Da gaske ne magungunan naƙuda na gargajiya na aiki?

    • Marubuci, Isidore Kouwonou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 7

A wajen daƙin haihuwa na asibitin Mamadou Diop da ke birnin Dakar, wasu mata uku masu juna biyu da suka kusa haihuwa na kaiwa da komowa.

Ɗaya daga cikinsu na nuna alamun gajiya: ta fara tafiya a hanklali, yayin da sauran biyun suka tafi da sauri.

Bisa ga bayanin da suka yi mana, wata ungozoma ce - da ba mu iya samun damar magana da ita ba - ta umarce su da yin wannan zirga-zirga, wani nau'i ne na motsa jiki yayin jiran lokacin haihuwa.

Tuni dai wadda ta fara gajiya a cikinsu ta riga ta fara nuna alamun fara naƙuda.

Khady Ndiaye ta bayyana cewa ta fuskanci irin wannan yanayin shekaru biyu da suka gabata, lokacin da ta haifi ƴarta ta fari.

Yanzu haka tana shirin haihuwa na biyu. "Amma ba ka sabawa da shi saboda zafi," in ji ta.

Ba mu dai samu damar magana da ungozomar asibitin ba. Sai dai a cewar Dr. Jean-Claude Togbé, babban likita a wani asibiti a Lomé na ƙasar Togo, wanda BBC Africa ta samu damar tuntuba ta ce motsa jiki na taimaka wa mace ta hanyar daidaita kwanciyar jaririn domin haihuwa ya kasance cikin sauri da kuma sauƙi.

"Don haka ne muke roƙon mata masu juna biyu su riƙa motsa jiki, musamman ƴan makonni kafin su haihu," in ji shi.

Amma dai a kula, akwai wasannin motsa jikin da ba a ba da shawarar a yi a cikin waɗannan lokutan.

"Yoga, alal misali, ba shi da kyau ga mata masu juna biyu," in ji likitan.

Baya ga wasanni da ƙwararru suka bayyana fa'idarsu ga mata masu juna biyu don sauƙaƙa haihuwa, an kuma samar da wasu hanyoyin da wasu ke amfani da su wajen rage raɗaɗi da kuma guje wa ɗaukar dogon lokaci ana naƙuda.

Yin amfani da wasu jiƙe-jiƙe ko ganyayyakin shayi wurin neman sauƙin zafin naƙuda ya zama ruwan dare a wasu ƙasashen Afrika.

Ko shayi da kuɓewa na maganin naƙuda?

Wasu mata masu juna biyu a wasu lokuta suna fuskantar alamomi kamar nauyin jiki, ciwon jijiya, da nauyi ko kumburar ƙafafu.

A cewar Afefa Bolou, wata ungozoma a Lomé, waɗannan alamomin suna nuna cewa an kusa sauka kenan.

Amma tun kafin wannan lokacin, wasu matan kan yi amfani da magungunan gargajiya don hanzarta ko matso da lokacin naƙuda.

Wannan shi ne abin da Tassi Mama, wata tsohuwar ungozomar gargajiya kuma mai bayar da maganin gargajiya a Lome, Benin ta bayyana.

"Waɗannan ba tsire-tsire ba ne masu rikitarwa da za su iya jefa mace cikin haɗari ba ne," in ji ta.

A cewarta, haɗa jiƙon busasshen ganyen gwanda yana taimakawa wajen daidaita kawanciyar jariri da kuma sauƙaƙa haihuwa.

"Ya kamata ku fara a wata na bakwai. Mace mai ciki tana buƙatar shan jiƙon da safe da kuma yamma," in ji ta.

Ta kuma ba da shawarar shan ruwan dafaffiyar kuɓewa a cikin watan ƙarshe na ciki.

"Wannan yana taimaka wa jaririn ya sauko kuma yana sauƙaƙa haihuwa."

Marceline Attiogbé, ɗaya daga cikin majinyatan, ta tabbatar da cewa ta bi wannan shawarar.

"Na gwada shan jiƙon ruwan gwanda kuma komai ya tafi daidai. Na sha jiƙon da safe da kuma da yamma. A cikin wata na tara, na ɗan dakata sai na haɗa shi motsa jiki," in ji ta.

Ta bayyana cewa ta yi amfani da wannan dabarar ce bayan an shaida mata a asibiti cewa jaririn nata ya na da girma, wanda hakan na iya sanya ta cikin wahala.

Hakanan ana ɗaukar shayin ganyen Raspberry yana taimakawa wurin rage raɗaɗin naƙuda.

Wani camfi ne da Tassi Mama ke bayar da shawarar amfani da ita, yayin da take tunatar da mu cewa waɗannan ganyayen shayin ba cikakkun magunguna ba ne.

"Ya kamata ku nemi shawara kafin amfani da su don guje wa duk wata matsala."

A cewar ƙwararriyar abinci mai gina jiki, Angèle Kouto, ganyen raspberry na ɗauke da sinadarin da ake kira frangine, wanda ke da tasiri a cikin mahaifa, ya kuma sanya haihuwa ya zo da sauƙi.

Duk da haka, duk da shaharar su, waɗannan magungunan gargajiya suna haifar da mabambantan ra'ayoyi.

Yayin da wasu ke ganin suna da amfani, ƙwararru da yawa—musamman likitoci—suna taka tsantsan ko ma suna adawa da amfani da su.

