Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyin da China ke yi wa Birtaniya leƙen asiri
- Marubuci, Gordon Corera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Security analyst
- Lokacin karatu: Minti 6
Tambaya ce da gwamnatoci suka dinga fama wajen neman amsarata: wace irin barazana China ke yi wa Birtaniya?
Yunƙurin amsa ta kuma na iya zama ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo kama wasu mutum biyu 'yan Birtaniya - Christopher Cash da Christopher Berry - bayan zargin su da taya China leƙen asiri a Birtaniya ƙarƙashin dokar Official Secrets Act.
Mutanen sun musanta aikata wani laifi - amma bayan yin watsi da zargin da ake yi musu a watan da ya gabata, sai kuma hakan ya jawo cecekuce irin na siyasa.
Duk waɗannan rikita-rikita na ƙara jawo ayoyin tambayoyi ne game da girman barazanar da Birtaniya ke fuskanta daga China.
A wani gefen, akwai masu yi wa China aikin leƙen asiri da ke ɓatar da kama a matsayin jami'an difilomasiyya, kuma suke ɗaukar mutane aikin tura musu bayanan sirri.
Wani shaida daga ofishin mai shigar da ƙara kan lamarin Cash da Berry da aka jingine ya nuna cewa: "China na son tattara bayanai ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ƙwararru kan tsare-tsare, da ma'aikatan gwamnati, da cibiyoyin mulkin dimokuradiyya, kuma sun iya yin bakin ƙoƙarinsu wajen samun duk bayanan da suke buƙata."
Sai dai kuma kusan kowace ƙasa a duniya na yin irin wannan aiki na leƙen asiri - amma neman sanin irin shirin da wata ƙasa ke yi tsohuwar hanya ce. Ita ma Birtaniya na yin irin wannan aiki kan China, kamar yadda ta yi ƙorafi a baya.
Duk lokacin da aka kama wata ƙasa da irin wannan laifi, akan samu rashin jituwa amma kowa ya san abu ne da aka saba.
Amma ayyukan ya sha bamban da irin wannan hanya, abin da ke jefa wa mahukuntan Birtaniya fargaba.
Inda lamarin ya ƙara rikicewa shi ne, wasu da dama na ganin ya kamata Birtaniya ta tattauna da China.
Ƙarfin tattalin arzikin China, misali, zai bai wa Birtaniya damarmaki wajen haɓaka nata.
Rahotonni sun ce sabuwar gwamnatin 'yan Labour na neman kyautata alaƙa da China. Sai dai yin nasarar hakan da kuma iya zama da kasadar da ke cikin yin hakan matsala ce da ta sha kan gwamnatoci da dama.
Fargaba game da tasirin siyasa
Irin girman sashen tattara bayanan sirri na China, wanda wasu ke ƙiyasin ya kai mutum rabin miliyan idan aka lissafa da ma'aikata da na ƙasashe waje, na nufin za ta iya gudanar da wasu ayyuka da yawa fiye da sauran ƙasashe.
A China, abin da aka fi sakawa a gaba shi ne yin tasiri kan muhawara irin ta siyasa, da kama masu adawa da gwamnati, da tattara byaanai masu yawna gaske, da kuma tabbatar da cewa gwamnatin jam'iyyar kwamunisanci ta ci gaba da mulki.
A Birtaniya, fargabar da ake da ita game da tasirin China a siyasa na ƙaruwa.
Hukumar leƙen asiri ta Birtaniya MI5 ta taɓa fitar da "ankararwar kutse" a watan Janairun 2022 game da zargin wani wakilin China, Christine Lee, wanda aka yi imanin ya yi kutse a majalisar Birtaniya.
Mis Christine ta musanta zargin. Daga baya ma ta shigar da ƙara a kotu kan MI5 wadda ba ta yi nasara ba, tana mai cewa sanarwar da hukumar ta fitar na da niyyar yin tasiri "a siyansace".
MI% ta kuma yi gargadin cewa China na taimaka wa 'yansiyasa a farko-farkon yunƙurinsu na samun manyan muƙamai - wata alama ta shiri na dogon lokaci da kuma juriyar haddasa tasiri a nan gaba.
Wani ɓangare da ke ƙara tsorata Birtaniya ita ce yadda China ke yin leƙen asiri kan masu adawa da gwamnatin ƙasar, kamar ƙungiyar masu fafutika ta yankin Tibet.
Kwararar masu fafutikar kare dimokuradiyya daga Hong Kong zuwa Birtaniya ta ƙara ta'azzara fargabar.
China ta sha musanta zargin leƙen asirin tana cewa yunƙurin ɓata mata suna ne kawai.
Yunƙurin jawo malaman jami'a
Akwia wani abu da mahukunta ke shan wahala wajen daƙile shi idan ana maganar China: ta yaya za a amfani girman tatalin arzikin China da kuma kauce wa barazanarta.
Babban abin da China ta saka a gaba shi ne haɓaka tattalin arzikinta a yanzu.
Wasu na ganin cewa 'yan China za su iya haƙura da ƙarancin yin wasu abubuwa da kuma ci gaba da zama ƙarƙashin mulkin jam'iyya ɗaya ta kwamunisanci matuƙar dai suna samun alfanun tatalin arziki.
Wannan ne babban dalilin da ya sa China take yawan neman hanyoyin inganta tatalin arzikinta fiye da ƙasashen Yamma.
Akwai kuma bayanan da ba na sirri ba ne, kamar binicke kan kayayyakin kimiyya a jami'o'i waɗanda ke da amfani a fannin farar hula da na soja.
MI5 ta ce tana aikin "daƙile yunƙuri na janye ƙwararrun malaman jami'a daga Birtaniya" domin samun fasahar da suke aiki a kan ta.
"A wannan duniyar da kayayyakin aikin soja suka daogara da lambobin latironi, kuma ake yawan kwarmata bayanan abubuwa, za a iya sabuta wata ma'aikata baki ɗayanta - kuma hakan zai jawo sauya wuraren ayyuka da samun dama irin ta siyasa," a cewar Andrew Badger, wani tsohon jami'in leƙen asiri na Amurka kuma marubucin littafin The Great Heist: China's Epic Campaign to Steal America's Secrets.
"Muhawar da ake yi a Birtaniya yanzu kan yadda za a hukunta masu leƙen asiri, da ƙarfafa dokoki, da daidaita kasuwanci da tsaro, ya kamata su fara daga amincewa da wannan gaskiyar: ƙarfin tattalin arziki zai ɗore ne kawai idan ƙasa na riƙe da wasu sirrika."
Babban haɗarin da ba za a iya ƙiyastawa ba
Yayin da ƙarfin tattalin arziki na China ke ƙaruwa - musamman a ɓangaren fasaha - babban haɗarin da ba za a iya ƙiyastawa ba shi ne dogaron Birtaniya da ƙasashen Yamma kan China a wasu fannoni masu muhimmanci, kamar ababen hawa masu amfani da lantarki da sauran ma'adanai da ake sarrafa kayayyaki masu muhimmanci.
Wannan ya ƙara bijiro da muhawara kan tasirin manyan kamfanonin China na sadarwa kamar Huawei, wanda ya samar da babban ɓangare na fasahar 5G a Birtaniya.
Kayayyakin China sun fi sauƙi kuma sukan fi na abokan hamayyarsu kyau - amma ko akwai wani haɗari?