Abubuwa uku da ya kamata a kula da su wajen zaɓar man girki

Man girki a cikin kwalabe

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Yasmin Rufo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Da zarar ka shiga kantunan sayar da kayan abinci, za ka ci karo da na'ukan man girki daban-daban kamar na kwakwa da man avocado da sauran su, kuma dukkansu kowanne na cewa yana da alfanu ga lafiyar al'umma.

Man girki da maiƙo na cikin abubuwan da suke daɗe suna haifar da muhawara mai zafi game da abinci mai gina jiki.

Kowane maiƙo yana da irin rawar da yake takawa a jiki - wasu suna ƙara tattara maiƙo mai illa ga jikin ɗan'adam, wasu suna ragewa.

Sinadarin cholesterol wani irin maiƙo ne da jiki ke samarwa a cikin hanta, amma ana iya samunsa a cikin wasu na'ukan cimaka. akwai mai illa, akwai mara illa. Idan mai illar ne ya taru sosai a jikin mutum, zai tattaru har ya toshe cikin jijiyoyin da jini ke gudana, wanda hakan ke jawo tsaiko a tafiyar jini, ko kuma ma ya hana jinin wucewa baki ɗaya.

Wannan ya sa fahimtar nau'in man girki ke da matuƙar muhimmanci domin guje wa yawan cin abinci da ke ɗauke da sinadarin cholesterol mai illa ga lafiya.

Nita Forouhi, Farfesar abinci mai gina jiki ne a Jami'ar Cambridge, ta shaida wa BBC cewa babu wani man girki guda ɗaya da za a cire shi ɗaya tal a ce yana inganta lafiya, sannan ta zayyana wasu abubuwa uku masu muhimmanci game da na'ukan man girki.

1. Kada ku guji man girkin sunflower da man gyaɗa

Man gyaɗa da nau'in sunflower ba du da tsada sosai domin litarsu ba ta wuce dala biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Man girkin vegetable da sunflower ba du da tsada sosai domin litarsu ba ta wuce dala biyu

Nau'in man girkin rapeseed ko man gyaɗa da aka fi sani da vegetable oil da nau'in sunflower suna fuskantar tsaiko a kasuwanni saboda ana tunanin ana sana'anta su ne a kamfani, kuma har ake cewa suna jawo cutar zuciya.

Amma har yanzu babu wata hujja takamaimiya da ke nuna hakan.

Waɗannan na'ukan man girkin suna ɗauke ne da tsakanin kashi 5 zuwa 10 na maiƙo mai illa, sannan suna ɗauke da maiƙo masu muhimmanci ga jikin ɗan'adam irin su mono da polyunsaturated fats. Maiƙon polyunsaturated ciki har omega-3 da omega-6 suna da muhimmanci wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwa da zuciya.

Forouhi ta ce waɗannan na'ukan man girkin suna da "kyau ga lafiyarmu."

Ta ƙara da cewa suna taimakawa waje rage kamuwa da cututtuka, "saboda suna maye gurbin nau'ukan maiƙo masu illa a jikin ɗan'adam."

Haka kuma a kasuwanni, waɗannan na'ukan man girkin sun fi sauƙi, don haka suke da sauƙin sha'ani.

2. Man margarine na rage maiƙo mai illa

Man margarine na yanzu ba su da sinadaran maiƙo masu illa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Man margarine na yanzu ba su da sinadaran maiƙo masu illa

Man margarine ma an daɗe ana cewa yana ƙara yawan maiƙo kuma aka cewa mu guje shi saboda wai yana ɗauke da maiƙo mai cutarwa da ake tunanin yana jawo cutar zuciya.

Amma nau'kan man na yanzu ba sa ɗauke da maiƙo mai cutarwa, don haka babu laifi a haɗa su a cikin cimakan yau da kullum, kuma suna rage yawan maiƙo mai illa daga jiki.

"Idan kana son amfani da butter, ka riƙa amfani da abinka, ba ka matsala," Forouhi.

Za ka iya amfani da man butter wajen girki, amma Forouhi ta ce ba kowane lokaci.

3. A guji amfani da man olive wajen suya

Man sunflower ko na vegetable za su fi kyau wajen suya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Man sunflower ko na vegetable za su fi kyau wajen suya

Kowane man girki yana da yadda yake yi idan ya ji tsananin zafin wuta, shi ya sa yake da kyau a guji amfani da wasu na'ukan wajen suya.

Tiriri na nuna cewa maiƙon da ke cikin man girkin ya fara fashewa, sai su fara fitar da wasu irin sinadarai waɗanda suke sakawa man ya fara tsami ko ya ƙone.

Mai wajen sayar da abinci Tim Hayward ya ce idan suya kaɗan zai yi, ya fi yin amfani da man girki da aka fi sabawa da su.

Amma idan suya ne da yake buƙatar wuta sosai kamar suya dankalin turawa ko kifi, ya fi amfani da man girkin vegetable ko na sunflower saboda suna iya jure zafin wuta sosai.

Wasu masu bincike sun bayyana cewa wasu nau'ukan man girkin idan uka ji wuta sosai, suna fitar da wasu sinadarai masu illa ga lafiya.

Wane irin man girki ya kamata a yi amfani da shi?

Idan kana so ka tsara yanayin amfani da man girkinka cikin sauƙi, ga shawara:

  • A girkin yau da kullum: Ma sunflower ko na rapeseed sun fi sauƙi da inganta lafiya kuma ana iya kowane irin girki.
  • Haɗa salads: Nau'in virgin olive oil na ƙara ɗanɗano kuma yana inganta lafiya.
  • Suya da zai daɗe a wuta: Man girki da suke jure tsananin zafin wuta kamar man vegetable ko na sunflower
  • Domin ƙarin ɗanɗano: Ku yi amfani da nau'in sesame ko avocado man kwankwa.

Farfesa Forouhi ta ce yana da kyau a lura da yanayin dahuwar, sama da lura da irin man girkin.