Waiwaye: Rashin naɗa sabbin jakadu da sabon taken Najeriya
Wannan maƙala ce da ke kawo muku labarin muhimman abubuwan da suka faru a makon jiya.
Ƴan bindiga sun kashe sojojin Najeriya biyar a Abia

Asalin hoton, Getty Images
A makon jiya ne wasu ƴan bindiga sun kashe aƙalla sojojin Najeriya biyar a wani harin ba-zata da suka kai a jihar Abia da ke Kudu maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da rikicin ƴan aware.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar a yau Juma'a, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Edward Buba.
Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai sojojin sun ɗora alhakin hakan kan ƴan awaren da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra.
Sanarwar ta ce "Dakarun Najeriya na alhinin mutuwar waɗannan sojoji kasancewar duk wani soja da aka rasa a fagen daga mummunan rashi ne.
EFCC ta ƙwato naira biliyan 156 a shekara guda

Asalin hoton, PRESIDENCY
A cikin makon jiya ne dai shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin Hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede ya ce hukumar ta samu nasarar ƙwato naira biliyan 156 daga ranar 29 ga waan Mayun 2023 zuwa 29 ga watan Mayun 2024.
Mista Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani shiri na musamman kan yaƙi da rashawa ranar Laraba a Abuja.
Ya ƙara da cewa daga kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da na ƙasashen waje da ma kudin intanet wato na kirifto.
Yayin da yake jawabi a madadin shugaban hukumar, sakataren EFCCn, Mohammed Hammajoda ya ce hukumar na nuna damuwarta kan yadda matasa da ɗalibai ke ƙara shiga harkokin damfara ta intanet da aka fi sani da 'yahoo-yahoo'.
Najeriya ta buƙaci a daina ruwan wuta a Gaza nan take

Asalin hoton, Reuters
A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne Najeriya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Gaza, ta kuma yi kiran a gaggauta wanzar da zaman lafiya a yankin.
Wata sanarwa da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya fitar ta ce gwamnatin ƙasar ta damu da halin da fararen hula suka shiga yanzu haka a Gaza, saboda yaƙin Isra'ila da Hamas.
Harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai kudancin Gaza a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ya kashe mutum aƙalla 45, mafi yawan su mata da ƙananan yara, lamarin da ya ƙara yawan hare-haren da aka kai kan fararen hula tun bayan ɓarkewar yaƙin.
Najeriya ta sauya taken ƙasa

Asalin hoton, HANNIBAL HANSCHKE
A cikin makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da amfani da tsohon taken ƙasar mai suna "Nigeria: We Hail Thee".
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a yau, wanda tuni aka yi amfani da shi lokacin da Tinubu ya yi wa taron majalisar na haɗin gwiwa jawabi a yau Laraba.
Shi ne karon farko da majalisar ta rera taken tun bayan daina amfani da shi shekara 46 da suka wuce.
Shugaba Tinubu ya ce taken na nuna bambancin al'adu, da kuma wakiltar kowane ɓangare tare da zimmar taka rawa wajen ƙulla 'yan'uwantaka.
'Rashin kuɗi ne ya hana Shugaba Tinubu naɗa sababbin jakadu'

Asalin hoton, AMB. YUSUF TUGGAR/TWITTER
A ranar Talatar makon jiya ne ministan harkokin waje na Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce rashin isasshen kuɗi ne ya haifar da jinkiri wajen naɗa jakadun ƙasar a ƙasashe.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron bayanin ayyukan ma'aikatun gwamnatin ƙasar a yau Talata a Abuja, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar babbar matsalar kuɗi da ta tattalin arziƙi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tun bayan da shugaban ƙasar ya mayar da dukkanin jakadun ƙasar na waje a ranar 2 ga watan Satumban 2023, bai naɗa wasu sababbi ba.
Ya kamata ƴan Najeriya su saka wa gwamnatin Tinubu albarka - Buhari

Asalin hoton, State House
A cikin makon jiya ne tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan mulki, yana mai neman 'yan ƙasar su goya wa gwamnatin jam'iyyarsu ta APC baya "don ta yi nasara wajen gina ƙasa".
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ya wallafa a shafukan zumunta, Buhari ya kuma nemi 'yan Najeriya "su saka wa gwamnatin ta Tinubu albarka" kuma "su ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa".
"Haka nan, Buhari ya yi wa gwamnatin Tinubu fatan gama mulki cikin nasara," in ji Garba Shehu.











