Sanwo-Olu zai yi tazarce a Lagos

An bayyana gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar a karo na biyu.

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na jihar Professor Adenike Temidayo Oladiji ya ce Sanwo-Olu ya yi nasara da ƙuri'u 762,134.

Jam'iyyar LP ce ta zo ta biyu inda ɗan takararta Gbadébo Rhode-Vivour ya samu ƙuri'u 312,329, sai kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP Abdulazeez Olajide Adeniran da ya zo na uku da ƙuri'u 62,449.

A zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a watan Fabrairu, jam'iyyar LP ce ta samu gagarumar nasara a jihar Lagos, wacce ita ce mahaifar ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, kuma a yanzu shugaba mai jiran gado.