Zinare: Mene ne amfaninsa ga tattalin arziki, kuma me ke sauya farashinsa?

.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, سمية نصر
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بي بي سي
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tun shekaru aru-aru zinare ke da daraja a wajen al'ummar duniya. Bayan kasancewarsa abin ado da ƙawa, ya kasance ƙarfe mai daraja da ke inganta tattalin arzikin ƙasashe.

Zinare na da matuƙar muhimmanci wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasashe, kuma kasuwannin hannun jarin duniya na sa ido sosai a kan farashinsa, wanda yake canjawa a kusan kullum.

Shin mene ne amfaninsa ga tattalin arziki, kuma mene ne muhimman abubuwan da suke sauya farashinsa?

Yanayin zinare

Zinare na taka rawar gani a hada-hadar kuɗi a ƙasashen duniya. Hada-hadar zinare da aka fara yi na farko a tarihi shi ne a zamanin Sarkin Lydia (wani yanki da a yanzu yake ƙasar Turkiyya) a shekarar 550 BC.

An kasance ana amfani da zinare a matsayin kuɗin hada-hada a ƙasashe da dama kafin a fara amfani da takardun kuɗi.

Amma duk da yadda takardun kuɗi suka karɓu a duniya, dole ana alaƙanta su da zinaren saboda yanayin ƙarfinsa, inda ake amfani da shi a matsayin hajar auna ƙimar kuɗi na ƙasashen duniya.

Ana aunwa yawanci abubuwa da farashin su ne da ƙimar zinare, sai a biya kwatankwacin darajar zinaren da takardar kuɗi.

A ƙarƙashin wannan tsarin, mutum zai iya kai wa gwamnati takardar kuɗi, ya ce a musanya masa da zinare.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A Birtaniya ne aka fara amfani da wannan tsarin a shekarar 1821, wanda shi ne ya haifar da ƙarshen amfani da azurfa a kasuwancin ƙarafa.

Bayan gano zinare mai yawan gaske a Arewacin Amurka, sai tsarin ya faɗaɗa zuwa ƙasashen duniya, inda ƙasashe irin su Faransa da Jamus da Amurka suka fara shiga tsarin.

Sai dai an taƙaita saya da sayar da zinare a tsarin.

An ci gaba da amfani da tsarin har yaƙin duniya na 1 ya ɓarke a shekarar 1914. Yaƙin ya sa aka koma amfani da takardar kuɗi saboda babu damar canjawa zuwa zinare, sannan ƙasashe da dama sun saka takunkumi kan fitar da zinare.

Wasu ƙasashen sun sake komawa amfani da tsarin hada-hadar zinaren bayan yaƙin duniya na 2, amma sai aka wayi gari da wani tsarin na daban na 'peg', inda Amurka ta fara saka farashi mafi ƙanƙanta na sayan zinare a dala.

A shekarar 1971, Amurka ta yi watsi da tsarin hada-hadar zinare saboda yadda ta fara shiga ƙarancinsa. Hakan ya sa kasuwannin hannun jari suka fara komawa hada-hada da takardar kuɗi, musamman dala.

Duk da cewa yanzu ba a amfani da zinare a matsayin kuɗin hada-hada a duniya, manyan bankunan ƙasashe da gwamnatoci a duniya suna ci gaba da tara shi tare da adana shi saboda inganta tattalin arzikinsu, saboda yadda farashinsa bai cika sauyawa ba.

Zinare a lokacin yaƙi

Zinare na taka muhimmiyar rawa ga ƙasashe a zamanin yaƙi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zinare na taka muhimmiyar rawa ga ƙasashe a lokacin yaƙi

Zinare na da matuƙar daraja ga mutane da ma a harkokin kasuwanci a lokacin yaƙi. Idan an mazauna wuraren da ake yaƙi za su tsere, zinare ya fi sauƙin tafiya da ma harkoki saboda duk inda suka je yana da daraja, kuma farashinsa bai cika karyewa ba kamar takardar kuɗi.

Rahotanni sun nuna cewa Rasha ta tara ɗimbin zinare a ƴan shekarun da ake ciki domin rage nauyin takunkuman da ƙasashen yamma suka lafta mata saboda yaƙin Ukraine.

Kamar yadda jaridar Telegraph ta Birtaniya ta ruwaito a ranar 3 ga watan Maris na 2022, Rasha ta tara zinare sama da dalar Amuka daga farkon yaƙin zuwa watan Yunin 2020, inda zinare ya kasance kusan kashi 23 na asusun ajiyarta.

Daɗin zuba jari

Kamfanoni da dama na jin daɗin zuba kuɗaɗe a zinare domin adana dukiyarsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamfanoni da dama na jin daɗin zuba kuɗaɗe a zinare domin adana dukiyarsu

"Zinare na da daɗin harka wajen adana dukiya," in ji Dr Nasser Qalawun, wani masanin tattalin arziki da ma'adinai da ke zauna a Landa.

Qalawun ya ce ko ɗaiɗaikun mutane da iyalai za su iya adana dukiya ta hanyar sayen zinare su ajiye, inda ya ce hakan ya fi yawa a ƙasashen Larabawa da India inda ake amfani da shi domin kwalliya da kuma adana dukiya.

Akwai bambanci tsakanin mallakar zinare domin kwalliya ko mallakarsa domin kasuwanci. Amurka da wasu ƙasashen turai suna mallakar zinare ne domin amfani da shi wajen sana'anta wasu abubuwa, kamar yadda Qalawun ya bayyana.

Ana amfani da shi wajen haɗa kwamfotoci da wayoyin salula da sauran su, sannan a ƙasashen Larabawa ana amfani da shi wajen kwalliya da kyaututtuka musamman ga mata.

"Shi ya a ƙasashen Larabawa aka fi amfani da shi a gida," Dr. Qalaun

Abubuwan da ke sauya farashinsa

Buƙatuwarsa

Buƙatuwarsa na taɓa farashinsa, kamar yadda tsarin yake a dukkan kayayyaki, inda ƙaranci ke ɗaga farashi.

Sai dai kuma yanayin yadda haƙo zinare ya yi wahalar gaske ya sa yanzu farashinsa na yawan tashi.

Matakan gwamnati

Matakan da gwamnati ke ɗauka a ɓangaren kuɗi na da muhimmanci. Idan kuɗin ruwa ya yi ƙasa, sannan kayayyaki suka yi tsada a ƙasar, farashin zinare zai tashi.

Haka lamarin yake a harkar musayar kuɗi. Idan darajar kuɗin ƙasar ya karye, dole farashin zinare zai tashi.

Yanayin ƙasa

Yanayin siyasar ƙasa da rikice-rikice da barazanar tsaro duk suna iya shafar farashin zinare, duk da zai yi wahala a iya gane ainihin yadda waɗannan abubuwan suke iya shafar farashin.

Masana tattalin arziki da dama suna alaƙanta tashin farashin zinare na yanzu da yaƙin Rasha a Ukraine, saboda masu zuba jari da dama suna fargabar narkewar kuɗinsu, don haka sai suke adana da jarinsu ta hanyar sayen zinare su ajiye.