'Yan ƙwadago a Najeriya sun bai wa Majalisa wa'adi ko su shiga yajin aiki

Labour Protest

Ƙungiyoyin ƙwadago sun gabatar da rubutaccen saƙo ga Majalisar Tarayyar Najeriya, a wani ɓangare na zanga-zangar da ta gudanar ranar Laraba.

'Yan ƙwadagon sun buƙaci shiga tsakanin 'yan majalisar a dambarwarsu da ɓangaren zartarwa ko kuma su tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar daga ranar Alhamis.

Sai dai mai tsawatarwa, Sanata Ali Ndume, wanda shi ne jagoran kwamitin mutum da majalisar ta wakilta don karɓar masu zanga-zangar da suka je harabar majalisar a Abuja, ya roƙi 'yan ƙwadagon a kan su jinkirta aniyarsu ta shiga yajin aiki daga Alhamis ɗin nan.

Ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon su bai wa Majalisar Tarayyar mako ɗaya a ƙoƙarinta na shiga tsakani don kawo ƙarshen wannan taƙaddama ba tare da durƙusar da harkokin gwamnati da na tattalin arziƙi a ƙasar ba.

Tun da farko, masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin shugaban NLC babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero sun yi wa majalisar tsinke cikin rakiyar jami'an tsaro, a yunƙurinsu na ganawa da masu yin dokar.

Sai dai sun gamu da turjiya da farko daga jami'an tsaro, lamarin da ya kai ga karya ƙofar shiga harabar majalisar kuma dandazon masu zanga-zangar suka ɗunguma ciki.

Labour Protests

Su dai, 'yan ƙwadagon a cikin saƙon da suka gabatar wa majalisar sun jaddada buƙatun cewa ya zama wajibi a gyara matatun man fetur na Najeriya ciki har da na Warri da Kaduna.

Sun kuma ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa farashin man fetur yana tafiya ne daidai da hawa da saukar farashin dala a kasuwar duniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar saƙon, ya zama wajibi gwamnati ta gaggauta aiwatar da alƙawurran da ta ɗauka na sauƙaƙa tsadar rayuwa.

Kuma sun nemi a sake mayar da tallafin man fetur da aka cire saboda a cewarsu babu ƙasar da ba ta tallafawa talakawanta a duniya.

Sun ce sun taɓa cimma yarjejeniya da gwamnati game da fito da wani tsarin amfani da makamashi da zai iya maye gurbin man fetur. Haka ma sun ce wajibi ne a biya malaman jami'o'in Najeriya albashin da su ke bin gwamnatin bashi na tsawon wata takwas.

Sun kuma taɓo batun kwamitin da aka kafa da zai duba tsarin sabon albashi, abin da suka ce daidai yake da alƙawarin bogi.

Shugaban ƙungiyar ta NLC Kwamared Joseph Joe Ajero ya ce a jawabin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a cikin wata ɗaya tak gwamnatin Najeriya ta yi nasarar tara naira tirliyan ɗaya, wani mataki ne kawai na tsotsar jinin talaka.

Don kuwa a cewarsa, "Kafin haka, ya dace a samar da hanyoyin rage raɗaɗi, amma sai ga shi an fake da guzuma an harbi barewa, babu wani abu da za a yi wa talaka".

Ya ce talakawa ba za su iya jiran sai nan da 2024 kafin su fara ganin alƙawurran da ba su da tabbas ba.

Bayan karɓar wasiƙar gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago, Sanata Muhammad Ali Ndume daga jihar Borno, ya roƙi ƙungiyar cewa akwai ƙalubale da matsaloli da Najeriya ke fuskanta.

Ya ce Majalisar Dokoki na biye da batun sau da ƙafa domin samar da matsaya tsakanin NLC da Fadar shugaban ƙasa. A cewarsa, ko a ranar Litinin sun fara tattaunawa kuma ya zama wajibi 'yan ƙwadago su cimma matsaya da ɓangaren zartarwa, su kuma 'yan majalisa za su goya musu baya.

b

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun gudanar da zanga-zangar ce don nuna adawa da ƙarin tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin man fetur waɗanda cire tallafin man fetur ya haddasa.

Wannan na zuwa ne bayan kiki-kakar da aka a ƙarshen wani taron kwana biyu tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadagon.

