Me ya sa gine-gine ke yawan rushewa a Legas?

Masu aikin ceto sun ƙoƙarin ceto waɗanda suka maƙale a wani bene mai hawa uku da ya rushe a Legas ta Najeriya a 2 ga watan Mayun 2022.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An hango wasu mutane na ta ƙoƙarin ceto waɗanda gini ya danne a Legas a 2022
    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 6

A wannan shekarar kacal, aƙalla gida ɗaya ne ke rushewa a duk mako biyu.

Duk da cewa za a iya tantance asarar dukiyar da aka yi, ba za a iya tantance asarar rayukan da aka yi ba.

Yadda ɓaraguzai ke yawaita a tsakanin gidajen, ya nuna gazawar gwamnati da kuma yawaitar zarge-zargen da ake yi cewa ƴan kwangila suna cuwa-cuwa domin rage kashe kuɗi.

Akwai tsare-tsare, sannan akwai ƙa'idojin kula da gine-gine da masu lura - amma tsare-tsaren ba su aiki.

Waɗanda suka yi laifi ba sa fuskantar hukunci, wanda hakan ya sa babu abin da ya sauya.

A Legas, jihar da wani masani ya bayyana wa BBC cewa ita ce, "babban birnin rushewar gidaje a Najeriya," aƙalla gidaje 90 ne suka rushe a cikin shekara 12 da suka gabata, inda sama da mutum 350 suka mutu, kamar yadda cibiyar kula da aikin injiniyanci ta 'Najeriya Council for the Regulation of Engineering in Nigeria' ta bayyana.

Daga ciki, rushewar ginin da ta fi muni akwai wanda ya auku a 2021.

Sunday Femi yana zaune wasu ƴan mitoci ne a Ikoyi lokacin da ya ji rushewar wani bene mai hawa 21 da ake tsaka da aikinsa ya rushe, inda mutum 42 suka mutu.

Bayan ginin ya yi ruku'u, sai ƙura ta turbuɗe shi.

"Kamar kowa da ke kusa, sai nima na shiga cikin wajen domin ganin ko zan iya taimakawa wajen ceto waɗanda suka maƙale. Na san wasu da suka mutu, kuma ina tuna lamarin a kullum," in ji shi a lokacin da yake tuna abin da ya faru kimanin shekara uku da suka gabata.

Masu aikin ceto suna duba baraguzan ginin mai hawa 21 da ya rushe ana tsaka da aikin ginawa a Legas a 2 ga Nuwamban 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗaruruwan mutane sun taru suna jiran tsammanin ganin halin da ƴan'uwansu suke ciki bayan ginin ya rushe a 2021
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutumin wanda ya kasance yana sayar da lemun kwalba da ruwa ga masu aikin ginin.

An katange wajen da ƙarfe, amma har yanzu ina iya hango karyayyun kankare daga nesa.

Da zarar ka je za ka shiga wajen, da ƴansanda za ka haɗu waɗanda za su bayyana maka cewa an hana su barin mutane suna shiga sai dai jami'an gwamnati.

Kamar yadda aka hana mutane daga shiga wajen, haka ma aka rufe bincike a kan lamarin - tun a shekarar 2022 gwamnan jihar ya karɓi rahoton binciken maƙasudin rushewar ginin.

BBC ta sha yunƙurin tambayar gwamnatin Legas domin ganin shawarwarin da aka fitar a cikin rahoton rushewar ginin na Ikoyi, amma ba ta samu ba.

A wani hukunci a game da rayukan da aka rasa, Babbar alƙaliyar kotunan majistare ta Legas, Oyetade Komolafe ta alaƙanta rushewar ginin da sakacin hukumomi, waɗanda aka ɗora wa alhakin bibiya tare da amincewa da tsarin ginin da ma ginin.

Mutane suna ta ƙaruwa a Jihar Legas, inda ake hasashen sun haura miliyan 20.

Kafin a fara gini, sai an samu izinin farawa daga hukumar bayar da izinin gine-gine. Sannan masu sanya ido daga Hukumar Kula da Ingancin Gine-Gine su zo su duba filin, sannan su riƙa zuwa lokaci bayan lokaci suna duba yadda aikin ginin ke tafiya.

Sannan Hukumar Kula da Ingancin Kaya ta Najeriya ta tabbatar da cewa ingantattun abubuwa ne kawai ƴan Najeriya suke amfani da su.

