Hanyoyi bakwai da za su taimaka wajen inganta muhalli a 2025

mutum

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Rage ɗumamar yanayi babban aiki ne, to amma idan mutane suka haɗa hannu akwai abubuwan da za su yi domin rage hayaƙin da ke ɗumama duniya.

A 2024, an samu ƙaruwar ɗumamar duniya da maki 1.5 a ma'aunin salshiyas, ƙaruwa da ba a taɓa ganin irin ta ba cikin shekara ɗaya, lamarin da ya ƙara haifar da ƙaruwar buƙatar rage hayaƙi a duniya.

Mafi yawan ayyukan da ake buƙata don magance sauyin yanayi sun zarta yadda mutane ke aiki - daga haɓaka makamashi da ba ya gurɓata muhalli, da daina amfani da man fetur da iskar gas da ma'adinin kwal.

Amma bincike ya nuna cewa ayyukan ɗaiɗaikun mutane za su iya taimakawa.

Yawaita cin ƴaƴan itatuwa da ganyayyaki

abinci

Asalin hoton, Getty Images

Ana hasashen cewa zuwa 2033 za a samu shanu biliyan biyu, da aladu biliyan ɗaya da kaji biliyan 32 da awaki da tumaki kusan biliyan uku a cikin duniyarmu, wato kusan dabobbi biliyan 38.

Yayin da duka waɗannan dabbobi ke neman hanyar rayuwarsu, sun kasance suna fitar da iskar gas ta methane da nitrous oxide - sinadari mai tasiri wajen ɗumama duniya fiye da sinadarin carbon sau 265.

Ba a maganar ƙasa da ruwan da ake buƙata don kiwon su.

Amfani da jirgin ƙasa fiye da na sama

jirage

Sufuri shi ne babbar hanyar fitar da hayaƙi a Amurka, inda yake samar da kashi ɗaya bisa uku na hayaƙin da ake fitarwa a ƙasar, sannan kuma yake samar da kashi 16 cikin 100 na hayaƙin da ake fitarwa a duniya.

Shiga jirgin sama koyaushe na iya haifar da ƙaruwar sinadarin canbon, don haka rage shiga jirgin saman shi ne zai taimaka wajen inganta muhalli.

Amfani da jirgin ƙasa ko mota ko ƙaramar mota maras ɗaukar mutane da yawa na taimakawa wajen rage sinadarin na carbon.

Idan za ku yi amfani da ƙananan motoci, ku shiga wadda take da ƙarancin amfani da fetur ko makamashin da yake fitar da hayaƙi mai yawa domin raguwar gurɓata muhalli.

Haka idan kana tuƙa ƙaramar mota ka yi ƙoƙarin taƙaita amfani da ita, musamman ga gajerun tafiye-tafiye da za ka iya yi da ƙafarka, domin rage hayaƙin da take fitarwa. Kuma hakan zai taimaka wajen inganta lafiyar jikinka.

Sayen tufafi kaɗan

mai sayar da tufafi

Asalin hoton, Getty Images

Tufafi na bayar da muhimmiyar gudumawa wajen ɗumama yanayi, inda yake samar da kashi 8 zuwa 10 cikin 100 na hayaƙin duniya, fiye da jiragen sama da na ruwa idan aka haɗa.

A kowane daƙiƙa, ana ƙona babbar motar tsummokara a duniya, a cewar gidauniyar Ellen MacArthur Foundation mai kula da muhalli.

Muhimmin abin da za ka yi shi ne sayen tufafi ƙalilan, musamman waɗanda aka yi da tufafin da ke mutuwa da wuri.

Haka kuma kana iya amfani da tufafin haya, ko sayen gwanjo, kamar yadda yanzu haka gwanjo ke zaman kashi 9 cikin 100 na tufafin Amurkawa, inda ake sa ran zai ƙaru a nan gaba.

Rage sinadarin carbon da dabbobi ke fitarwa

Muna son kiwon dabbobi, amma bincike na nuna cewa ajiye dabbobi ba shi da amfani ta fuskar inganta muhalli. Ɗauki kare ko mage da muke kiwo, su kaɗai kan fitar da sinadarin carbon mai nauyin fiye da tan uku a tsawon rayuwarsu, kwatankwacin hayaƙin da ƙaramar motar da ta yi tafiyar kilomita 12,070 ke fitarwa.

