Iska da mamakon ruwan sama sun hallaka mutane a Turai

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Mamakon ruwan sama da da iska mai karfin gaske sun haddasa barna a yankunan tsakiya da kudancin Turai, tare da hallaka akalla mutum 13 wadanda suka hada da yara uku.

Yawancin wadanda suka mutu a sanadiyyar bishiyoyi ne da iska ke kayarwa a Italiya da Austria da kuma tsibirin Corsica na Faransa.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai guguwa a wadannan yankuna na kasashen sun yi ta’adin gaske na gidaje da dukiya, ga kuma rayuka.

Ruwan ya yi barna a tsibirin na Faransa, a sansanonin shakatawa yayin da can a birnin Venice na Italiya iska ta bannata wani sashe na hasumiyar Cocin St Mark.

Mamakon ruwan saman ya biyo bayan tsananin zafi da aka sha da kuma kamfar ruwan sama a yawancin sassan nahiyar ta Turai.

A tsibirin na Corsica, iska mai gudun kilomita 224 a cikin sa’a daya, ta ruka tumbuke bishiyoyi da awon gaba da muhallai na tafi-da-gidanka.

Hukumomi a can sun ce wata bishiya ta iska ta kayar ta hallaka wata yarinya ‘yar shekara 13 a wani sansanin shakatawa.

Haka ma wani mutum shi ma ya rasa ransa ta irin hakan, yayin da wata mata dattijuwa ta mutu lokacin da rufin wata runfa da iska ta ballo ya fada wa motarta.

Wasu mutum biyu mai kamun kifi da kuma wata mata da ke cikin wani kwale-kwale a teku suma sun gamu da ajalinsu a ruwa.

Daga bisani kuma lokacin da ministan cikin gida na kasar ta Faransa da Gérald Darmanin, da ya kai ziyarar gani da ido illar da ruwa da iskar suka yi a tsibirin, ya sanar da mutuwar mutum na shida.

Karin gomman mutane a teku da kuma a tudu sun ji rauni.

Wadan suka ga yadda abin ya faru sun ce bakatatan ruwa da iskar suka fara ba wata alama ta gargadi.

Wa ni ya ce bai taba ganin irin wannan ruwa da iska masu karfin gaske ba a tsibirin.

Ambaliya

Asalin hoton, EPA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ainahin yankin cikin kasar ta Faransa, wasu yankuna na kudancin kasar sun rasa wutar lantarki, kuma ruwa ya mamaye tituna a birni na biyu mafi girma Marseille.

Can a Austria bishiyoyi da iska ta kayar sun kashe wasu 'yan mata biyu a kusa da wani tafkin a Carinthia.

Sannan daga baya kuma an samu rahoton mutuwar karin mutum uku a lardin Lower Austria, suma dai a sanadiyyar bishiyoyin da ke faduwa.

Haka ma a Italiya, wani mutum da wata mata suma sun rasa ransu a wurare daban-daban ta sanadiyyar faduwar bishiya a yankin Tuscany.

Iska da ruwan sun rika tuge tantuna da lema a dandalin Cocin St Mark, hatta hasumiyar Cocin ita ma ta gamu da barnar.

Wuraren shakataw na bakin teku ma sun gamu da bannar ruwa da iskar.

To amma kuma a kudancin kasar ta Italiya an ci gaba da dan-karen zafin da ake yi inda yanayi ya kai digiri 40 a ma'aunin Selshiyas a Sicily.

Idan aka matso kusa a tsallaken Tekun Bahar Rum a Algeria kalla mutum 38 ne suka mutu a sanadiyyar gobarar daji.

Sassan Turai da dama sun gamu da tsananin zafi da kanfar ruwan sama tsawon makonni, abin da ake alakantawa da sauyin yanayi.

Masana na gargadin cewa za a ci gaba da samun karuwar yanayin zafi a duniya har sai gwamnatocin kasashe sun dauki matakan rage hayaki mai gurbata yanayi.