Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jagororin ADC sun ce ba gudu ba ja da baya duk da harin da ake kai musu
Jamiyyar hamayya ta ADC a Najeriya ta yi zargin cewa ana hana mambobinta yin taruka a wasu jihohin kasar, lamarin da jagororinta suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Shugabannin jam'iyyar na kasa sun bayyana hakan ne a wani taro da suka yi a Kaduna, ranar Alhamis, inda suka bukaci da a gaggauta gudanar da bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a hare-haren da aka kai wa wasu 'ya'yan jam'iyyar a jihohin Kaduna, da Kebbi da kuma jihar Katsina, lamarin da ya kai ga jikkata wasu 'ya'yan jam'iyyar.
Tawagar shugabannin ta ce ta ziyarci jihar ta Kaduna ne domin jajanta wa reshenta na jihar a kan harin da wasu gungun mutane suka kai wa 'yan jam'iyyar da makamai a lokacin da suke wani taro a makon da ya gabata, kuma ta ce wannan ba zai karya mata guiwa ba.
'Yan tawagar sun kuma yi zargin cewa sun gamu da cikas a yunkurinsa na ganawa da mambobin na jihar Kadunan a sakatariyar jam'iyyar da ke jihar.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal na daga cikin tawagar shugabannin na ADC da suka ziyarci jihar ta Kaduna, inda ya yi wa BBC bayani kan makasudin ziyarar tasu da ta danganci jajantawar harin da aka kai wa mambobin nasu na Kaduna.
Tambuwal ya kuma yi bayani kan cikas din da suka ce sun samu wajen halartar inda suka tsara za su jajanta wa 'yan jam'iyyar tasu na jihar ta Kaduna da aka kai wa hari.
''An ce kwamishinan 'yansanda ya fito da wata takarda ya nuna ba tare da ya ba jami'an jam'iyya wannan takarda sun karanta ba, cewa an samo oda daga kotu an hana a je wannan wuri inda muka zo mu yi wannan zaman.
'' An hana mu zama a wannan wurin to shi ya sa mu a matsayinmu na shugabanni mun yarda da bin doka shi ya sa muka zo gidan daya daga cikin jagororinmu, Mallam Nasir El- Rufai don mu gabatar da alhininmu,'' in ji shi.
Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya kuma ce: ''Bayan ma abin da ya faru a nan Kaduna kun ga abin da ya faru a jihar Kebbi kuma ga abin da ya faru a jihar Katsina.''
''Wannan abin takaici ne a ce ana amfani da matsayi irin wannan na amana ana kuntata wa talaka da kuma sauran wadanda ya kamata a ce an ba su kariya,'' in ji shi.
Shi ma da yake tsokaci ga BBC a kan lamarin, tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce babu dalilin da zai sa a hana jam'iyyar taruka da mambobinta.
Ya kara da cewa ba inda tsarin mulkin Najeriya ya ce sai an sanar da 'yansanda kafin a gudanar da wani taro na siyasa.
''In kana son ka gaya ma 'yansanda don kana jin tsoro za a iya samun wata matsala ta tsaro za ka iya gaya musu amma wannan kai ka ga dama ba wai doka ce ta ce haka ba.'' Ya ce.
Duk wani kokari da BBC ta yi na ji daga bakin hukumomin 'yansanda na jihar ta Kaduna dangane da lamarin hana jam'iyyar ta ADC ganawar da ta shirya, ya ce tura.
Wakilin BBC ya nemi tuntubar kakakin rundunar 'yansanda a jihar ASP Mansur Hassan amma lamarin ya ci tura.
Wasu masu lura da al'amura na ganin irin salo da yanayin siyasar kasar ke dauka a yanzu, kasa da shekara biyu kafin babban zaben kasar na 2027, wata alama ce ta irin wainar da za a toya a babban zaben na gaba.