'Niyyar kisa suka yi' - BBC ta gano yadda jami'an tsaron Kenya suka harbi masu zanga-zanga

- Marubuci, Bertram Hill & Tamasin Ford
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
- Lokacin karatu: Minti 7
BBC ta bankaɗo mambobin rundunar tsaron Kenya waɗanda suka kashe masu zanga-zangar ƙarin haraji a majalisar ƙasar a watan Yunin bara.
Binciken da BBC ta yi kan wasu hotuna sama da 5,000 ya kuma nuna yadda waɗanda aka kashen basa ɗauke da makamai sannan su ba barazana ba ne.
Dokokin ƙasar - wadda ke Gabashin Afirka - sun bayar da damar zanga-zangar lumana don haka mace-macen ya janyo haifar da Allah wadai daga Al'umma.
Duk da umarnin da kwamitin majalisa ya bai wa hukumar ƴansandan Kenya mai zaman kanta (IPOA) ta gudanar da bincike game da mutanen da aka kashe a titunan Nairobi har yanzu babu wani rahoto da aka miƙa wa majalisar kuma ba wanda aka kama.
Tawagar BBC ta dubi hotuna da bidiyon da masu zanga-zangar da ƴan jarida suka ɗauka a ranar.
Mun auna lokacin da aka ɗauki hotunan ta hanyar amfani da lokutan da ke jikin hotuna da bidiyon da aka ɗauka kai-tsaye yayin da ake wallafa su a shafukan sada zumunta.
Binciken kisan kai uku da aka yi a majalisa ya kai ga tabbatar da wasu harbin bindiga da aka yi amfani da bindigogin wani ɗansanda da wani soja.
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC ya ce lamarin ya faru ne yayin da ƴanmajalisar dokokin Kenya suka zauna don kaɗa ƙuri'ar ƙarshe kan dokar haraji mai sarƙaƙiya, yayin da masu zanga-zanga suke kan tituna daga waje, ranar Talata 25 ga watan Yunin 2024.
Gargaɗi: Labarin ya ƙunshi hotuna masu tayar da hankali

Masu zanga-zangar matasa ne da ake kira Gen Z, waɗanda suka yi gangami a shafukan sada zumunta, sun fara kwarara tsakiyar Nairobi da safe a yanayin zanga-zanga ta uku mafi girma tun bayan gabatar da dokar harajin kuɗi ranar 9 ga watan Mayu.
Fitaccen mai fafutika, Boniface Mwangi wanda ya halarci zanga-zangar ya bayyana cewar ''biki ne mai ƙayatarwa''.
"Yara sun zo da na'urar ƙara sauti, da abinci da ruwan sha, don haka biki ne."



Zanga-zangar da aka yi a farkon makon dai ta sanya ƴan majalisar sanya haraji kan buredi da man girki da ababan hawa, da kuma wani haraji da zai ƙara tsadar kayayyaki da suka haɗa da audugar mata.
Amma game da matakan haɓaka dala biliyan 2.7 (£ 2bn), gwamnati ta ce tana buƙatar yanke dogaro da rance daga waje, kamar ƙarin harajin shigo da kayayyaki da wani harajin kan harkar asibitoci na musamman
"A karon farko dai batu ake na al'ummar Kenya da ma'aikata da matsakaitan masu kuɗi da talakawa akan masu riƙe da muƙamai'', in ji Mwangi.
Burin masu zanga-zangar shi ne kutsawa zauren majalisar, inda ake kaɗa kuri'ar ƙarshe.
Da misalin ƙarfe 9: 30 na safe ne ƴan majalisar dokoki suka kammala shiga zauren majalisar.
Daga waje kuma, dubban masu zanga-zange ne ke dannawa titin majalisar daga gabas da arewa da yammacin birnin.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A wurina rana ce kamar kowacce," cewar Ademba Allans mai shekara 26 ɗalibin koyon aikin jarida.
''Mutane na watsa zanga-zangar kai tsaye a shafukansu na TikTok da Instagram, ya yinda gidan telebijin ke watsa abin da ke faruwa kai-tsaye,'' in ji shi.
Da farko dai an sanya wa zanga-zangar shinge an kuma harba hayaƙi mai sa hawaye, daga nan sai ƴan sanda suka fara amfani da bindigogin ruwa da harsashan roba.
Da misalin ƙarfe 13:00 na rana sama da mutum 100,000 sun fantsama a tituna.
Allans ya ƙara da cewa ''adadin mutane ya fara ƙaruwa, kuma an fara kama mutane'',
"Ƴansanda sun fito ko ina. Suna ƙoƙarin kora mutane baya. Har kan motocin da suke fesa ruwa mutane ke ƙoƙarin hawa."
Duk da yamutsin da ke gudana a waje, ƴan majalisa na cikin an fara kaɗa ƙuri'a.
Da misalin ƙarfe 14:00, masu zanga-zanga sun kora ƴansanda baya daga arewa maso gabashin majalisar.
Da misalin ƙarfe 2:14 na rana ƴanmajalisar suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudirin dokar, ƴan majalisa 195 ne suka amince, yayinda 106 suka ƙi amincewa .
Ƴan adawa sun fice nan take talakawa suka samu labari daga waje.
"A dai dai wannan lokaci ne mutane suka fara cewa komai zai faru sai mun shiga zauren majalisar mun nuna wa ƴan majalisar cewar mun yi imani da abinda mu ke gwagwarmaya a kai," in ji Allans.
Da misalin ƙarfe 2:20 na rana ne, masu zanga-zangar suka samu damar kutsawa ta shingen ƴan sanda suka danna titin da zai kai su majalisa.
An banka wa wata motar ƴansanda da aka yi watsi da ita wuta. An karya katangu masu zanga-zanga sun samu hanya don takawa zuwa da ƙafa zuwa cikin majalisar.
Afkawar ba ta yi nisa ba masu tsaron majalisar suka tarwatsu su.
A lokacin da wannan lamari ke faruwa, ƴan jarida na naɗar abinda ke faruwa daga kowacce kusurwa.
Ɗaya daga cikin bidiyon ya nuna wani ɗansanda cikin farin kaya yana ihu yana cewa "uaa!", wadda le nufi ''kashewa'' a harshen Swahili, jim kaɗan kuma sai wani ɗan sanda ya durƙusa daga nan sai aka ji sautin harbin bindiga sai kuma mutane bakwai daga cikin masu zanga-zangar suka faɗi ƙasa.
David Chege mai shekara 39 injiniyan na'ura mai ƙwaƙwalwa kuma malami a makarantar koyar da yara ƙanana a coci da Ericsson Mutisya mai shekara 25 tsohon mahauci su ne waɗanda aka harba.
Akwai kuma wasu mutane biyar da suka jikkata ɗaya daga cikinsu ya samu shanyewar rabin jiki.

