Mutumin da ya shafe kwana 61 binne cikin akwatin gawa

Mick Meany s'entraîne pour son défi, à la veille de ses funérailles.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mick Mean lokacin da yake kwance cikin akwatin gawa, kwana guda kafin binne shi
    • Marubuci, Dalia Ventura
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mundo News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wannan labari ne mai matuƙar ɗaukar hankali da ya faru da wani ɗan asali Ireland duk da cewa ba a ƙasar lamarin ya faru ba.

Mutumin mai suna Mick Meany, ɗa ne ga wani manomi daga gundumar Tipperary a ƙasar, kuma kamar wasu ƴan ƙasar sun yi ƙaura zuwa Ingila tun bayan yaƙin duniya na biyu, domin neman aiki don tallafa wa iyalansu.

Burinsa a rayuwa shi ne zama zakaran dambe, amma kuma sai ya tsinci kansa a matsayin lebura.

Mafarkinsa na zama zakaran dambe ya gamu da cikas ne bayan da ya gamu da hatsari, lamarin da ya raunana masa hannunsa.

To sai dai ya samu wani burin daga wani hatsarin da ya auku da shi.

Wani rami da yake tonawa ne ya rufta masa, a lokacin da yake maƙale cikin ramin ne kuma, wani sabon burin ya zo masa na: Kafa tarihin zama mutumin da ya fi jimawa a binne cikin akwatin gawa da ransa.

Abu ne da ba a saba gani ba, amma irin wannan ya zama wata gasa ta burgewa a Amurka tun shekarun 1920 da 1966, wani matuƙin jirgin ruwa ya ɗauki akwatin gawar zuwa Ireland, inda aka binne ta tsawon kwana 10 a karon farko.

To sai dai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da lokacin da Digger O'Dell, wani Ba'amurke wanda ya kwashe kwana 45 binne ƙarƙashin ƙasa a Tennessee, don haka Meany ya sa a ransa cewa sai ya karya wannan tarihi.

Gasar binne mutum da ransa

Un malade du choléra soulève le couvercle de son cercueil, terrifié.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Batun binne mutane da ransu ya jima yana girgiza mutane da dama, ciki har da Tsohon shugaban Amurka, George Washington.

Me ya sa yawan maimaita wani abu da ake kallo a matsayin hanyar cutarwa a tarihi ke ƙoƙarin zama abin burgewa?

Abin da ke sa mutane aikata wannan da alama ya bambanta, kama daga watayawa da kafa tarihi da yunƙurin samun kuɗi, zuwa yunƙurin ɗaukar hankalin mutane.

Alal misali, O'Dell, ya riƙa binne kansa har sau 158 a lokacin da yake raye, lamarin da ya sa ya samu kuɗi, ta hanyar tallata wurare ko kayayyaki.

A shekarar 1971 ya binne kansa na ƙarshe domin yunƙurin neman saukar da farashin gas.

Le bras de Meany dépassait du trou du cercueil, une bière à la main.

Asalin hoton, Getty Images

Meany na zaune a Kilburn, wata gunduma a arewacin Landon, wanda ƴan asalin Irekan suka fi yawa a cikin.

Ya kasance yana yin abubuwa da dama na ban mamaki, ciki har da ɗaukar mutane a kan kujera da haƙoransa.

Haka kuma ɗan kasuwa ne, inda a wasu lokuta kuma yake taɓa wasan dambe, har ya taɓa yunƙurin karawa da Muhammad Ali a Dublin.

A lokacin da Meany ya bayyana ƙudirinsa na binne kansa da rai, mutane sun riƙa ba shi shawara amma ya nace.

Ƴarsa, Mary ta ce a lokacin da matarsa ta ji labarin ƙudirin wani mutum a radiyo na kafa tarihin binne kansa na tsawon fiye da kwana 45, ta san cewa mijinta ne saboda ya sha fada mata ƙudirinsa.

Ya so yin hakan a ƙasar Ireland, amma danginsa suka hana shi, saboda fargabar zai iya mutawa, irin mutuwar da cocin katolika ke ɗauka a matsayin mutuwa mummuna.

Amma Mary ta ce Meany bai fahimci hakan ba.

A ranar 21 ga watan Fabrairun 1968, ya aikata abin da mutane da dama suka roƙe shi kada ya yi.

Ƙarƙashin ƙasa

Danginsa sun shiga damuwa, saboda bayanin da ya zo musu cewa Meany ya ci ''abincinsa na ƙarshe'' a gaban ƴanjarida, kafin shiga cikin akwatin gawar.

