulla, sun ce majiyyata na ƙaruwa a kowace rana - musamman jarirai - kuma akwai ƙarancin kayan aiki.

Mpox cuta ce mai saurin yaɗuwa, kuma ta kashe mutane aƙalla 635 a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kongo a bana.

Kodayake an yi jigilar alluran rigakafi 200,000, da Hukumar Tarayyar Turai ta bayar zuwa babban birnin ƙasar, Kinshasa, a makon da ya gabata, amma har yanzu ba a samu kai wa ɓangarorin da dama a wannan ƙasa mai fadi ba - kuma za a iya ɗaukar makonni da dama kafin su isa Kivu ta Kudu.

Emmanuel Fikiri, wani ma'aikacin jinya da ke aiki a asibitin da aka mayar da shi cibiyar kwararru don shawo kan cutar, ya shaida wa BBC cewa: "Mun samu labari daga shafukan sada zumunta cewa an riga an samar da allurar rigakafin."

Ya ce wannan shi ne karo na farko da ya yi jinyar masu cutar mpox kuma a kowace rana yana jin tsoron kamuwa da ita, akwai kuma haɗarin zai yaɗawa ƴaƴansa masu shekaru bakwai da biyar da ɗaya.

“Kun ga yadda na taba majinyata domin aikina ne na ma’aikacin jinya. Don haka muna roƙon gwamnati ta taimaka mana ta hanyar fara yi mana allurar.”

Abin da ya sa za a ɗauki lokaci kafin a yi jigilar alluran shi ne dole ne a ajiye su a wuri mai sanyin gaske domin kada ƙarfinsu ya ragu, kuma ya kamata a kai su yankunan karkara da ke Kivu ta kudu kamar su Kamituga da Kavumu da kuma Lwiro inda ɓarkewar cutar ta yi ƙamari.

Rashin ababen more rayuwa da rashin tituna masu kyau na nufin cewa dole ne a yi amfani da jirage masu saukar ungulu domin a iya jigilar alluran, wanda hakan zai ƙara masu tsada a ƙasar da ke fama da matsalolin tattalin arziki.

A cibiyar lafiya ta al'umma, Dokta Pacifique Karanzo na fama da gajiya da rashin kuzari sakamakon kai komo da yake ta yi tun da safe.

Duk da yana sanye da takunkumi, ina iya ganin gumi na kwararowa a fuskarsa. Ya ce yana jin takaicin ganin majinyata suna kwance a gado ɗaya.

"Za ku ga har ma akwai marasa lafiyan da ke kwana a ƙasa," in ji shi, baƙin cikinsa na bayyane a fili.

“Ɗan agajin da muka samu shi ne ɗan maganin da muke bai wa marasa lafiya da kuma ruwa. Dangane da sauran kalubalen, har yanzu ma'aikata ba su da wani ƙwarin gwiwa."

MPOX

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Bayanan hoto, Ana samun ƙaruwar jarirai masu fama da mpox a asibitin al'umma na Lwiro
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata matsala kuma, in ji shi, ita ce babu isassun kayan ma'aikatan lafiya za su sanya domin su kare kansu.

''Muna iya ƙoƙarin mu ga cewa mun kula da marasa lafiya ba tare da mun sanya kawunanmu cikin haɗarin kamuwa da cutar ba.''

Daga ka shiga asibitin al'umma na Lwiro, wanda ke da nisan sa'a guda daga babban garin kudancin Kivu, Bakavu, abu biyu za ka fara cin karo da su.

Na farko shi ne ƙarar koke-koken jarirai. Na biyu kuma shi ne wani irin wari sakamakon haɗuwar fitsari da kuma ruwa da ke tsaye a wuri guda.

Asibitin na fama da mastalar ƙarancin ruwa, wanda hakan ke nufin dole su yi tsumulmuar ɗan ruwan da suke da shi da suka ajiye a cikin jarkokin da ke ƙarƙashin gadajensu.

Cikin makonni ukun da suka gabata, asibitin da ya kamata a ce yana kula da majinyata 80 a kowane wata ya samu kwararowar marasa lafiya kusan 200.

“Abin baƙin ciki ne ganin ɗana na fari yana fama da wannan mummunar cutar. abin yana matuƙar sosa min zuciyata,” in ji Faraja Rukara mai shekaru 18.

Ɗanta, Murhula, a halin yanzu shi ne mai mafi ƙarancin shekaru da ke fama da cutar mpox a asibitin - yana da makonni huɗu da haihuwa ne kacal. Wannan shi ne karon farko da ita, kamar sauran mutane da yawa a nan, ta ci karo da mpox, wanda ƙwayarta ke dangi ɗaya da cutar agana (small pox).

Cutar na haifar da raguwar sha’awar cin abinci, wanda ke haifar da ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin kananan yara.

A wani ɗaki da ke makwabtaka da su, mata da yara da dama - kusan 20 - suna cunkushe a ciki, suna raba gadaje bakwai kacal da katifa biyu da aka shimfida a ƙasa.

