Su wane Kurdawa masu ƙungiyar PKK kuma me ya sa ba su da ƙasarsu ta kansu?

Wasu Ƙurdawan Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyar PKK, ko kuma Kurdistan Workers' Party, ta kasance matsala ga Turkiyya tsawon shekaru da dama.

Ƙungiyar, wadda ta kafu kan neman sauyi, an kafa ta ne a shekarun 1970 kuma ta fara ɗaukar makamai don yaƙar gwamnatin Turkiyya a 1984, da zimmar kafa ƙasar Kurdawa tasu ta kansu a cikin Turkiyya.

Su wane ne Kurdawa kuma me ya sa ba su da ƙasarsu ta kansu?

Wata rundunar Kurdawa kenan Daular Usmaniyya a shekarar 1915.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kurdawa da yawa sun taya Daular Usmaniyya yaƙi a Yaƙin Duniya na Ɗaya, amma kuma an samu waɗanda suka yi adawa da hakan

Kurdawa na ɗaya daga cikin 'yan asalin mazauna tsaunuka da yankunan Mesopotamia, wadda ta kai har kudu maso gabashin Turkiyya, da arewa maso gabashin Syria, da arewacin Iraƙi, da arewa maso yammacin Iran, da kudu maso yammacin Armenia.

Ana ƙiyasin cewa akwai Kurdawa miliyan 25 zuwa 35 da ke zaune a waɗannan yankunan. Su ne ƙabila ta huɗu mafi girma a Gabas ta Tsakiya (bayan Larabawa, da Fasha, da Turkawa), amma kuma ba su da ƙasa mai zaman kanta.

Tsawon ɗaruruwan shekaru, Kurdawa sun zauna ƙarkashin mulkin Usmaniyya. Bayan rushewar daular a ƙarshen Yaƙin Duniya na Ɗaya, da yawansu sun fara tunanin kafa ƙasarsu da ake kira Kurdistan. Ƙasashen Yamma da suka yi nasara a yaƙi sun ce za a iya yin hakan a yarjejeniyar Sèvres ta 1920.

Sai dai kuma, Yarjejeniyar Lausanne ta 1923 ta shafe ta, wadda ta tsara iyakokin ƙasar Turkiyya a yanzu kuma ba ta ayyana wani shirin kafa ƙasar Ƙurdawa ba.

Kurdawa sun zama 'yan tsirari a duka ƙasashen da suke zaune. Duk wani yunƙuri da Kurdawan suka yi na kafa ƙasarsu na haɗuwa da fushin hukumomi tsawon shekara 80 da suka wuce.

Me ya sa Turkiyya ke kallon PKK a matsayin barazana?

Abdullah Ocalan tare da mayaƙan PKK a Lebanon a shekarar 1992

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abdullah Ocalan tare da mayaƙan PKK a Lebanon a shekarar 1992
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kurdawa ne kashi 15 zuwa 20 na al'ummar Turkiyya.

Yayin yaƙi da yunƙurin Kurdawan a Turkiyya a shekarun 1920 da 1930, an mayar da Kurdawa da yawa wasu wurare, aka hana amfani da wasu tufafinsu, aka taƙaita magana da harshensu, har ma da ƙin amincewa da ƙabilarsu inda aka koma kiran su da Turkawan kan duwatsu (Mountain Turks).

A 1978, Abdullah Ocalan - wani ɗan gwagwarmya mai sassaucin ra'ayin daga kudu maso gabashin Turkiyya - ya kafa PKK, wadda ke neman kafa ƙasar Kurdawa a cikin Turkiyya. A 1984 ƙungiyar ta fara ɗaukar makamai.

Tun daga lokacin ne kuma aka kashe sama da mutum 40,000 a cikin Turkiyya da kuma yankunan Syria da yankunan Iraƙi masu iyaka da Turkiyya sakamakon faɗa tsakanin 'yan PKK da dakarun gwamnatin Turkiyya. An raba dubun dubatar mutane da muhallansu a cikin Turkiyya.

Turkiyya ta ayyana PKK a matsayin ƙungiyar 'yanta'adda. Ƙasashen Amurka, da Birtaniya, da ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU duka suna kallonta a matsayin ta 'yanta'adda.