Akwai hanyoyin da za ka iya rage sinadarin carbon da dabbobin ke fitarwa, misali ta hanyar abincin da suke ci.

Alal misali cin kifi da wasu nau'in ƙwari kan taimaka wajen rage sinadarin carbon da dabbobin ke fitarwa.

Haka yana da kyau mu riƙa musanya ledojin da muke amfani da suke wajen kwasar kashin dabbobin zuwa abubuwan da ƙona su baya lahani ga muhalli.

sauya na'urorin ɗumama ɗakuna

wata mace

Asalin hoton, Getty Images

Ɗumama ɗakunanmu a lokacin huturu na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen makamashi. Har yanzu man fetur ne kashi 60 cikin 100 na makamashin da muke amfani da shi wajen ɗumama ɗakuna, kuma fanni na ɗaya daga cikin fannonin da ke samar da hayaƙi.

Idan muna son kashe na'urorinmu ko rage amfani da su, da me za mu sauya su domin ɗumama ɗakunanmu?

A birnin Brussels, masana kimiyya da injinoni sun fara tunanin fara gine-gine da wasu kayayyaki da ke ɗumama muhalli.

Haka ƙasar Canada ta fara irin wannan aiki domin rage amfani da na'urorin ɗumama ɗakuna.

Cibiyar Makamashi ta Duniya ta ƙiyasta cewa nan da 2030, za a samu raguwar na'urorin ɗumama ɗakuna da ke fitar da hayaƙin carbon da aƙalla tan 500, kwatankwacin hayaƙin da ƙananan motoci ke fitarwa a duka nahiyar Turai a yau.

Zuba jari da kuɗinka don inganta muhalli

Wata mace

Asalin hoton, Getty Images

A duk lokacin da muke maganar inganta muhalli, ba mu fiye tunani kan kuɗinmu ba.

Amma yadda muke adana kuɗimu, ko zuba jari ko kashe su zai iya tasiri wajen magance sauyin yanayi.

Bankuna su ne manyan cibiyoyin da ke ɗaukar nauyin kamfanonin makamashi, yayin da kake ajiye kuɗinka a banki, kai tsaye ko a fakaice kana taimaka wa hakan.

Idan ba ka yarda da kamfanonin da bankinka ke bai wa bashi ba, kana iya janye kuɗinka daga ciki zuwa wani bankin da kake ganin ya fi mayar da hankali wajen gina al'umma, wanda ba ya bayar da bashi ga kamfanonin da ke samar da makamashi mai gurɓata muhalli.

Haka batun yake ga kuɗinka na fansho, kuɗin fansho na daga cikin manyan kuɗaɗen da bankuna ko kamfanoni ke amfani da su wajen bai wa masu zuba jari.

Mutane da dama ba su san inda ake zuba jarin kuɗaɗensu na fansho ba. Kuma yana da kyau ku riƙa tambayar cibiyar da ke tasarrufi da kuɗinku na fansho yadda yake yi da su.

Rage amfani da robobi da ledoji

Roba ko leda ta kasance ɗaya daga cikin muhimman ɓangarororin rayuwarmu. An samu ledoji masu ɗimbin yawa a tekun Antarctic da cikin dabbobin da ke rayuwa a ƙarƙashin teku da abincinmu da ruwan da muke sha.

Ana sa ran samun ruɓanyar robobin da muke amfani da su zuwa aƙalla nunƙi ɗaya nan da 2050. Idan muka ci gaba da ƙera robobi a duniya nan da 2050 za su iya cin kashi 20 cikin 100 na man da ake samarwa.

Kuma fiye da kashi 99 na robobi ana ƙera su ne da sinadaran da ake samu daga makamashin fetur.

Yana da matuƙar wahala mu daina amfani da robobi, amma za mu iya ɗaukar matakan rage amfani da su, wannan ba duniya kaɗai zai amfanar ba, har da lafiyarmu, saboda akwai robobin da ake alaƙantawa da matsalar rashin haihuwa.

Yi ƙoƙari ku maye gurbin ledojin da kuke amfani da su a shugananku da wasu abubuwan zuba kaya.