An dai sami maijinya ta farko da ta warke daga cutar a asibitin, ita ce Amenipa Kabuya mai wata 10 da haihuwa. Amma ba da daɗewa ba bayan an sallame ta, mahaifiyarta, Yvette Kabuya, ta dawo asibitin sakamakon ita ma ta kamu da cutar.

Cutar na matuƙar yin illa ga jikin ɗan'adam inda ake samun wasu ƙuraje masu raɗaɗi, da zazzabi da raguwar nauyi sakamakon rashin cin abinci. hakan na nufin mutane suna matuƙar zaƙuwa kan su sami allurar rigakafin, wanda lamari ne da ba a saba gani a wannan yankin da inda a baya aka nuna ƙyamar shirye-shiryen rigakafi da aka ƙaddamar a baya.

Beatrice Kachera, ƴar shekara 50, tana shafa kuncin jikarta ƴar shekara uku wanda ta garzaya da ita asibitin a gurguje: “Kwatsam na ga yarinyar ta fara nuna alamun rashin lafiya, ban ma san sunan cutar ba.

“Ba za mu tsaya muna kallo har sai yara har ma da manya sun mutu ba. A Kawo mana alluran rigakafin,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

Beatrice Kachera

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Bayanan hoto, Beatrice Kachera, wadda jikarta ke fama da mpox, ta ƙosa ta ga an fara fitar da allurar rigakafin

Sai dai wasu na fargabar rikicin da ake fama da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo tsakanin sojoji da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, musamman ƴan tawayen M23, zai kawo cikas a ynƙurn yaƙi da cutar.

Dr Gaston Bulambo, shugaban sashen kula da lafiya na lardin Kivu ta Arewa ya shaidawa BBC cewa "Rikicin na yin tasiri matuƙa a shirin rigakafin gaba ɗaya."

“Ba wai kan allurar rigakafin cutar ta mpox ba ne kwai, amma duk shirye-shiryen rigakafi suna fuskantar ƙalubale saboda matsalolin jigilar alluran rigakafin zuwa cibiyoyin kiwon lafiya. Wannan ya faruwa ne saboda matsalar rashin tsaro”.

Gwamnan Kudancin Kivu, wanda ya fito daga Lwiro, ya shaida wa BBC cewa ƙazamin fadan ya kori mutane da dama daga gidajensu inda suka kwararo cikin lardinsa, wanda hakan ke ƙara ta'azzara yaɗuwar cutar.

Jean-Jacques Purusi Sadiki ya ce "Muna karɓar dubban ƴan gudun hijira, kuma har yanzu muna fama da wasu batutuwa da dama."

"Ana amfani da kaso mai yawa cikin kuɗaɗen da ke akwai wurin tunkarar yaƙin da ke gudana, inda ake sayen makamai, da kuma ciyar da sojoji," in ji shi.

"Ƙasar na asarar maƙudan kuɗaɗe wajen ƙoƙarin magance wannan rikici, maimakon amfani da waɗannan kuɗaɗen wurin bunƙasa ababen more rayuwa ciki har da ɓangaren lafiya."

MPOX

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Bayanan hoto, Asibitin Lwiro ya cika maƙil da majinyata wanda suka kamu da cutar

Duk da haka, gwamnan ya yi imanin cewa ƙungiyoyin ƴan tawayen ba za su kawo cikas ga jigilar alluran rigakafin ba saboda mpox na addabar mutane a yankunan da suke iko.

Ya ce gwamnati na yin iya ƙoƙarinta don samawa likitocin abin da suke buƙata: “A cikin kwanaki biyu masu zuwa, zan je Lwiro da kai na. Zan ba da abin da ke akwai dangane da taimakon gaggawa ga jama'a, har sai gwamnati a Kinshasa ta iya ba da ƙarin tallafi daga na ta ɓangaren."

Hukumomin ƙasar sun ce za a fara yin alluran rigakafin a watan Oktoba, inda za a fara da yara ƴan ƙasa da shekaru 17, da kuma waɗanda suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar.

Gwamna Purusi Sadiki ya haƙiƙance cewa za a iya daƙile ɓarkewar cutar a lardinsa: “Batun jajircewar siyasa ne. Ina da yaƙinin cewa za mu yi nasara.”

Wani ra'ayi ne da ya bambanta daga na likoitoci kamarsu Dr. Karanzo a asibitin Lwiro, amma duk da haka suna ɗan farin cikin cewa ana ƙara samun wayewar kai game da cutar Mpox a yankunansu.

Alamu sun nuna cewa mutane na garzayawa asibiti da zaran sunfara ganin alamun cutar maimakon fara zuwa wurin masu ba da maganin gargajiya, wanda ke nufin har yanzu asibitin bai sami asarar rayuka ba.

Amma yayin da aka samu mutum 5,049 da suka kamu da cutar tun farkon wannan shekarar a Jumhuriyar Dimokraɗiyar Kwango, ma'aikatan asibitin na ganin cewa dole ne a ƙara hanzari kan samar da abubuwan da ake buƙata.

Sai an haɗa shirin rigakafi, da samar da magunguna, da kuma sauran kayan aiki da za su taimaka wa mutane musamman ta ɓangaren tsaftar jiki da muhalli ne za a iya magance yaɗuwar wannan cutar.