Me PKK ke nema a Turkiyya?

A shekarun 1990, PKK ta sauya buƙatun neman kafa ƙasa, inda ta koma neman 'yancin kai na Kurdawa.

Da yake magana da BBC a 2016, jagoran ɓangaren soji na PKK Cemil Bayik ya ce: "Ba mu son ɓallewa daga Turkiyya don kafa ƙasa. Muna son cigaba da zama a cikin Turkiyya cikin 'yanci.

"Gwagwarmya za ta ci gaba har sai an amince da 'yancin Kurdawa," a cewarsa.

Sai dai, Turkiyya na ci gaba da kallon PKK a matsayin "mai neman ɓallewa daga ƙasar".

An yi mummunar arangama tsakanin dakarun Turkiyya da 'yan PKK a tsakiyar shekarun 1990, lokacin da aka lalata dubban ƙauyuka a yankunan Kurdawa, wnada ya tilasta wa dubun dubatar Kurdawan sauya matsuguni a wasu biranen.

Ko PKK ta taɓa neman yarjejeniyar zaman lafiya?

Mayaƙan PKK kenan a yankin Kurdistan mai 'yancin kansa a Iraƙi, wanda ke maƙotaka da Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mayaƙan PKK kenan a yankin Kurdistan mai 'yancin kansa a Iraƙi, wanda ke maƙotaka da Turkiyya

PKK ta sha wuya a 1999 lokacin da aka tsare shugabanta, Abdullah Ocalan, bisa tuhumar cin amanar ƙasa.

Jim kaɗan bayan haka, PKK ta sanar da tsagaita wuta ta shekara biyar don raɗin kanta, kuma ta yi yunƙurin sauya alƙibla ta hanyar gwagwarmaya a siyasance.

Ta nemi shiga siyasar Turkiyya, da neman ƙarin 'yanci ga Kurdawa, da kuma sakin mambobinta da aka kama.

Turkiyya ta ƙi yarda ta tattauna da ita kuma 'yan ƙalilan kawai ta yi wa afuwa daga cikin mambobin ƙungiyar.

Tsakanin 2009 da 2011, PKK da gwamnatin Turkiyya sun yi tattaunar sirri a ƙasar Norway, amma ba ta ɗore ba.

A watan Maris na 2013, Ocalan ya sake sanar da tsagaita wuta bayan tattaunawa da gwamnati kuma ya nemi dakarun PKK su fice daga Turkiyya. Sai dai kuma yarjejeniya ta rushe a watan Yulin 2015.

An kashe sama da mutum 7,000 sakamakon rikici tsakanin PKK da gwamnatin Turkiyya tun bayan rushewar yarjejeniyar zaman lafiya a 2015, a cewar Crisis Group

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kashe sama da mutum 7,000 sakamakon rikici tsakanin PKK da gwamnatin Turkiyya tun bayan rushewar yarjejeniyar zaman lafiya a 2015, a cewar Crisis Group

An kashe sama da mutum 7,000 sakamakon rikici tsakanin PKK da gwamnatin Turkiyya a ƙasar da Iraƙi tun bayan rushewar yarjejeniyar zaman lafiya a 2015, a cewar cibiyar Crisis Group.

Faɗan ya fi ƙamari a 2015 da 2016, kuma an fi gwabzawa a kudu maso gabashin Turkiyya.

Zuwa 2019, dakarun Turkiyya sun kora mayaƙan da yawa daga ƙasar, inda aka koma yinsa a yankin Kurdistan mai 'yanci da ke arewacin Iraƙi da Syria.

A Syria, dakarun Turkiyya (da kuma wasu ƙungiyoyin ƙawance da ake kira Syrian National Army) na ci gaba da yaƙar ƙungiyar People's Defence Units (YPG) ta Kurdawa.

Tun daga Oktoban 2024, gwmanatin Turkiyya tare da Devlet Bahceli, shugaban jam'iyyar Nationalist Movement Party, na ta tattaunawa da PKK, inda ya kai wa Ocalan ziyara a gidan yari mai tsananin tsaro da ke Tekun Marmara.