Mene ne aikin Sarki a Masarautar Birtaniya?

Sarki Charles na uku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Charles

Me zai faru yanzu?

Sarki Charles na III ya gaji mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta II, bayan rasuwarta a fadar Balmoral tana da shekara 96.

A farkon shekarar da muke ciki, Sarauniyar ta yi bikin cika shekara 70 a kan karagar mulki abin da ya sa ta zama Sarauniyar da ta fi daɗewa a kan karagar mulkin Birtaniya.

Bayan Sarauniyar ta mutu, nan take sarauta ta koma kan ɗanta wanda shi ne magajinta wato tsohon Yariman Wales.

A ranar Asabar aka naɗa Charles a matsayin sarkin Birtaniya a hukumance a fadar St James da ke birnin Landan a wani biki da aka yi.

Ayyukan da Sarkin zai gudanar

Sarki shi ne shugaban ƙasa na Birtaniya, sai dai ikonsa ba ya tasiri kuma zai kasance ba ya goyon bayan wani ɓangare a harkokin siyasa.

Zai riƙa karɓar saƙonni a kowace rana daga gwamnati a cikin wani jan akwati gabanin tarurruka masu muhimanci ko takardun da ke buƙatar sa hannunsa.

Haka kuma a kowace Laraba Firaiminista yake ganawa da Sarki a fadar Buckingham domin ya yi masa bayani a kan al’amuran gwamnati.

Waɗannan tarurruka duk na sirri ne kuma babu wani bayani a hukumance game da abin da aka faɗa.

Haka kuma Sarki na taka muhimmiyar rawa a ɓangaren Majalisar Dokokin ƙasar.

Sarki Charles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Charles da mahaifiyarsa

Bugu da ƙari, Sarkin zai karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashe duniya masu ziyara tare da ganawa da jakadun ƙasashen waje da ke zaune a Birtaniya.

Shi ne zai jagoranci taron tunawa da mazan jiya da ake yi a watan Nuwamba ta kowace shekara a birnin Landan.

Sabon Sarkin shi ne shugaban ƙungiyar Commonwealth wadda ƙungiya ce mai mambobi kasashe 56 da kuma mazauna biliyan 2.4.

Sai dai tun bayan lokacin da Barbados ta zama Jamhuriya a 2021 an samu wasu ƙasashen Caribbean da ke cikin ƙungiyar da sun nuna alamun su ma za su bi sahun ƙasar ta Barbados.

Hoton Sarki Charles na uku zai maye gurbin na mahaifiyarsa a kan sabon tambari na Royal Mail da kuma takardun kudi kuma za a sabunta kalmomin da ke cikin sabon fasfo ɗin ƙasar ya koma mai martaba.

Taken ƙasar zai koma “Allah ya ja zamanin sarki”

Shin ya tsarin gadon Sarauta yake?

Tsarin gadon sarauta ya bayyana wanda zai karɓi sarauta daga iyalin gidan sarauta bayan wanda ke kan mulki ya mutu ko ya sauka daga sarautar ƙasar.

Na farko a layi - magajin sarauta - shi ne babban ɗan sarki. A matsayin ɗan fari na Sarauniya Elizabeth, Charles ya zama sarki a lokacin mutuwar mahaifiyarsa kuma matarsa ta koma Sarauniya da ake kira Queen Consort.

Dokokin gadon sarauta da aka yi wa kwaskwarima a 2013 sun sa ba za a ba ƴaƴa maza fifiko fiye da yayyensu mata ba.

Magajin Charles shi ne babban ɗansa, Yarima William wanda ya gaji sarautar mahaifinsa na Duke na Cornwall.

Sai dai ba a nan take zai zama Yariman Wales ba - wannan wani muƙami ne da sarkin ne kawai zai ba shi.

Babban ɗan Yarima William, Yarima George shi ne na biyu a matsayin magajin sarauta sannan babbar ƴarsa Gimbiya Charlotte ita ce ta uku. 

Gidan sarautar Birtaniya
Bayanan hoto, Gidan sarautar Birtaniya
Gidan sarautar Ingila
Bayanan hoto, Gidan sarautar Ingila

Me ke faruwa a naɗin Sarauta?

A bikin naɗin sarauta ne ake naɗa sarki a hukumance. Ana gudanar da shi ne bayan wani lokaci na zaman makoki na sarkin da ya gabata.