A cewarsu, barin mata su yi amfani da waɗannan jiƙe-jiƙen na iya jefa su cikin haɗari.

"Akwai haɗura..."

Afefa Bolou, wata ungozoma ce da gwamnati ta bai wa lasisi sama da shekara goma da suka gabata a Lomé, ta ce babu wani likita da zai ba mace mai ciki shawarar shan shayin ganye domin sauƙaƙa haihuwa.

A cewarta, akwai yiwuwar yin amfani da shi ba daidai ba, kuma ana fama da ƙarancin bayanan kimiyya game da sinadarai da ke cikin waɗannan ganyayyakin.

Ta ƙara da cewa: "Sai dai idan mai cikin ta kai haihuwa, ƙafafunta na fama da kumburi.

A wannan yanayin, mace mai ciki tana iya shan ruwan ƙanƙara. Hatta ƙwararrun likitoci sun ba da shawarar yin hakan."

A cewar ungozomar, shan shayin ganye ba tare da shawarar likita ba na iya zama haɗari.

"A wasu matan, muna lura da lokacin haihuwa cewa ruwan da ke cikin mahaifa yana kasancewa da launi, ta hanyar yi musu tambayoyi ne muka fahimci cewa suna shan shayin ganye," in ji ta.

A cewarta, hakan na iya kai ga mutuwar jariri.

Har ila yau, majinyata suna zuwa asibiti suna bayyana cewa ba za su iya jin ƙarar bugun zuciyar jaririn da ke ciki, wanda aka saba aunawa lokacin da ake ɗauke da ciki da kuma naƙuda.

"Kuma idan muka ɗauki horton cikin, sai mu ga cewa an rasa jaririn, ita kanta majinyaciyar ba ta san adadin shayin ganyen da ya kamata ta sha ba don guje wa irin wannan yanayi," in ji Afefa Bolou, wadda ke ba da shawarar gujewa amfani da waɗannan magungunan yayin da ake da ciki.

Sai dai ta fayyace: "Wani lokaci mukan nemi mata masu juna biyu da su wanke kansu da jiƙon ganyen gwanda.

Wannan yana taimaka wa jarirai saukowa cikin sauƙi kafin a haife su. Amma kuma yana da illa, domin bai kamata a yi amfani da shi tsawon lokaci ba."

A cewarta, marasa lafiya da ke shan wannan jiƙo na tsawon lokaci suna fuskantar barazanar "fashewar ruwan haihiwarsu kafin ma su shiga naƙuda."

Lallai ganyen gwanda ya na ɗauke da sinadarai da ke kama da oxytocin ko syntocon, masu iya haifar da zuwan naƙuda da wuri.

Wannan lamari yana haifar da sakin ruwan cikin mahaifa, wanda ke da mahimmanci ga jaririn ya shaƙi iska a cikin mahaifa.

Wannan na iya haifar da mutuwar jaririn ko, idan an haife shi da rai, ya wajabta ba shi iskar oxygen cikin gaggawa.

Rashin haƙurin waɗansu majinyata

A cewar ungozomar, wani lokaci iyayen da ke raka mata masu juna biyu zuwa wurin haihuwa ne ke haifar da matsala ga ma'aikatan kiwon lafiya.

"Yayin da muke yin ƴan gyare-gyare, mun fahimci cewa mahaifiyar mai cikin ko surukarta ta ba ta shayin ganye ko kuma wata ƙwayar da za ta haifar da naƙuda," in ji ta.

Sai matar mai ciki ta fara kururuwa, ta ci gaba, amma ba wanda ya gaya wa ungozomar ainihin abin da ya faru.

"Sai da ruwa ya ƙare ne muka gano abin da ya faru a bayanmu, wasu iyayen na zargin mu da barin ƴaƴansu mata su sha raɗaɗin haihuwa, don haka suke gaskata ba su waɗannan abubuwan sha."

Ta bayyana cewa waɗannan lamuran suna tasowa ne musamman a lokacin da ake sa ran mace ta haihu da kanta.

Wannan shi ne saboda wasu iyaye - ko ma marasa lafiya da kansu - suna buƙatar "magani" kafin haihuwa, wanda yanzu ungozoma ke ƙi bayarwa akai-akai.

Ta bayyana cewa babu wani magani da zai rage ko kuma ya hana raɗaɗin naƙuda.

"Majiyyatan mu da masu raka su dole ne su bar mu mu yi aikinmu, in ba haka ba suna jefa rayuka cikin haɗari."

Ms. Bolou ta ci gaba da cewa: "A wannan lokaci mai muhimmanci, babu wani abu da za mu yi.

Muna nan muna sa ido, mu na tafiya tare da matar, muna ki wa da komowa, mu koya mata dabarun numfashi, da kwantar mata da hankali, ta yadda za ta iya haihuwa cikin sauƙi."

A yau, a cibiyoyin kiwon lafiya, in ji ta, yawan matan da ke haihuwa da kansu na ƙaruwai, ba tare da yin amfani da magunguna na yau da kullum ba.

"Za ku lalata mahaifar ku a banza idan kuna shan abubuwa ba kaƙƙautawa," in ji ta.

Shawara: A nemi shawarar likita ko masani a kodayaushe kafin shan kowane irin magani.