Amma a lokuta da dama, an yi watsi da wasu ƙa'idojin.

Makarantar Ƙwararrun Magina ta Najeriya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Kare Gine-gine daga Rushewa sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin daɗinsu a kan yawaitar rushewar gine-gine mai taken gine-gine da inganci a cikin ayyukansu na na Ranar Magina ta shekarar 2022 a Legas a ranar Asabar 12 ga Maris, 2022.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An sha gudanar da zanga-zanga a kan kira ga masu gine-gine da su riƙa bin ƙa'idoji.

A cikin ofishin Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA), ko'ina a tsanake yake - babu alamar ɗaga hankali game da irin matsalolin da ake fuskanta.

Kakakin hukumar, Olusegun Olaoye ya tabbatar da cewa suna shan suka, amma ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi musu cewa suna ƙarɓar cin hanci domin bayar da takardar amincewa da yin gini.

"Yanzu haka muna da masu zuwa duba gine-gine guda 300, amma muna ƙoƙarin ƙara yawan su," in ji shi.

Masana ma sun yi amannar cewa ana buƙatar ƙarin masu bibiya da dubiya.

Muhammad Danmarya, masanin gine-gine ne, ya bayyana cewa ana buƙatar masu zuwa duba gine-gine su kai dubbai.

"Mutum 300 sun yi kaɗan a jiha kamar Legas, ya kamata kowace ƙaramar hukuma ta samu aƙalla masu zuwa duba gine-gine da masu bibiya guda 57, sannan kuma Legas na da guda 57," in ji shi.

"Kusan ko'ina ka je a kowane lokaci za ka tarar ana gine-gine, don haka akwai buƙatar a riƙa zuwa dubawa a kowane lokaci."

Amma saboda wani giɓi da aka samu, wasu gurɓatattun kamfanoni suna amfani da damar wajen yin cuwa-cuwa ta hanyar wasu ƙa'idojin gine-ginen.

"Kawai suna zuwa ne su ɗauke mu a duk lokacin da suke da aiki, su biya mu idan mun kammala," in ji lebura Habu Isah wanda ya yi shekaru yana aikin leburanci a wuraren gini.

"Ban taɓa samun wani horo ba, da kaina na iya komai."

Amma koda an samu inda aka kauce wa amfani da wasu daga cikin ƙa'idojin, hukumar kula da gine-ginen ba ta ɗaukar mataki.

"A iyakar sanina, ban taɓa ganin an hukunta wani ba a baya saboda rushewar gini a Legas," in ji Mista Olaoye na LASBCA.

"Na san yawaitar lamarin na ɗaga hankali, amma muna aiki domin shawo kan lamarin."

Wata makarantar firamare ta rushe a Legas.
Bayanan hoto, Mutum 20 ne suka mutu bayan makarantar firamare ta rushe a Maris na 2019 a Legas.

Ana kuma zargin akwai sa hannun ƴan siyasa wajen hana hukunta masu laifi.

"Idan kana da alaƙa da masu mulki, koda ka yi laifi a rushewar gini, babu abin da zai faru," in ji wani ɗan siyasa a Legas wanda ya buƙaci a sakaya sunansa.

"Mun sha samun irin wannan, inda wasu manyan gine-ginen suke da alaƙa da ƴan siyasa kuma babu abin da ya faru.

"A Najeriya idan kai mai kuɗi ne, kuma ka san manyan mutane, za ka iya kauce wa matsaloli."

Yanzu da gine-gine 19 suka rushe a bana, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Legas ta bayyana, akwai yiwuwar matsalar a wannan shkerar ta fi ƙamari a cikin shekara goma da suka gabata.

Amma wataƙila an koyi wasu darussa.

Shugaban hukumar bayar da lasisin injiniyoyi (COREN) ya bayyana a kwanakin baya cewa ƙasar ba ta da cikakken abin da ake buƙata domin gudanar da binciken abubuwan da ke faruwa.

"Ba mu da ƙwararru da kayan aikin da ake buƙata domin gudanar da binciken," in ji farfesa Sadiq Abubakar.

A yanzu da babu wata mafita, magina da sauransu za su cigaba da tafiya ne a haka, tare da sadaukar da rayuwarsu.

Ƙarin bayani: Andrew Gift