Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern da Marseille na rububin Rashford, Manchester United na shirin bayar da aron Antony
Bayern Munich da Marseille sun bi sahun Paris St-Germain wajen neman ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekara 26 daga Manchester United. (Teamtalk)
Manchester United na shirin sauraron tayin aro kan ɗan wasan Brazil Antony, mai shekara 24 a watan Junairu. (Insider Kwallon Kafa)
Tsohon dan wasan Italiya da Roma Francesco Totti, mai shekara 48, ya ce wataƙila ya koma taka leda bayan ƙungiyoyin Seria A sun tuntube shi. (Gazzetta Dello Sport)
Arsenal da Aston Villa da Newcastle na zawarcin ɗan wasan Red Bull Salzburg mai shekara 20, Oscar Gloukh. (Caught Offside)
Bayer Leverkusen na shirye-shiryen tafiyar kocinta Xabi Alonso a bazara mai zuwa, Inda tsohon dan wasan Sifaniyan ke jan hankalin Real Madrid da Manchester City, idan Pep Guardiola ya tafi. (Sky Germany)
La Liga na neman izinin hukumar kwallon kafa ta Sifaniya da Uefa da kuma Fifa domin gudanar da wasan da Barcelona za ta yi da Atletico Madrid a watan Disamba a birnin Miami. (Mail)
Arsenal na shirin zawarcin Brentford dan kasar Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, sakamakon tagomashin da ya ke samu a farkon kakar wasa ta bana. (Football Insider)
Arsenal na nazarin hanyoyin kara girman filin wasan Emirates. (Times)
Julen Lopetegui ba ya fuskantar sallama a matsayinsa na kocin West Ham duk da rashin fara kkakr wasan bana da ƙafar dama da kungiyar ta yi. (Guardian)
Arsenal da Chelsea na sa ido kan dan wasan Juventus ɗan ƙasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24.
Everton na shirin miƙa tayin £17m kan ɗan wasan Besiktas ɗan kasar Turkiyya Semih Kilicsoy mai shekaru 19. (Kontraspor)