Abu 16 da Tinubu ya ce zai mayar da hankali a kansu idan ya yi nasara

Fadar shugaban Najeriya

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na shugaban kamfe, shi ne ya ƙaddamar da kundin a Fadar Shugaban Ƙasa

A ranar Juma'a ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da kundin manufofinsa ga 'yan ƙasar waɗanda yake fatan aiwatarwa idan suka zaɓe shi a babban zaɓe na 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na shugaban kamfe, shi ne ya ƙaddamar da kundin da suka yi wa laƙabi da "Tsarin Inganta Najeriya" yayin bikin da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, babban Najeriyar.

Tuni babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar suka ƙaddamar da nasu kundin tare da fara yawon nema n ƙuri'u a zaɓen na watan Fabarairu mai zuwa.

Sauran jam'iyyun adawa na ci gaba da shirin shiga yaƙin neman ƙuri'un, yayin da jam'iyyu kamar Labour Party (LP) da New Nigeria Peoples Party (NNPP) ba su kai ga fito da nasu manufofin ba.

Mun duba abu 16 da kundin manufofin na APC ya ƙunsa, waɗanda ta ce za ta mayar da hankali a kansu.

'Yan APC

Asalin hoton, State House

Tsaron ƙasa

Tinubu ya saka matsalar tsaro a matakin farko a kundin manufofinsa, inda ya ce yabi gwamnatin Buhari da cewa "ta yi ƙoƙari".

"Gwamnati mai ci ta yi ƙoƙari game da harkar tsaro a lokacin da ta zo. Ta tarar cewa 'yan ta'adda sun kakkafa tutocinsu a garuruwan da suka ce nasu ne," in ji shi.

Da yake bayanin abin da zai yi idan ya yi nasara, Tinubu ya ce: "Za mu bi hanyoyin ɗaukar matakan gaggawa don gyara matsalar tsaron ƙasar nan ta hanyar:

  • sauya wa rundunar soja fasali da ayyukanta
  • sabunta hanyoyin sadarwa da kayan aiki
  • ƙarfafa ikon sojoji a sararin samaniya
  • kyautata albashi da walwalarsu
  • hana ƙungiyoyin miyagu amfani da dazuka
  • tsaurara tsaron iyaka

Tattalin arziki

A cewar Tinubu, noma ne ƙashin bayan tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa "kuma haka za a ci gaba".

Sai dai ya amince cewa "yana da kyau a dinga lura da yawan al'ummarmu da ke ƙaruwa".

A cewarsa: "Haka nan, dole ne mu mayar da hankali kan matasanmu. Su ne ƙasar nan kuma gobenta. Matasa 'yan shekara 15 zuwa 35, su ne fiye da kashi 65 cikin 100 wato miliyan 130 na al'ummarmu mai yawan miliyan 200."

Wasu daga matakan da zai ɗauka:

  • Sauya tsarin kasafin kuɗi
  • Yi wa hanyoyin karɓar haraji kwaskwarima
  • Yaƙi da rashawa a aikin gwamnati da kare ɓarna
  • Haɗa kai ko kuma saita kuɗaɗen shigar gwamnati
  • Rage ciyo bashi a kuɗaɗen ƙetare saboda daidaita darajar naira

Noma

Ɗan takarar na APC ya ce ɓangaren noma zai samar da damarmaki ga 'yan Najeriya, musamman matasa, sannan kuma ya taimaka wajen faɗaɗa harkokin tattalin arziki ta hanyar rage dogaro da man fetur.

"Manoman Najeriya na cikin mutanen da suka fi kowa juriya da kuma hazaƙar ƙirƙira a duniya," in ji shi.

Matakan da zai ɗauka:

  • Adana hatsi
  • Ayyukan raya ƙasa a karkara
  • Tallafi ga manoma
  • Haɓaka noman rani
  • Babban shirin sharewa da gyara ƙasar noma

Wutar lantarki

Game da lantarki kuwa, Tinubu ya ce Najeriya na damar samar da wuta mai yawan 12,000MW, amma ya yarda cewa tana iya samar da 8,000MW ne kawai kuma ta rarraba wa 'yan ƙasa 4,000MW kacal.

"Tattalin arzikinmu a ƙuntace yake saboda gazawarmu wajen samarwa da rarraba wutar lantarki yadda ya kamata," a cewarsa.

Matakan da zai ɗauka:

  • Dakatar da cazar kuɗin bai-ɗaya ga waɗanda ba su da mita
  • Saita ƙudiri kan samar da lantarki
  • Tsarin samar da lantarki ta hanyoyi marasa gurɓata muhalli
  • Taimaka wa tsarin ƙera mita a cikin gida
  • Haskaka karkara da lantarki
  • Gyara a harkar samar da lantarki

Man fetur da iskar gas

A tsarin Tinubu, "tarihi ya nuna cewa man fetur da gas ba su ne maganin matsalolin Najeriya ba a ɓangaren tattalin arziki, amma ɓangare ne mai muhimmanci wajen ci gaban ƙasar," a cewarsa.

Matakan da zai ɗauka a ɓangaren:

  • Ƙara yawan man da ake haƙowa
  • Inganta rayuwar al'ummar da ake haƙo mai a yankunansu
  • Tabbatar da samar da mai
  • Aiwatar da gyara harkokin mai baki ɗaya

Sauran abin da manufofin suka ƙunsa

Jam'iyyar APC da ɗan takararta Tinubu sun yi alƙawarin cewa matuƙr 'yan Najeriya suka damƙ musu amanar shugabancin za su gudanar da ayyukan ci gaba a waɗannan ɓangarori masu zuwa:

  • Sufuri
  • Ilimi
  • Ɓangaren ilimi
  • Tattalin arzikin latironi
  • Wasanni, nishaɗi da al'adu
  • Bai wa matasa jari da horarwa
  • Harkokin mata
  • Shirye-shiryen zamantakewa
  • Gyaran ɓangaren shari'a
  • Sauya fasalin ƙasa
  • Harkokin waje na Najeriya