Hotuna sun nuna yadda Allans ɗalibin karatun aikin jarida ya ke riƙe da tutar Kenya yayin da yake ƙoƙarin tarar da Chege wanda ya jikkata sakamakon harbin bindiga
Ko waye ya harba bidigar?
A cikin bidiyo jami'in da ya yi ihu, "uaa!", bayan mai harbin ya rufe kamera. Sai dai BBC ta kwatanta kayan jikinsa da na sauran ƴansanda da ke wurin
Bayan harbin ma, an ci gaba da jiyo ɗan sandan mai farin kaya yana cewa da abokan aikinsa su harbo, bai damu da ɓoye kansa ba sunan sa John Kaboi.
Shaidu da dama sun bayyana wa BBC cewar a ofishin ƴansanda na tsakiyar Nairobi yake.
Kaboi bai ce komai ba da aka tuntuɓe shi.
Ba wanda aka kama game da mutuwar Chege ko Mutisya. BBC ta gano cewar ba wanda ke ɗauke da makami a tsakanin su.


Amma ba waɗannan ba ne kaɗai mutanen da suka rasa rayukansu. Kashe-kashen sun fusata masu zanga-zangar har suka yi yunƙurin kutsawa majalisar.
Da misalin ƙarfe 2:57 na rana suka yi nasara.
Hotunan sun nuna yadda suke fasa katangar tare da kewaye harabar majalisar.
Da yawa sun ɗaga hannayensu sama yayin da wasu ke ɗauke da kwalaye ko tutar Kenya.
An yi harbi don gargaɗin masu zanga-zangar, amma sai suka durƙusa ƙasa sannan suka ci gaba da dannawa zuwa ginin tare da ɗaukar abinda ke faruwa ta wayar salula.
Suna shiga ciki , komai ya dagule. Aka karya ƙofofi aka kunna wa wani sashe na majalisar wuta yayin da ƴan majalisar suka fice daga ginin.
Mummunan lamari ne amma bayan mintuna biyar hotunan sun nuna yadda suka fice kamar yadda suka shiga.
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, ya yi nazarin hotuna fiye da 150 da aka ɗauka mintuna kafin da kuma bayan harbin Shieni.
Mun kuma iya gano sojan da ya harbi kan Shieni ta baya daga tazarar mita 25, sai dai shi ma ba mu san sunansa ba.
"Bidiyon ya nuna yadda abin ya faru ƙarara," a cewar Faith Odhiambo, shugabaar ƙungiyar lauyoyi ta Kenya.
"Burinsu shi ne kashe masu zanga-zanga. In ba don haka ba ai za su iya kama shi, amma tun da suka harbe shi a ka - ai ƙarara niyyar kisa suka yi.
Sai dai rundunar sojin Kenya, (KDF), ta shaida wa BBC cewa rundunar ƴansandan Kenya, IPOA ba ta gabatar mata da buƙatar bincikar jami'inta kan wannan zargi ba.
Tana mai cewa a shirye KDF take don yin aiki bisa tsarin doka, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ɗora mata alhaki.
Bayan harbin an ƙara ganin Allans, inda ya jagoranci kwashe mutane. Bidiyon da aka ɗauka ya nuna shi ɗauke da wani mutum da jini ke zuba daga ƙafafunsa.
"Na ji tsoro, cewa iyayena ba za su sake ganina ba,'' in ji shi.
"Amma kuma ina tsoron barin mutane su mutu, bayan kuwa zan iya taimaka musu.''
A lokacin magaribar ranar 25 a watan Yuni, ƙasar ta kasance cikin tashin hankali. Bayan mako guda na zanga-zanga, hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Kenya ta bayyana mutuwar mutum 39, yayin da mutum 361 suka samu raunuka.
A wannan maraicen ne kuma Shugaba William Ruto ya gode wa jami'an tsaron ƙasar saboda ''kare martabar ƙasar, daga ''gungun masu laifi'', waɗanda suka ''yi amfani da zanga-zangar wajen cimma burinsu''.
Kwana guda bayan haka ne aka jingine ƙudirin.
"Bayan sauraron ƙorafin mutanen Kenya, waɗanda suka nuna rashin gamsuwa da kuɗirin, na haƙura,'' kamar yadda shugaban ya bayyana a jawabin da ya yi ta gidan talbijin, yana mai cewa ba zai sanya hannu kan ƙudirin ba.
Amma har ya zuwa yau babu wani jami'in tsaro da aka gurfanar kan zargin kisa, babu wata sanarwa a hukumance da aka wallafa game da haka.
Ƙarin rahoto daga masu tace bidiyo na BBC, Valeria Cardi da Emile Costard.











