Kumbon leƙen asirin Koriya ta arewa ya faɗa cikin teku

Hoton tarkace a cikin tekun Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Reuters

Koriya ta arewa ta ce wani hatsari ya afku a lokacin da take shirin aika tauraron ɗan'adam na farko a sararin samaniya, wanda ya sa ya fada cikin teku.

Fadar Pyongyang ta sanar a baya cewa ta shirya harba tauraron ɗan'adam nan da ranar 11 ga watan Yuni domin sanya ido kan ayyukan sojojin Amurka.

Yanzu ƙasar ta ce za ta yi ƙoƙorin ƙaddamar da na biyu nan gaba kaɗan.

Harba kumbon ya tayar da ƙararrawar gargaɗi a birnin Seoul na maƙwafciyar ƙasar, Koriya ta kudu, yayin da a Japan aka yi gargaɗi ga mazauna Okinawa da ke kudancin ƙasar.

An dai samu hargitsi da ruɗani a birnin Seoul yayin da mutane suka farka da ƙarar jiniya da aka yi ta sama da kuma saƙon gaggawa da ke gaya musu cewa su yi shiri don gudu sai kuma bayan mintuna 20 aka ce an aika da shi cikin kuskure.

Rikici ya yi ƙamari a Koriya, inda aka kwashe shekaru 70 ana takun-saka tsakanin ƙasashen biyu, kuma wannan ƙararrawar ƙarya na iya yin illa sosai ga amincin mutane ga tsarin faɗakarwa.

Koriya ta Arewa barazana ce ga Koriya ta Kudu, sai dai idan aka yi wata sanarwar a nan gaba, shin ko za a ɗauka ta ƙarya ce?

Wata mata ƴar shekara 33 mai suna Kim da ke zaune a birnin Seoul ta shaida wa BBC cewa ta "tsorata matuka" lokacin da ta samu sanarwar gaggawa, inda ta fara tattara komatsanta domin arcewa daga inda take.

"Ban taba tunanin za ayi yaƙi ba, amma bayan yaƙin Ukraine ya sa na yi tunanin cewa Koriya ta Arewa ko China za su iya mamaye Koriya ta Kudu," in ji ta, ta kara da cewa a tunaninta Pyongyang ba ta yi tunani ba kafin ta kaddamar da hari.

Firaiministan Japan, Fumio Kishida ya ce da alama Koriya ta Arewa ta harba miyagun makamai kuma gwamnati na yin nazari kan bayanan.