Newcastle na zawarcin Mainoo, watakila Man U ta kori Amorim

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle na nazarin daukar dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Kobbie Mainoo mai shekaru 20 a watan Janairun badi (Talksport), external
Real Madrid da Paris St-Germain bibiyar halin da William Saliba ya ke ciki a Arsenal, inda suke ci gaba da tattaunawa kan sabon kwantagari da su bai wa dan wasan bayan Faransa mai shekara 24 (CaughtOffside), external
Chelsea ta kara kaimi a yunkurin da ta ke take yi wajan dauko dan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton mai shekara 21 a watan Janairun badi (Teamtalk), external
Watakila Everton ta shiga kasuwar cefanar da 'yan wasa domin neman dan wasan baya idan ta cigaba da fuskantar matsalar yan wasa masu fama da rauni. (Football Insider), external
West Ham da Everton da Nottingham Forest na sha'awar daukar dan wasan Tottenham Sergio Reguilon a bazara yayin da dan wasan Sfaniya mai shekara 28 zai kasance ba shi da kwantarigi da wata kungiyar bayan ya bar Tottenham.(Mail), external
Liverpool na tunanin daukar dan wasan Barcelona da Uruguay Ronald Araujo a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan baya Ibrahima Konate mai shekara 26 idan ya koma taka leda a Real Madrid. (Fichajes - in Spanish), external
Bournemouth ta kuduri aniyyar kara tattaunawa da kocinta Andoni Iraola a wata mai zuwa saboda kwantiragin dan kasar Sfaniya zai zo karshe a bazara mai. (The I paper - subscription required), external
Ruben Amorim na fuskantar wani mawuyacin lokaci a matsayin kocin Manchester United, inda wasanni uku masu zuwa za su tabbatar da ko zai ci gaba da jagorantar kungiyar a Old Trafford ko a'a. (Daily Express), external
Kocin Crystal Palace, Oliver Glasner, da tsohon kocin Ingila Gareth Southgate da kocin Fulham Marco Silva da kuma kocin Bournemout, Iraola na cikin wadanda ake ganin zasu maye gurbin Amorim idan Manchester United ta kore shi daga aiki. (Daily Star), external
Ita ma West Ham ta fara nazari kan wadanda za su maye gurbin Graham Potter kuma suna son wanda zai iya jan ragamar tawagar da magoya bayan kulob din. (Teamtalk), external
Wakilin dan wasa mai kai hari na Senegal Nicolas Jackson ya ce dan wasan mai shekaru 24 ba zai taba komawa Chelsea ba, bayan ya koma Bayern Munich a matsayin aro. Canal+ via Transfermarkt - in German)














