Abin da muka sani kan ginin da ya rufta wa ɗalibai a Jos

Jos ta jihar Filato

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar ‘yansanda a jihar Filato da ke arewacin Najeriya ta bayyana cewa yara 22 ne suka mutu sakamakon ruftawar gini mai hawa biyu a wata makaranta a birnin Jos na jihar.

A cikin bayanin da ta fitar, rundunar ta tabbatar da cewa dalibai 154 lamarin ya rutsa da su, sai dai an samu nasarar ceto yara 132 wadanda ke karbar magani a asibiti.

A ranar Juma’a ne gini mai hawa biyu na makarantar Saint Academy - da ke unguwar Busa-buji a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa - ya rufta ne a lokacin da ɗaliban ke ɗaukar darussa, yayin da wasu ke rubuta jarrabawa.

Iyayen yara sun cika harabar makarantar bayan faruwar lamarin, domin sanin halin da ƴaƴansu ke ciki, yayin da waɗanda suka ga gawarwakin ƴaƴansu suka kiɗime.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) na ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo sauran mutanen da ginin ya danne.

Iyayen ɗalibai sun garzaya asibitin birnin Jos domin sanin halin da ƴaƴansu ke ciki.

Likitoci sun rika kira ga al'umma su bayar da gudunmowar jini domin ceto rayukan ɗaliban da aka kai asibitin.

..

Ana tunanin cewa makarantar na kunshe ne da yara sama da 1,000.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani mazaunin yankin Abel Fuandai ya shida wa BBC cewa dan abokinsa ya mutu a rushewar ginin kuma ya ce “lamarin ya yi muni”.

Har yanzu dai babu masaniya kan abin da ya haddasa ruftawar ginin makarantar duk da cewa hukumomi na dora laifin lamarin kan rashin yin ginin a wurin da ya dace.

Sai dai ruftawar ta faru ne bayan kwanakin da aka kwashe ana zabga ruwan sama a jihar ta Filato.

Lokacin da ya yi magana da kamfanin dillancin labaru na AFP, daya daga cikin daliban da abin ya rutsa da su wanda ke kwance a asibiti, Wulliya Ibrahim ya ce: “na shiga aji, bayan kamar minti biyar sai na ji wata kara, daga nan ban san me ya faru ba, sai kawai na tsinci kaina a nan.

Wani mazaunin yankin, Chika Obioha ya ce ya ga gawarwaki da yawa yayin da ake zakulo mutane.

Ana yawan samun ruftawar gine-gine a Najeriya cikin shekarun nan, inda masu lura da al’amura ke dora laifin hakan kan rashin ingantaccen aiki da rashin amfani da kayan aiki masu inganci da kuma rashawa.

A 2021, akalla mutum 45 ne suka mutu lokacin da wani bene ya rushe a jihar Legas da ke kudancin Najeriyar.

'Mun ji ƙara mai ƙarfi'

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida yadda al'amarin ya faru, Samuel Akpan ya yi wa BBC ƙarin bayani kan yadda abin ya faru.

Samuel, wanda ke cikin mutanen da suka kai ɗauki wajen ganin an ceto yaran da abin ya rutsa da su tun kafin isowar ma'aikatan ceto ya ce yana cikin wani kanti da ke kusa da makarantar ne a lokacin da suka ji wata ƙara.

"Lokacin da na ji ƙara, sai na ce mene ne ya faru? Sai na ga ashe ginin mai hawa biyu ne ya rushe kuma ɗaliban da ke ciki suna rubuta jarrabawa ne, sai muka ruga domin ganin abin da ke faruwa.

"Amma da farko sai muka rasa abin da za mu yi, babu abin da za mu yi amfani da shi wajen ɗaga ɓaraguzai, dole ne mu jira ma'aikata su zo."

Ya bayyana cewa sun samu nasarar ceto wasu mutane ƙalilan waɗanda ke da rai, sai dai kayan aikin da ke hannunsu ba wani abin a zo a gani ba ne.

Ya bayyana cewa akwai sauran mutane a ƙarƙashin ginin.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda ginin makarantar ya rufta:

Jos ta jihar Filato

Asalin hoton, Getty Images

Jos ta jihar Filato

Asalin hoton, Getty Images

..

Asalin hoton, Getty Images

...

Asalin hoton, Getty Images