A wasu sassan Najeriya, an ga masu zanga-zangar tsamo-tsamo cikin ruwan sama baya ga tsattsauran matakin tsaro da aka ɗauka, inda suke gudanar da maci tare da rera taken goyon baya da ɗaga alluna da ƙyallaye masu rubuce-rubuce.

"A bar talakan Najeriya ya shaƙi iska," wani ƙyallen masu zanga-zanga ya ce a cibiyar kasuwanci ta Kano.

Wakilin BBC a Kano ya ce ɗaruruwan mambobin ƙungiyar ne ciki har da mata suka fita domin wannan zanga-zangar.

Shugabanni da mambobin ƙungiyar da dama sun taru a fitaccen dandalin 'Unity Fountain' da ke tsakiyar Abuja babban birnin ƙasar, riƙe da tutoci da alluna masu saƙonni iri daban-daban.

b

A ranar Litinin ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ta talbijin ga al'ummar Najeriya, inda a ciki ya jajanta wa 'yan ƙasar game da halin matsi da matakin janye tallafin mai ya jefa su, amma ya ce babu wani zaɓin da gwamnati take da shi da ya fi hakan.

Sannan shugaban ya sanar da waɗansu shirye-shiryen rage raɗaɗi da gwamnatinsa za ta ɓullo da su.

Sai dai ƙungiyar ƙwadagon ta ce babu wani tasiri da shirye-shiryen za su yi wajen rage wa al'umma matsin rayuwa.

Wasu ma'aikatun Kano sun kasance a rufe

b

Wakilin BBC ya ce wasu ma'aikatu da kasuwannin birnin Kano sun kasance a rufe saboda wannan zanga-zanga.

An jibge jami'an tsaro a faɗin birnin Kano domin sanya idanu kan yadda zanga-zangar ke gudana. Mutane da dama sun zauna a gida, maimakon fita harkokin kasuwanci da ayyukansu a birnin Kano da safe.

Wasu titunan jihar sun kasance babu yawan zirga-zirga a birnin, wanda ko a jiya wasu ƙungiyoyin fararen hula ciki har da ɗalibai suka yi wata zanga-zanga saboda tsadar rayuwa da halin matsin da ake fama da shi a ƙasar.

An tsarara tsaro a biranen Najeriya

g

Asalin hoton, Getty Images

Rahotonni daga jihar Kaduna na cewa, an jibge jami'an tsaro masu yawa, daidai lokacin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ke gudanar da maci a kan tituna.

Haka ma a birnin Abuja da Legas, an tsaurara tsaro, yayin da wasu rahotanni ke cewa 'yan ƙwadago masu zanga-zanga sun rufe wani sashe na Babban Titin Ahmadu Bello a Eti-Osa.

Kwamared Nasir Kabir, jami'in tsare-tsare na ƙungiyar ƙwadago ta NLC ya ce: ''Duk duniya babu inda gwamnati ba ta bayar da tallafi, amma sai nan Najeriya ne lokaci ɗaya (farashin man fetur) zai kai sama da kashi 600? Muna cikin tattaunawa aka je aka sake ƙara farashin mai. Mu muna ganin gwamnati kawai wasan kwaikwayo take yi.

Gwamnati kawai ta fito ta bayyana sunayen waɗanda ake cewa su ne suke morar tallafin man fetur ɗin nan".

Ya ci gaba da cewa sun yi alƙawari da gwamnati don gyara matatun man fetur da ake da su, da kuma bunƙasa samar da wutar lantarki, amma babu ko ɗaya da aka cika har yanzu.

A cewarsa ''Yaudara ce wannan, idan ma akwai wani tallafi da ake biya, me ya sa ba a janye ba tun tuni?''

Nasir Kabir ya ce sun sanar da dukkan hukumomin tsaro game da zanga-zangar ta yau, don haka suna fatan jami'an za su ba su cikakkiyar kariyar da doka ta ba su''.

Buƙatun NLC na shiga zanga-zanga

Kimanin buƙatu guda shida ne ƙungiyar 'yan ƙwadagon ta buƙaci mahukuntan Najeriya su biya.

Cikinsu akwai:

1- Aiwatar da yarjejeniyar da aka amince da ita tsakanin gwamnati da ƴan kwadago da majalisa da kuma TUC

2- Janye dokoki masu tsauri da aka sanya, ciki har da na janye tallafin mai da kara farashinsa

3- Gyara matatun man fetur na Warri da Kaduna da kuma Fatakwal.

4- Biyan albashin watanni takwas na malamai da ma'aikatan jami'o'i.