Matar da ke fafutukar share yankin da mai ya gurɓata don kare muhalli

Hoton mace

Asalin hoton, EUCHARIA NWAICHI

Wannan labari ne na wani abu da ba kasafai aka saba gani ba, na wata mata da ke aikin kare muhalli daga gurɓacewa.

Zirarar mai lokaci zuwa lokaci a yankin Neja-Delta da ke kudancin Najeriya, ya gurbata yawancin muhallai a yankin.

Abin yana da haɗari – ƙungiyoyin 'yan bindiga sun kasance suna fasa bututai, inda suke zargin kamfanonin mai da cewa sun manta da su.

Ayyukan masu garkuwa ma na ƙaruwa, inda a yanzu ba a yarda da wani mutum da ya fito daga wani wuri.

Wata masaniyar fannin kimiyya mai suna Eucharia Nwaichi, ta ce a shirye suke wajen share yankin da mai ya gurɓata da kuma wuta ke ƙonawa.

‘’Muna son mafita ta kare muhalli. Ba ma son lalata abubuwa a ƙoƙari da muke yi na neman gyara,’’ kamar yadda Eucharia ta faɗa wa BBC.

An bai wa Eucharia mai shekara 44 lambar yabo na Maddox – wanda kyauta ne da ake bai wa masanin kimiyya da ya jajirce wajen neman kawo mafita a cikin al’umma.

Ta nuna farin cikinta lokacin karɓar kyautar a birnin Landan, inda ta kasance mace ta farko daga Afirka da ta samu kyautar.

Eucharia ta karanci fannin halittu a jami’ar Jihar Fatakwal. Hanyar da take bi wajen farfaɗo da tsirrai da kuma ruwan da mai ya gurɓata abu ne mai sauki.

.

Asalin hoton, EUCHARIA NWAICHI

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta kasance tana aiki a yankin Neja-Delta da ke da manyan rijiyoyin mai tun a shekara ta 2003.

Lokacin da take karatun digiri a mataki na uku, ta gano cewa kayan bola da ke fita daga masana’antun mai, na gurɓata ruwan sha.

Gurbacewar muhallin na janyo rikici tsakanin al’ummomin da kuma kamfanonin mai da ke aiki a yankin.

Eucharia ta bayyana cewa bayan tattara hujjoji kan abin da ke janyo rikici tsakanin ɓangarorin biyu, ta buƙaci kamfanonin da su sauya yadda suke haar mai.

Amfani da hanyoyin kimiyya lokacin da ake samun rikici tsakanin ɓangarorin, shi ya sanya ta samu lambar yabon.

‘Eucharia ta kasance tana shiga tsakanin ɓangarori da ba su jituwa ta hanyar yin tambayoyin kimiyya da za su samar da mafita,’’a cewar Tracey Brown, darektan wata ƙungiyar agaji da ta bayar da kyautar.

Abin da ya sanya ta zamo ta daban cikin mutane shi ne amfani da hanyar diflomasiyya da take yi – wajen ganin ta shawo kan mutane da kuma bin hanyar lalama da kamfanoni domin su biya kuɗin share muhallin.

Bayan fama da gurɓacewar muhalli na gomman shekaru, a yanzu mutane na zuwa kotuna domin bi masu hakki. A shekarar 2021, wata kotu a Netherlands ta yanke hukuncin cewa kamfanin Shell ya biya wasu manoma kuɗi saboda lalata musu gonaki.

Sai dai Eucharia ta ce mai na ci gaba da gurɓata muhallai. Lokacin da aka shigar da ƙara, buƙatar aikin share muhalli ba shi ne abu kaɗai da ya kamata a yi ba, ta ce akwai buƙatar a haɗa har da mutane da ke zaune a wuraren da mai ya gurɓata domin a samu mafita.

‘Idan ba ka tafi da kowa ba, za a iya garkuwa da kai. Da farko nakan samu shugaban al’umma da shugabar mata da kuma shugabannin matasa,’’ in ji Eucharia.

.

Asalin hoton, EUCHARIA NWAICHI

Magana da Turancin Pidgin ko wani yare a cikin gida da kuma amfani da ilimin gargajiya, na taimakawa wajen ƙara yarda tsakanin mutane,’’

‘Mutane na cike da farin ciki kamar su ma masana ne na kimiyya, saboda suna aiki da mu masana domin samun mafita,’’ a cewar Eucharia.

‘Mu ma muna koyon wasu abubuwa daga gare su. Suna da ilimin yin shuka da ba mu da shi – suna koya mana yadda za a samu mafita a yankinsu,’’ in ji Eucharia.

Ta ce ya kamata a sake share filayen da mai ya gurɓata domin shuka ta girma idan aka yi shaki maimakon a ce al’umma za su mayar da hankali kawai kan biyan diyya.

Duk da cewa kamfanonin na bai wa mutanen yankin damar tafiya karatu zuwa jami’o’in Amurka, ta ce ta tsaya domin aiki a yankin Neja-Delta, saboda tana da zimmar ganin ta ciyar da ƙasarta gaba’’.

Yawancin masu rajin kare muhalli na ganin kamfanonin haƙo mai na ƙasashen waje a matsayin abokan gaba.

Ƙungiyar Amnesty International na jajircewa a ko-da-yaushe wajen ganin ta sanya kamfanonin yin abin da ya kamata, ba wai barin al’ummomin cikin barazana ga lafiyarsu da kuma rashin tsaftataccen ruwan sha da kuma yadda suke gurɓata rayuwar mutanen yankin.

Sai dai Eucharia ta ce ba ta son ɗaukar ɓangare. ‘Bamu zo nan domin yin faɗa ba. Muna son mutane su yi abin da ya kamata,’’.

Ita ma ta fuskanci barazana a baya. A shekara ta 2020, ta bayyana a cikin wata takarda cewa wani kamfanin mai ya yi mata barazana domin ta fito ta yi magana kan gurɓata muhalli da ya yi a yankin, inda suka lalata mata kayan aiki.

Ta ce kamfanin ya ƙalubalance ta cewa a matsayinta na mace, bai kamata a bar ta ta yi aiki a wajen ba.

Duk da cewa yankin na cike da barazana iri-iri, Eucharia ta ci gaba da fafutika saboda tana da yaƙinin cewa hakki ne da ya rataya a wuyanta na kare muhallinta.