Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka da Isra'ila ne suka kitsa rushewar gwamnatin Assad - Iran
Jagoran addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zargi Amurka da Isra'ila da hannu a kifar da gwamnatin tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad.
A cikin wani tsokaci da ya yi, Ayatollah ya kuma ce faɗuwar gwamnatin Assad ba za ta raunana ƙarfin Iran ba.
Haka nan kuma ya yi zargin cewa akwai hadin baki da wata ƙasa "maƙwafciyar Syria" wajen kitsa lamarin, sai dai bai bayyana sunan ƙasar ba.
Ita kuwa Rasha ta bayyana kare lafiyar ƴan ƙasarta da ke Syria a matsayin "abu mai matuƙar muhimmanci", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, TASS ya ruwaito.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Rasha, Maria Zakharova ta ce gwamnatin Rasha na tuntuɓar hukumomin Syria domin tabbatar da hakan.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan tawayen HTS suka karɓe mulki da ƙasar Syria bayan tserewar shugaban ƙasar Bashar al-Assad.
Zuri'ar Assad ta yi mulkin kama karya na tsawon shekara 53 a Syria. Yanzu dai mulkin ya zo ƙarshe.
Shugaba Bashar al-Assad ya karɓi ragamar mulki ne a 2000, bayan mahaifinsa ya yi mulkin aƙalla shekara 30.
Shekara 13 da suka wuce ya yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe masu zanga-zangar lumana, lamarin da ya sauya zuwa yaƙin basasa da ya ɗaiɗaita ƙasar. An kashe mutane fiye da rabin miliyan, kuma an tilasta wa wasu miliyan 12 barin muhallansu.
Amma a ranar Larabar makon da ya gabata, wata ƙungiya mai rajin addinin Islama, Hayat Tahrir al-Sham (HTS) ta yi nasarar ƙaddamar da hari mai muni a arewa maso yammacin ƙasar, bayan ta yi haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyin tawaye.
Ƴan tawayen sun ƙwace birni na biyu mafi girma a Syria, Aleppo, sannan suka danna kudanci zuwa babban birnin ƙasar Damascus, suka kuma fi ƙarfin dakarun Syria.
Ƴan Syria da dama sun ce sun shaƙi iskar ƴanci yayin da wasu ke bayyana damuwa game da abin da zai faru nan gaba.
An shafe shekaru ana sa ran cewa yaƙin Syria ya zo ƙarshe bayan gwamnatin Assad ta karbi iko a mafi yawan biranen Syria, kuma ta samu nasarar yin haka ne da taimakon Rasha da Iran da kuma ƙungiyoyin tawaye da Iran ke marawa baya.
Gwamnatin ta yi nasarar riƙe manyan wuraren da aka yi rikicin, amma mafi yawan sassan ƙasar ba su a hannun gwamnati.
Daga cikin su akwai arewaci da gabashin ƙasar da ke hannun mayaƙan ƙurdawa masu samun goyon bayan Amurka, da ake kira Syrian Democratic Forces (SDF).
Yankunan da ƴan tawayen suka mamaye na ƙarshe kafin yanzu su ne Aleppo da kuma Idlib da ke kusa da Turkiyya kuma mutane aƙalla miliyan huɗu ke rayuwa, sai dai mafi yawan su suna zaman gudun hijira ne.
Mayaƙan HTS ne suka mamaye yankunan, amma suna haɗaka da wasu ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da suke zaune a yankunan.
Akwai kuma wata ƙungiyar ƴan tawayen da Turkiyya ke goyon baya mai suna Syrian National Army (SNA) wadda itama ta ke riƙe da wasu sassa.