Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaran da duniya ta manta da su a yaƙin Yemen
Idan ana neman inda tashin hankali ya samu wajen zama, to bai wuce unguwar da ake kira al-Rasheed da ke birnin Taiz, na ƙasar Yemen ba.
Birni ne wanda tsaunuka da mayaƙan ƙungiyar Houthi suka yi wa ƙawanya, a wannan unguwa, hatta ƙananan yara ba su tsira daga bala'in yaƙi wanda ƙasashen duniya suka kawar da idonsu a kai ba.
Wannan yaron marar jiki da ke da baƙin gashin kai, yana amfani da sandar da ke taimaka masa wajen tafiya, ya shiga gaba domin zagayawa da tawagar BBC a wannan unguwa.
A cikin kangon gidansu, Bader ya zauna bisa ɓuraguzan bulo, ana iya ganin gundulen ƙafarsa da aka datse.
Ɗayar ƙafarsa mai lafiyar babu takalmi, babban yayan sa Hashim na gefen shi suna tattauna irin ƙalubale da tashin hankalin da suka fuskanta.
Wani makami da ƙungiyar Houthi ta harba da sanyi safiya cikin watan Oktoba na a shekarar da ta gabata, lokacin da yaran ke kan hanyar su ta zuwa gida daga makaranta, makamin ya gogi ƙafar dama ta Bader, kamar yadda mahaifin sa al-Harbi Nasser al-Majnahi ya shaida wa BBC.
Tun bayan wannan lokacin yaran ba su sake komawa makaranta ba.
"Komai ya canza gaba ɗaya", in ji shi yayin da yake zaune kan katifa ya ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya.
"Ba su fita wasa da sauran yara. Sun zama nakassasu. Suna jin tsoro, kuma suna cikin matsancin tunani."
A cikin wata murya mai ban tausayi dake nuna yaro ne karami wanda bai kai shekaru 9 ba da yake da su, Hashim ya ce yanason komawa makaranta domin ci gaba da karatu
"Inason karatu"inji shi. Wakiliyar BBC ta tambayi Bader ko shima yanason komawa makaranta? sai ya ce "Eh, amman an yanke mani ƙafa ta ya ya zani koma makaranta?
Mahaifin su ya ce ba za su koma cikin wannan sabon zangon karatu da za'a fara ba, saboda ba shi da kuɗin motar da zasu riƙa shiga don zuwa makarantar.
Ya kuma ce baya da wata hanyar da zai iya tserartar da iyalansa da ga wannan masifar.
"Duk da dai muna jin tsoro, bamu da kwnaciyar hankali, amman ba za mu iya rayuwa wani wuri ba, saboda kuɗin hayar zai yi yawan da ba zamu iya biya ba. Saboda haka dole mu ci gaba da zama nan ko mu mutu ko mu yi rai"
Ƙasar ta fara shiga yaƙin basasa, sai daga bisani abokanan adawa na yankin suka rurara wutar rikicin, ta hanyar nuna goyon baya ga ɓangarorin adawa.
Saudiya ta goyi bayan gwamnati, inda Iran ta goyi bayan Houthi waɗanda yawancin su ƴan shi'a ne.
A watan Satumban 2014, ƙungiyar Houthi suka ƙwace ikon babban birnin kasar, Sanaa.
Saudiya ta tura dakarun ta da suka samu goyon bayan Amurka da Birtaniya, ta kuma yi alkawarin mayar da ikon babban birnin karkashin gwmanati, sai dai yunƙurin na Saudiya ya gamu da cikas, inda ta kwashe tsawon shekara takwas tana ɓarin wuta ba tare da cin nasara ba.
A yanzu haka, Saudiya na neman hanyar janye a ƙalla sojojin ta cikin gaggawa.
Yanzu haka a birnin Taiz, Bader da Hashim ƙarar yaƙin da ake gwabzawa ne ke tada su daga bacci.
"Naji fashewar abubuwa," inji Bader," kuma kwararrun maharba bindiga. Suna harbe komai da ke makwabtan mu. Ina jin kamar za'a samu fashewar wani abu kusa da ni, ko kuma a tada gidan mu gaba ɗaya.
Tawagar BBC ta yi tafiya kaɗan daga gidan su Bader, sai suka ci karo da wani ƙaramin yaro mai shekaru uku a ƙofar gida yana sanye da launin ruwan ɗorawa, ya yi shiru, anyi masa ƙafar ƙarfe a damar sa.
Mahifin sa ne ya taimaka masa ya miƙe tare da sumbatar goshin shi.
Lamarin da ya faru da Amir ya faru ne rana guda da Bader da Hashim sa'o'i kaɗan ne tsakani.
Amir ya je wani gida da ke tsallaken titi a lokacin da mamakin ya faɗa masu, ya kashe kawun sa da ɗan kawun sa mai shekaru shidda.Amir ya tsira sai dai ya samu gagarumin raunin da ba zai manta da shi ba.
Sharif ya bayyana irin ciwo da damuwar da Amir ke ciki.
"Ya na tuna duk wani abu da ya faru a lokacin da lamarin ya faru har aka isa asibiti da shi, ya riƙa cewa 'Wannan ne abunda ya faru da kawuna da ɗan uwana.'
"Yana yawan magana kan hayaƙi da jinin da ya gani. kuma idan ya ga yara na wasa ya na jin haushi sai ya ce ' Ni bani da ƙafar da zani yi wasa da ita.'"
Kowane gida da ke unguwar akwai matakin fargabar da suke fuskanta.
Munir mai yara huɗu, kusan ya fi kowa rayuwa cikin fargaba saboda gidan su na makwabtaka da dabdalar mayakan Houthi.
"Kwararren mai harba bindiga na gaban mu,"inji Munir, ya rarrafa zuwa jikin tagar falon shi." Ina iya ganin shi daga nan idan na buɗe labule. Duk wanda ya fita wajen lambu zai harbe shi"
"Muna rayuwa cikin fargaba anan Taiz. Mutane basusan lokacin da wani makami zai faɗa masa ba ko ƙwarraren mai harba bindiga ya harbe shi. Da yardar Allah zaman lafiya zai dawo a Yemen."
A hanyar tawagar BBC ta barin gidan Munir, sai suka ci karo da babban ɗan sa, Muhammad, ɗan shekaru 14, wanda ke bisa keken guragu. A lokacin da aka kai hari a makarantar su, sauran yaran sun tsere sun bar shi a baya. yanzu yana cikin fargabar kada irin haka ta faru a gidan su, kuma iyalansa za su iya shiga matsala idan sukayi kokarin ceto shi.
Wani mai bada maganin gargajiya, ya shaidawa BBc cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu , ya ba yara kusan 100 da makamin ƙungiyar Houthi ya haddasa aka yanke wani ɓangare na jikin su magani.
Yawancin yaran da aka kashe a Taiz sun mutu ne sakamakon harbin ƴan Houthi, yayin da wasu ƙalilan suka mutu sakamakon makami mai linzami da Saudiya ke harbawa a sararin smaniyar ƙasar, wasu kuma dakarun tsaron kasar ne ke kashesu. Kowane ɓangare suna da alhakin kashe yara a yankin.
Rikicin na Yemen ya yi sauƙi, tun bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani, inda aka samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata shidda.
Ba a yaƙi sosai amman kuma babu kwanciyar hankali a yankin.
Ƙasashen Saudiya da Iran sun shirya tsakanin su, wanda abu ne mai kyau da zai taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin Yemen.