Me ya sa Kenya ta ɗage haramcin sare itatuwa, kuma me hakan ke nufi ga ƙasar?

...

Shugaban Kenya William Ruto ya cire dokar hana sare itatuwa da aka shafe tsawon shekaru shida ana amfani da ita - lamarin da ya haifar da fushi daga masu kare muhalli.

Shugaban kasar ta Gabashin Afirka ya ce "bukatar bude tattalin arzikin" yankunan da suka dogara da kayayyakin gandun daji ne ya sa ya yanke shawarar.

Me ya sa aka dage dokar haramcin?

Shugaba Ruto ya yi tsokaci kan yadda rikakkun bishiyoyi ke rubewa a dazuzzukan Kenya yayin da kasar ke shigo da katako daga kasashen ketare.

...

Yana son farfado da girbin katako don samar da ayyukan yi ga matasa tare da share fagen bunkasa kasuwanci a masana'antar da ke kunshe da biliyoyin daloli.

Yanzu masu shigo da katako da kayan daki daga ketare za su fara biyan haraji yayin da Ruto ke neman a rika kera su a cikin kasar.

Me ya sa aka haramta sare itatuwan?

Kokawar da jama'a ke yi kan illar sare itatuwa ba bisa ka'ida ba, kamar raguwar yawan ruwa a manyan kogunan Kenya, ya kai ga ayyana dokar hana sare dazuzzuka a cikin watan Fabrairun 2018.

Shugaban kasar na wancan lokaci Uhuru Kenyatta ya ce matakin zai taimaka wajen gyara dazuzzukan da suka lalace da kuma bunkasa aikin dashen itatuwa.

An kuma yi ma wa hukumar kula da gandun daji ta Kenya (KFS), wace ita ce hukumar da ke da alhakin kare dazuzzukan, cikakken garambawul cikin tsarinta domin dakile cin hanci da rashawa da kuma inganta ayyukanta.

...

Mene ne sakamakon haramcin?

Wani binciken da aka yi a baya bayan nan, ya nuna cewa an yi asarar kudaden shiga da suka kai Sh4 billion (£22,300,000, $28,300,000) da kuma ayyuka 44,000 cikin shekaru shidan da dokar ke ci.

Gandun daji na bayar da gudummawar kashi 3.6 cikin dari na yawan arzikin da aka samu daga abin da aka sarrafa a cikin gida a Kenya.

Kenya ta sa ran samun bunkasar gandun dajin kasar da kashi 10 cikin dari a shekarar 2022.

Rahoton binciken tattalin arziki na 2020, ya nuna cewa yawan gandun dajin ya karu daga kadada 141,600 a shekarar 2018 zuwa kadada 147,600 a shekarar 2019, karuwar sama da kashi hudu kadai cikin dari.

Mene ne shirin gwamnati na kiyaye gandun daji?

Gwamnatin Ruto ta bayyana wani tsari na shuka bishiyoyi guda biliyan 15 cikin shekaru 10 domin bunkasa gandun dajin kasar.

Ana yawan kwatanta masana'antar katako a matsayin ɗaya daga cikin sassan Kenya mafi samun riba, inda dubban matasa marasa aiki ko ilimi suka samu aikin yi a cikin shekaru goma da suka gabata.

Yankunan da suka dogara da katako don rayuwa galibi na gundumonin da ke bangaren Rift Valley, musamman ta bangaren da ke kudanci.

Me masana ke cewa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu fafutukar kare muhalli sun bayyana damuwarsu a shafin Twitter kan matakin na Ruto, inda wasu ke ikirarin cewa shugaban na warware wasu alkawuran da ya dauka na yaki da sauyin yanayi.

“Ranar bakin ciki ga itatuwa a Kenya yayin da aka dage dokar hana sare itatuwa. 'Yan Kenya suna nuna damuwa - ta yaya za a kare gandun daji?

''Bishiyoyin da aka dasa ba za su biya bukatun raya muhalli, da zamantakewa, da al'adu ba, kamar yadda William Ruto yake da ikon sawa ko hanawa,"in ji masaniyar ilimin halittu Dr Paula Kahumbu.

Masaniya a harkan yanayi Elizabeth Wathuti ta yi jayayya da ra'ayin cewa masu saran itace za su zabi tsofaffin bishiyoyi su bar kanana "tsari ne wanda ba za a yi amfani da shi yadda ya kamata ba. "

Hukumar fafutukar kare muhalli ta GreenPeace Africa ta roki shugaba Ruto da ya gaggauta dawo da dokar hana sare itatuwa a duka dazuzzuka.

Haka kuma hukumar na son a bar kungiyoyi masu zaman kansu su rungumi dazuzzuka domin kula da itatuwan asali.

...

Wasu darussa za a iya koya?

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kasar Gabon ta kula da dazuzzukanta tun farkon shekarun 2000 wajen samar da wuraren shakatawa na kasa guda 13, daya daga cikin wadannan na cikin jerin wuraren tarihi na UNESCO.

Dazukan kasar suna tsotse tan miliyan 140 na carbon dioxide a kowace shekara, wanda ya yi daidai da cire motoci miliyan 30 daga kan titi a duniya.

A lokacin COP26 shugabannin duniya sun yi alkawarin kawo karshen sare itatuwa nan da shekarar 2030.