Zakarun Turai : Haalanda ya sake kafa tarihi bayan Man City ta doke Napoli 2-0

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland ya sake kafa wani tarihin inda ya kasance danwasan da ya fi sauri wajen cin kwallo 50 a gasar Zakarun Turai, inda Manchester City ta doke Napoli da ci 2-0.
Haaland ya kafa wannan tarihi ne da wasa 49, inda ya zura kwallon da ta ba shi wannan dama a minti na 56 bayan an koma daga hutun rabin lokaci, a wasan da aka zaku da ganin tsohon danwasan Man City Kevin de Bruyne wanda ya koma Napoli, sai dai an fitar da shi bayan minti na 26.
De Bruyne wanda ya bar City a bazara ba tare da sonshi ba bayan ya dauki kofi 16 a cikin shekara goma, ya fita daga wasan ne kasancewar an ba wa dan bayansu kuma kyaftin, Giovanni di Lorenzo katin kora, saboda ya yi wa Haaland keta a matsayinsa na bango na karshe a baya a don haka kociyansu Antonio Conte ya fitar da shi ya shigo da dan baya domin karfafa bayan.
Jeremy Doku ne ya ci wa Manchester City kwallon ta biyu a minti na 65 a karawar da ke zaman ta farko ta kungiyoyin biyu a gasar ta Zakarun Turai.
A sauran wasannin na Alhamis Eintracht Frankfurt a gida ta ci bakinta Galatasaray 5-1, kamar yadda ita ma Sporting Lisbon ta lallasa bakinta Kairat Almaty 4-1.



















