Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace dama ƙungiyoyin Afirka ke da ita a gasar kofin duniya ta Fifa Club World Cup?
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
Gasar Kofin Duniya ta kulob-kulob ko kuma Fifa Club World Cup da za a yi a Amurka za ta bai wa tawagogin Afirka huɗu da za su buga gasar ƙarin dama.
Ƙungiyar Al Ahly ta Masar da ta lashe kofin Champions League na Afirka sau 12, da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu, da Wydad Casablanca ta Morocco, da Esperance ta Tunisia, su ne za su nemi murƙushe takwarorinsu na Turai da sauran nahiyoyin duniya.
Babu wani kulob daga Afirka da ya taɓa lashe kofin gasar ta Club World Cup a tarihi, inda biyu ne kawai suka taɓa kaiwa wasan ƙarshe a karo 20 na gasar.
Amma yanzu akwai ladan da za a samu - jimillar abin da za a bayar ya kai dala biliyan ɗaya, inda aka ware dala miliyan 475 don bai wa waɗanda suka fi ƙoƙari.
Duk da cewa Fifa ta ƙara yawan wasannin da aka saba bugawa duk da yawan wasannin da ke gaban ƙungiyoyi, kocin Esperance Maher Kanzari ya ce "dama ce" ga 'yanwasa su bayyana kansu.
Wakiltar Afirka da alfahari
Kanzari ya buƙaci tawagar 'yanwasansa ta tashi tsaye lokacin da za su fafata da Flamingo, da Chelsea, da Los Angeles FC a Rukunin D.
"Muna sane da cewa idanun masoya ƙwallo na kanmu, kuma za mu yi bakin ƙoƙarinmu wajen nuna ƙwarewar 'yanƙwallon Afirka."
Wannan ne karon farko da ƙungiyar da ta lashe kofin zakarun nahiyar Afirka huɗu za ta shiga gasar tun 2019.
Ita kuwa Al Ahly za ta kara da kulob ɗin su Messi ne Inter Miami a wasan farko ranar Lahadi, kafin karawa da Palmiras da kuma Porto.
Wydad za ta buɗe nata wasan ne da gwabzawa a Rukunin G da Manchester City, sai kuma Juventus da Al Ain ta Daular Larabawa.
Bambancin lada
Duka ƙungiyoyin Afirka da za su buga gasar ta Kofin Duniya za su samu ladan aƙalla dala miliyan 9.55 - irin wanda wakilai daga Asiya da Arewacin Amurka da Amurka ta Tsakiya za su samu.
Wannan adadi ya ninka dala miliyan huɗu da Palmyras ta samu bayan l;ashe kofin zakarun nahiyar Afirka.
Duk da haka, ladan da ƙungiyoyin Afirka za su samu shi ne mafi ƙanƙanta. Wakilan Kudancin Amurka shida za su samu ladan dala miliyan 15.21, yayin da za kungiyoyin Turai 12 za su samu kudi daga dala miliyan 12.81 zuwa 38.19.
Nasarar da ƙungiya ta samu a matakin rukuni za ba ta dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan ɗaya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan dala miliyan 40.
Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun ƙarin dama a nan gaba.
"Wuri ne da ya kamata mu nuna ƙwarewarmu a matsayinmu na ƙungiyoyin Afirka," in ji Hersi - shugaban ƙungiyar kulob-kulob ɗin Afirka a hirarsa da BBC.
"Akwai buƙatar mu yi fafutikar neman ƙarin dama a nan gaba."
Idanu a kan Afirka?
Wasu na fatan ƙungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kuɗi idan aka kwatanta da takwarorinsu.
Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar Caf ta ƙaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin ɗigimin da aka yi lokacin da aka fara ta, mai tawaga huɗu wadda kulob ɗin Sundowns ya lashe.
Kulob ɗin na Pretoria da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka Caf, Patrice Motsepe ya mallaka, ya kafa kansa a matsayin jagora a harkar ƙwallon ƙafar Afirka - ita ta lashe kofunan gasar Afirka ta Kudu tara na baya-bayan nan.
Sundowns za su kara da Ulsan HD da Borussia Dortmund da Fluminense a Rukunin F, abin da wani magoyi ƙwallon ƙafa ya ce zai taimaka wajen nasararta a gasar ta Club World Cup.
"Idan muna maganar faɗin duniya, ba na ji Sundowns sun kai shaharar sauran ƙungiyoyin," in ji Wayne Magwaza, wani mai adawa da Sundowns ɗin.
"Idan ta yi ƙoƙari sosai, hakan zai shafi yadda mutane ke kallon ƙwallon ƙafar Afirka ta Kudu."
Fargabar gajiya
Lokacin gudanar da gasar Club World Cup ya shafi harkokin wasa a Afirka, ta yadda sai da aka matsar da lokacin gudanar da gasar Kofin Ƙasashen Afirka wato Afcon 2025 daga watannin Yuni da Yuli zuwa ƙarashen shekarar ta 2025.
Tuni ƙungiyar ƙwararrun 'yanƙwallo ta duniya ta shigar da ƙara a shekarar da ta gabata kan abin da suka kira "nuna ƙarfin iko" da Fifa ta yi wajen faɗaɗa gasar, amma kuma duk da haka ba a dakata ba.
Ɗanwasan Najeriya na AC Milan Samuel Chikwueze ya ce kulob ɗin nasa ba zai buga gasar ba, amma duk da haka yawan wasannin da za su buga sun yi yawa.
"Lokaci ɗaya da 'yanwasa za su huta shi ne daidai lokacin da suka saka gasar," a cewar ɗanƙwallon mai shekara 26.
"Abu ne mai wahala buga wasanni masu yawa. Mutum zai gajiyar da ƙafufuwansa da tunaninsa ta yadda ma ba zai ji daɗin taka ledar ba."
Su kuwa 'yankallo kodayaushe aka yi maganar cin kofi su ne a gaba.
"Zuwa gasar Club World Cup ba ƙaramin abu ba ne," in ji wani magoyin bayan Sundowns mai suna Mothabela.
"Yadda suke taka leda yana ba mu ƙwarin gwiwa. Muna da ƙwarin gwiwar za su kai matakin kusa da ƙarshe."