Ya sanya tufafi mai launin shuɗi, ya ɗaure jikinsa, sannan ya shiga cikin akwatin mai tsayin mita 1.90 da faɗin mita 0.78, da aka shimfiɗa wa wata katifa ta musamman.

Ya ɗauki wasu abubuwa muhimmai kafin ya kulle kansa, kafin ya bayyana cewa ''Nakan yi hakan ne domin matata da ƴata da kuma girmama Ireland.''

A lokacin da aka binne shi a ƙarƙashin ƙasa, Mista Meany ya riƙa numfashi ta wasu bututun ƙarafuna da aka maƙala a cikin akwatin, inda ta nan ne kuma aka riƙa tura masa abinci da ruwan sha da sigari da jaridu da littattafai domin karantawa ta hanyar amfani a wata ƙaramar fitila.

Au moment où ils sortent le cercueil, entourés de nombreuses personnes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin da aka tono shi, mutane da dama sun taru domin yi masa maraba.

Bayan kammala shirya akwatin gawar an shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki domin binne shi.

Bikin ya ɗauki hankali manyan mashahuran mutane da suka haɗa da fitaccen ɗan wasan dambe Henry Cooper da tsauraruwar fina-finai Diana Dors, waɗanda suka je domin bankwana da akwatin gawar Meany.

Ya yi magana da mutanen da suka halarci jana'izar binne akwatin tasa ta hanyar wata wayar hannu da aka maƙala ta cikin akwatin, da za ta ba shi damar yin magana da mutanen duniya.

Bikin ya samu halartar ƴanjarida da dama, sai dai bikin binne gawar ya rasa karsashi sakamakon ɓarkewar yaƙin Vietnam.

To amma a lokacin tono gawar, danginsa sun yi duka mai yiwuwa domin ganin batun tono shin ya bazu a duniya.

'Daga bajinta zuwa ɗimuwa'

A ranar 22 ga watan Afrilun shekarar da ta gabata aka tono shi bayan mako takwas da kwana biyar.

An yi bikin tono shi a gaban makaɗa da maraya da ƴanjarida da sauran masu kallo.

An shigar da akwatin tasa zuwa cikin wata babbar motar ɗaukar kaya a gaban dandazon jama'a.

Meany na sanye da tabarau domin kare idanunsa daga hasken rana a lokacin da aka buɗe akwatin.

Ya kasance cikin datti, da gemu buzu-buzu da gashin kansa alamun ya jima a keɓe.

"Zan iya ƙara wasu kwanaki 100 binne cikin ƙasa, in ji shi. "Na yi farin cikin kafa wannan tarihi a duniya."

Gwajin lafiya da aka yi masa ya tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiyarsa.

Meany toujours dans le cercueil, peu après son exhumation

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Meany a lokacin da aka buɗe shi daga cikin akwatin gawa, inda ƴan'uwa da dangi suka rungume shi.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayanai sun nuna cewa ba tarihi kaɗai Maeny ya kafa ba, domin kuwa ya samu wasu alfanun masu yawa sanadiyya abin da ya aikata.

Ƴarsa Mary ta ce an yi masa alƙawarin zagayawa da shi zuwa wasu ƙasashen duniya tare da akwatin tasa, tare da kuɗi fam 100,000 idan ya karya tarihin O'Dells.

Haka kuma akwai alƙawarin gida mai hawa uku a birnin Dublin da ya kai kimanin dala 12,000 a 1971.

Bayan shafe kwanaki 61 binne a ƙarƙashin ƙasa, Meany ya karya tarihin,

sai dai har yanzu ba a cika masa alƙawarin zagayawa da shi zuwa wasu ƙasashen duniya ba.

Haka ma burinsa na shiga kundin bajinta na duniya ya dusashe, domin kuwa kundin adana abubuwan bajinta na Guinness ya ƙi amincewa da bajintarsa, saboda kundin bai tura wakilai domin tantance binne shin ba.

To amma kasancewa ƴanjarida da dama sun halarta, babu tababa game da shafe waɗannan kwanaki 61 binne cikin ƙasa.

Sai dai watanni bayan haka wani mutum mai suna Emma Smith ya karya wannan tarihi bayan shafe kwanaki 101 ƙarƙashin ƙasa a Skegness a Ingila.

Labarin Meany ya ƙara fitowa fili ne bayan mutuwarsa a 2003 cikin wani shirin Fim na musamman mai taken "Buried Alive/Beo Faoin Fód", wanda aka riƙa nunawa bukukuwan bayar da kyautuka.