Ɗan Chadi mai zane da kayan bola

Mai zane-zane Apollinaire Guidembaye na da saƙo.

Muna buƙatar kula da muhalli.

Ya ce, "idan ba mu wayar da kai ba, wace irin duniya za mu bari ga masu tasowa?"

Yana aiki a N'djamena, babban birnin Chadi inda yake amfani da burushi da bolar da yake gani kan tituna wajen yin zane.

"A N'djamena, gurɓatacciyar iska abu ne da ake iya gani. Kana ganin ƙarafa marasa amfani da robobi cikin kwantaccen ruwa.

"Na kaɗu, amma na yarda da canji.

"Doff shi ne sunan da ake kirana, ma'ana Wolof da ke nufin 'hauka'.

"Ina hauka saboda ina tsintar duk abin da ke min magana. Yayin tattaki, idan na ga abu da ya yi mani magana, ina ɗauka."

Ya ƙara da cewa, "A wurina, babu abin da aka rasa, ana iya gyara komai."

Da zarar ya karɓi abubuwan da yake buƙata, Apollinaire yana kai su ɗakin zanensa.

"A aikina, za ka ga abubuwan da ba a cika ganinsu ba, kamar rufin gida da kwanson harsashi da wayoyi da gwangwani da sauransu.

Ana sayar da zane-zanen da ya yi ga mutane a faɗin duniya.

Barbara Kokpavo, darakta kuma wadda ta ƙirƙiri ɗakin bajekolin zane-zane na Gallery Soview a Accra da ke Ghana, ta ce Apollinaire na cikin jerin sabbin masu rajin kare zane-zane a Afirka.

"Ina tunanin masu basirar yin zane daga nahiyar masu kwarmata bayanai ne. Tabbas haka suke saboda suna magana a kan muhimman batutuwa. Suna ankarar da mu game da buƙatar a yi wani abu kan yanayin rayuwa.

Ta ce zanen Apollinaire na burge masu saye, a ƙasarsa ta Chadi da kuma ƙasashen duniya.

Ta ce, "Ƴan Chadi na sayen zane-zane. Matasa suna saye kuma suna son duk wasu zane-zane saboda abubuwa ne da ke magana ga matasa.

"Muna magana ne game da kayan da ake ƙara sarrafawa, don haka bagatatan, waɗannan abubuwa ne da ke magana ga matasa, da ke tambaya kan matsalolin da muke fuskanta a matsayin matasa kuma ina ganin hakan ne ya sa muke ƙara ƙarfafa gwiwar sabbin matasa masu sayen zane-zane saboda muna samar da abin da yake magana da su."

Ta ce zanen Apollinaire na "nuna ayyukan wasu masu zane-zanen da suke matasa da matsalolin muhalli ya shafa... Ya kamata zane-zanen da muke gani su bayyana batutuwan muhalli da matsalolinsu na ƙashin kai wajen kare duniyarmu."

A yanzu, Apollinaire yana taimakawa wajen horas da sabbin masu zane-zane a N'Djamena.

Ya ce, "Ina ganin rawar da masu basirar zane za su taka na da muhimmanci. A yau, ina ƙoƙarin koyar da dabarun sake sarrafa kaya ga masu tasowa.

"A wajena, yana da muhimmanci mu koya wa masu tasowa, sannan su ma su girma da shi sannan su ɗora a kan yaƙin da nake."

An samar da wannan labarin bisa tallafin Gidauniyar Bill da Melinda Gates.