Yadda ruwan sama ke buɗe ƙaburbura a maƙabartar Ɓashama

Bashama
Lokacin karatu: Minti 3

A duk lokacin da damuna ta fara zuwa nisa, manoma sukan shiga farin ciki tare da shig harkar noma gadan-gadan, inda har wasu ma'aikata suke ɗaukar hutu domin zuwa kula da gonakinsu.

Amma a wani lamari da Hausawa ke kira 'duniya juyi-juyi' a daidai lokacin da wasu suke murnar, wasu kuma fargaba suke shiga na abubuwan da za su fuskanta.

Daga cikin abubuwan da ake fargabar fuskanta akwai ambaliyar ruwan sama da kusan duk shekara ke zuwa ta ɗaiɗaita wasu garuruwa a Najeriya da ma wasu ƙasashen duniya. Ko a bana, mutanen da ambaliya ta kashe a jihar Neja sun kai aƙalla 230 sannan wasu suke ɓace.

Ambaliyar ruwan sama dai a Najeriya za a iya cewa ta fara zama ruwan dare, domin tana yawan maimaituwa a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya sa hukumar kula da yanayi ta ƙasar ke yawan fitar da gargaɗi domin a kiyaye aukuwar lamarin a duk shekara.

Sai dai ba masu rai kaɗai ba ne damunar take shafa, domin ambliya takan shiga maƙabartu, ta sa ƙaburbura su rufta, wanda hakan ya sa masu haƙar ƙabari suka ce da zarar damuna ta fara nisa, sukan shiga tashin hankali.

'Duk shekara muka gani'

A maƙabartar Ɓashama da ke unguwar Tudun Wada a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu, ruwan sama kan kutsa ciki, har ƙaburbura su rufta, lamarin da ke ɗaga hankalin masu aikin maƙabartar.

Malam Magaji Adamu, shi ne shugaban masu aikin maƙabartar, ya bayyana wa BBC cewa a daidai lokacin da damuwa ta kunno kai, sukan shiga tunani da fargabar "halin da ƴan'uwanmu da iyayenmu matattu za su shiga musamman idan ruwan ya fara nisa."

Ya ce, "kusan duk shekara ambliya tana zuwa wannan maƙabarta, amma wata shekarar tana fin wata. Kimanin shekara biyar baya ne aka yi wata ambaliyar da ba mu taɓa gani ba saboda sai da ambaliyar ta shafe kwalta har ta kusa hana motoci wucewa," in ji shi.

Magaji ya ce tun lokacin ba a sake irin wancan ambaliyar ba, "duk da ana cigaba da samun ambaliyar duk shekara."

A game da yadda ruwa ke samun kutsawa maƙabartar, shugaban masu aikin kula da maƙabartar ya ce ambaliyar na shiga ne ta ɓangaren kudanci. "Kuma mun sha yin kiraye-kiraye domin a fahimci matsalar. Duk shekara muna bayyana abin da muke fuskanta da kuma abin da muke ganin za a yi a magance aukuwar lamarin."

Ya ce idan ruwan ya shiga maƙabarar, "sai ƙaburbura su rufta bayan ruwan ya janye daga bisani."

Me ke jawo ambaliyar?

A game da abin da ke jawo ambaliyar, Malam Magaji ya ce dattin da ake zubawa a magudanar ruwa ne ke taruwa ya cushe babban kwalbatin da ke gefen maƙabartar, wanda ke tilasta ruwan neman hanya.

"Idan dattin ya cunkushe rafin da ke gabashin maƙabartar da kuma na yamma da maƙabartar, maimakon ruwan ya tafi babban rafi, sai ya kwaroro cikin maƙabartar," in ji shi.

Ya ce duk shekara suna shiga cikin fargaba da tashin hankali, saboda sun san abin da zai faru.

A cewarsa, rafin na ɗauko ruwa da yawan da ya wuce misali, sannan ba a yi tanadin da zai riƙa tura ruwan zuwa babban rafi ba.

Sai dai ya ce maganar da ake yaɗawa cewa gawarwaki na fitowa saman ruwa saboda ambaliyar, "ba haka ba ne."

"Gaskiya mu dai ba mu taɓa ganin inda ambaliyar ta rufta ƙaburbura ba, sannan gawarwaki suka fito suna yawo a saman ruwa ba. Kawai dai ƙaburbura suna ruftawa, idan ruwan ya janye kuma mu bi mu cike da ƙasa," in ji Magaji.

'Ƴan China sun zo'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Magaji wanda zuriyarsu ta kwashe sama da shekara 50 suna hidimta wa maƙabartar ya ce abin da ya kamata a yi mai sauƙi ne, domin a cewarsa sun san abin da ke faruwa.

"Mun daɗe muna bayanin abin da ke faruwa, kuma an daɗe ana zuwa ana ɗaukar hotunan gurin. Har wasu turawa ƴan ƙasar China sun zo sun ɗauki hotuna, amma har yanzu shiru ba a yi aikin magance matsalar ba."

Magaji ya ce da zarar an yi kankare a kwalbatin da ke gabashin maƙabartar, "sannan a faɗaɗa shi, to idan aka yi haka duk ruwan da ya zo, zai bugi kankaren ne kawai ya tafi babban rafi saboda an magance zaizayar da bakin gaɓar ke yi."

Ya ce idan ba a magance zaizayar ba ta hanyar yin kankaren, ramin zai cigaba da faɗaɗa yana ƙara shiga maƙabartar, "kuma ba a san inda matsalar za ta tsaya ba."

Ya ƙara cewa a matakinsu na ma'aikata, duk shekara idan damuna ta zo suna daina haƙa ƙabari a gefen da ke da lema, "sai mu kuma can arewacin maƙabartar. Idan kuma rani ya zo, sai kuma koma yankin da ya fi lema domin sauƙin aiki."

A ƙarshe ya yi kira ga gwamnti da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su kawo ɗauki, " a zo a mana aiki mai kyau, a yi kankare a gefe da gefe."