An kashe masu kare muhalli 177 a duniya

Mutane dauke da akwatin gawa

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa an hallaka mutane 177 a fadin duniya a shekarar da ta wuce a kan fafutukar da suke yi ta kare muhalli.

Kungiyar masu raji ta Global Witness ta ce kusan kashi casa'in cikin dari na kisan ya wakana ne a yankin Latin Amurka.

A binciken da kungiyar ta yi ta ce ta gano cewa yankin na Latin Amurka, waje ne da ya dade da tarihi na fafutukar kare muhalli da kuma ‘yancin mallakar muhalli.

Binciken ya nuna cewa kasar Colombia nan ne aka fi gasa wa masu fafutukar kare muhallin aya a hannu.

Nazarin ya nuna kashi daya bisa uku na miyagun hare-hare ko kisan gillar da ake yi a kan masu kare muhallin a yankin na Amurka ta Kudu da ma duniya baki daya na faruwa ne a can.

Sai kuma Brazil da ke matsayi na biyu yayin da Mexico ke bi musu baya sai Honduras.

Yankin katafaren dajin Amazon shi ne ya fi samun wannan kashe-kashe inda mutanen yankin ke fadi tashin kare dajin nasu daga barnatawa da sunan diban albarkatu, ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar ta Global Witness ta ce bincike ya nuna al’ummomin da ke zaune a yankunan da ke da albarkatu na muhalli su suka fi lakantar yadda za a kare dazukan saboda haka suna taka muhimmiyar rawa wajen takaita illar sauyin yanayi.

Amma duk da haka irin wadannan mutane na fuskantar takura a kasashe irin su Brazil da Peru da Venezuela a kan kare muhallin, inda kusan kullum ake samun labarin kai musu hari.

Bayan yankin na Latin Amurka, a Philippines ma kusan labarin haka yake ga masu fafutukar kare muhallin kamar yadda binciken ya nuna.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahoton ya nuna cewa kamfanoni da dama da ke da mazauni a Birtaniya da Tarayyar Turai da Amurka an ce suna da alaka da wannan tauye hakki na dan’Adam da ke da nasaba da muhalli.

Kungiyar ta ce da dama wadanda ke kai hari kan masu rajin kare muhallin, ba sa shiga hannun hukuma har a gurfanar da su a gaban kotu.

Kuma rashin daukar tsauraran matakai a kan masu laifin shi ke kara ta'azzara matsalar, in ji rahoton.

Lamarin da ya zame wa masu fafutukar ta yaki da masu hakar ma’adanai da hakar mai da sare itatuwa domin yin katako, a filaye ko dazukan babbar matsala.

Masu rajin kare muhallin na yankuna na karkara su ma ba kasafai kan tsira daga ta’adar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai ba da masu safarar miyagun kwayoyi wadanda ke ribatar barnata muhallin.

Kungiyar masu rajin ta kara da cewa shugabannin yankuna na gargajiya su ma ba su tsira ba daga hare-haren da kisa, kuma da dama kisan masu rajin kare muhallin na wucewa ba tare da wani bincike ba saboda matsalar takunkumi ga ‘yancin ‘yan jarida a yawancin sassan duniya.

Kungiyar ta Global Witness ta yi kira ga gwamnatoci a fadin duniya da su dauki matakan gaggawa kan lamarin tana mai kari da cewa masu fafutukar kare muhallin na kuma fuskantar matakai na shari’a wajen hana su katabus, bayan hare-hare da kisan.