Elizabeth ta biyu ta zama Sarauniya a ranar 6 ga watan Fabrairu 1952 bayan mutuwar mahaifinta Sarki George na shida amma ba a naɗa ta ba sai a ranar 2 ga watan Yuni 1953.

Naɗin sarautarta shi ne na farko da aka yaɗa kai-tsaye ta talibijin kuma mutum sama da miliyan 20 ne suka kalli bikin.

Sauraniya Elizabeth

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth ita ce shugaba ta 39 da aka naɗa a Westmintser Abbey

A cikin shekaru 900 da suka gabata a Westminster Abbey ne aka riƙa gudanar da naɗin sarauta-William the Conqueror shi ne sarki na farko da aka naɗa a wannan wuri kuma Charles shi ne na 40.

Biki ne da ke gudana a cocin Ingila na Anglican karkashin jagorancin babban limamin cocin wato Archbishop of Canterbury.

Ana shafe sarki fa “mai tsarki” kuma yana karɓar sandar sarauta. Babban limamin cocin Ingila zai sanya masa kambun St Edward a kai da aka yi da zinari tun 1661.

Ba kamar bukukuwan aure na sarauta ba, naɗin sarautar wata al'ada ce ta jiha, Gwamnati ce take ɗaukar nauyinsa kuma ita ce take yanke shawara a kan waɗanda za su halarci bikin.

Su wane ne kuma ke cikin gidan sarauta?

Sarauniya Elizabeth da iyalinta

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth da iyalinta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duke na Cornwall da Cambridge (Yarima William) shi ne babban dan Sarki Charles da matarsa ta farko Diana gimbiyar Wales.

Yana auren Duchess ta Cornwall da Cambridge (Catherine) Suna da ƴaƴa uku: Yarima George da Gimbiya Charlotte da Yarima Louis.

Gimbiya Anne ita ce ƴa ta biyu da Sarauniyar ta haifa. Ta auri Vice Adm Timothy Laurence. Tana da yara biyu da mijinta na farko Kyafin Mark Philips: Peter Philips da Zara Tindall.

Earl na Wessex ( Yarima Edward) shi ne autan Sarauniya. Yana auren Countess ta Wessex (Sophie Rhys Jones) Suna da yara biyu: Loiuse da James Mountbatten-Windsor

Duke na York (Yarima Andrew) shi ne ɗan sauraniya na biyu. Yana da yara mata biyu da tsohuwar matarsa, Duchess ta York ( Sarah Ferguson): Gimbiya Beatrice da gimbiya Eugenie.

Sai dai Yarima Andrew ya ajiye mukaminsa na yi wa jama a hidima sakamakon hirar da ya yi da Newsnight a 2019 kan zargin ya ci zarafin wata mata ta hanyar lalata.

A 2022 ya biya kuɗin da ba a bayyana adadinsu ba a matsyin diyya ga Virginia Giufrre wadda ta kai ƙara kotu a Amurka.

Duke na Sussex (Yarima Harry) shi ne ƙanin William. Yana auren Duchess ta Sussex (Meghan Markle). Suna da yara biyu: Archie da Lilibet.

A 2020 sun sanar cewa za su ajiye muƙamansu a matsayin manyan masu sarauta kuma za su koma Amurka da zama.

A ina ‘yan gidan sarauta suke zama?

Ana sa ran Sarki Charles da Sarauniya Camilla za su koma Fadar Buckinham da zama. A baya suna zaune ne a Clarence House da ke Landan.

Yarima William da Catherine Duchess ta Cornwall da Cambridge a baya-bayan nan sun koma West London daga Kensington domin su zauna a Adelaide Cottage da ke Windsor Estate.

Yarima Harry da Meghan Markle na zama a California.

Yarima William da iyalinsa

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Yarima William da iyalinsa

Shin ko har yanzu ‘ yan gidan sarauta suna da farin jini?

Kuri’ar jin ra’ayoyin jama'a da aka gudanar a lokacin da aka yi bikin cikar Sarauniya shekara70 kan karagar mulki ta nuna cewa kashi 62 cikin 100 na mutane na ganin ya kamata masauratar ta ci gaba da mulkin ƙasar.

Kashi 22 ke cewa ya kamata a samu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a maimakon haka.