Mene ne duwatsun da ke yawo a sararin samaniya?

Asalin hoton, SPL
Asteroid: Ɗutse ne wanda bai da girma sosai da ke zagaye rana.
Comet: Shi ma dutse ne mara girma sosai kuma a wani lokaci yana aiki, kuma idan ya narke zai iya tafasa a rana ya zama ƙura da iska.
Meteoroid: Ɗan ƙaramin dutse ne daga comet ko kuma asteroid wanda ke zagaye rana.
Mateor: Hasken da ke fitowa idan Meteoroid ya shiga sararin samaniyar duniyar Earth kuma ya tafasa ya zama tauraro.
Meteorite: Wannan kuma dutse meteoroid ne da ya iya wucewa ya shiga sararin samaniyar duniyar Earth kuma ya sauka a kan ƙasar duniyar.
Girma da adadi
A kullum, duniyar Earth na samun sama da tan 100 na ƙura da kuma ƙwayoyi na ƙasa.
Kusan sau ɗaya a shekara, asteroid mai girman mota na faɗowa cikin sararin samaniya, wanda yake tahowa a matsayin dunƙulen wuta, sai ya ƙone kafin ya faɗo ƙasa.
A duk shekara 2,000, ana samun meteoroid da ke da girman filin ƙwallo da ke faɗowa cikin duniyar Earth inda yake lalata wurin da ya faɗa.
Haka kuma a miliyoyin shekaru, ana samun wani babban abu da ke faɗowa wanda ke barazana ga ci gaban duniya baki ɗaya.
Duwatsun da ke sararin samaniya sun fi ƙanƙanta da kusan mita 25 kuma akasarinsu suna ƙonewa da zarar sun shiga duniyar Earth kuma ba su cika lalata wuri ba.
Idan akwai dutsen meteoroid da ya fi girman mita 25 amma ƙasa da kilomita ɗaya, idan dutsen ya faɗo ƙasa, akwai yiwuwar zai iya lalata wurin.
Idan aka kwatanta, asteroids da ke da yawa a duniyoyin Mars da Jupiter, kuma ba su da wata barazana ga duniyar Earth, kuma zai kai girman kilomita 940.
Irin bala'in da ake fuskanta da ba a san zai faru ba
Akasarin meteorites da ake samo su a ƙasa ba su da nauyi. Sakamakon ƴan ƙanana ne ba su haddasa wata illa ga duniya.
Meteorites mai nauyin 0.45kg wanda ke tafiya sama da gudun da ya kai 200mph zai iya fadowa kan rufin kwanon gida ya huda shi sa'annan ya fasa gilas ɗin mota.
Alal misali, a lokacin da aka taɓa samun wani meteorite ya faɗo a Ontario da ke Canada a 2009 inda har ya fasa gilas ɗin mota.
A wani lamarin kuma da ya faru, meteorites ɗin kuma ya taɓa faɗowa a bayan wata mota nau'in Chevy Malibu a Peekskill da ke New York sai dai babu wanda ya samu rauni sakamakon wannan lamarin.
Wani meteorite ɗin kuma da ya sake faɗowa shi ne Tunguska meteorite wanda ya ɗara Chelyabinsk girma kuma ya fi ƙarfi da kusan kashi 10.
Meteorite ya fashe a saman kogin Tunguska a ranar 30 ga watan Yunin 1908 inda ya bazar da kadada 500,000 na wani daji.










