Ƙabilar da tsofaffi ke da nagarta fiye da wasu matasan yanzu

Tsimane woman with dark hair pinned up, wearing a white top with black flowers and a necklace

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Martina na ɗaya daga cikin 'yan ƙabilar Tsimanes 16,000 da ke zaune a dajin Amazon.
    • Marubuci, Alejandro Millán Valencia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
    • Aiko rahoto daga, Bolivia
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da Martina Canchi Nate ke tafiya ckin dajin Bolivia, wasu ƙwari na kewaye da ita, mun buƙaci da tsaya domin tattaunawa da tawagarmu.

Katin shaidarta ya nuna shekarunta 84, amma cikin mituna 10, ta iya tona itacen rogo uku domin amfani da su, sannan ta yi amfani da sharɓeɓiyar addar da ke hannunta ta sari bishiyar agada (plantain).

Ta kuma kuma cicciɓi damin agada ta kuma saɓa a bayanta, sannan ta nufi gida daga gonar tata inda take noma rogo da dawa da agada da kuma shinkafa.

Martina na ɗaya daga cikin 'yan kabilar Tsimanes 16,000 (da ake furtawa da “chee-may-nay"), wata ƙaramar ƙabila ta marasa matsuguni da ke zaune a tsakiyar dajin Amazon, mai nisan kilominta 600 daga arewacin La Paz, babban birnin Bolivia.

Ƙarfin da ta nuna ba baƙon abu ba ne a wajen 'yan ƙabilar Tsimanes duba da shekarunta.

Masana kimiyya sun bayyana cewa 'yan ƙabilar sun ƙasance mafiya lafiyar manyan jijiyoyin da ke ɗaukar jini daga zuciya da aka taɓa gani a fannin nazari, kuma ƙwaƙwalwarsu ba ta saurin tsufa saɓanin na sauran mutanen da ke yankin arewacin Amurka da Turai da kuma sauran wurare.

'Ƴan ƙabilar Tsimanes ba su yawa a duniya. Sun kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka dogara da farauta da noma don ciyar da kansu.

Juan wearing a blue T-shirt, holding a bow
Bayanan hoto, Juan kan tafi farauta, inda yakan kwashe kwana guda zuwa biyu a daji.

'Yan ƙabilar Tsimanes na da ƙarfin, gudanar da farauta da noman abinci da kuma saƙa abubuwan rufin gidajensu.

Ƙasa da kashi 10 na ayyukansu ne kawai suke yi a zaune, saɓanin kashi 54 na sauran ayyukansu. Matsakaicin lokacin da suke ɗauka suna farautar shi ne na sa'a takwas, inda suka shafe aƙalla kilomita 18.

Suna zaune a tekun Maniqui, aƙalla tafiyar kilomita 100 a jirgin ruwa daga garin da ke kusa da kogin, kuma ba koyaushe suke iya samun abincin da aka sarrafa ko barasa ko sigari ba.

Masu bincike sun gano cewa kashi 14 ne kawai na sinadaran ƙara kuzari (calories) sukan same shi daga abinci mai kitse, saɓanin kashi 34 da ake samu a Amurka.

Abincin da suke ci cike yake da sinadarin fibre, kuma kashi 72 na sinadaran ƙara kuzari suna samunsa ne daga abincin mai ƙara kuzari, saɓanin kashi 52 a Amurka.

Abincinsu mai gina jiki suna samunsa daga dabbobin da suek farauta, kamar tsuntsaye da birrai da kifaye.

A fannin girki kuwa sukan yi amfani da hanyar gargajiya, kamar gashi, amma babu batun suya.

Meat cooking over an open fire

Asalin hoton, Michael Guvern

Bayanan hoto, 'Yan ƙabilar Tsimanes kan samu abinci mai gina jiki daga dabbobin da suke farauta.

Binciken da Farfesa Kaplan da abokin aikinsa, Michael Gurven na jami'ar California, ya gano cewa tsofaffin 'yan ƙabilar Tsimanes ba su nuna alamun cutakan da mafi yawan tsofaffi ke ɗauke da su kamar hawan jini da ciwon siga da matsalar zuciya.

Hakan ya janyo hankalin wasu masu bincike waɗanda suka faɗaɗa bincike a kan wannan ƙabila da sauran ƙabilu masu kamanceceniya da ita.

Yayin da shekarun mutane ke ƙara yawa sinadarin cholesterol da sauransu sinadarai kan sa manyan jijiyoyin jininsu su kumbura tare da haifar musu da matsaloli, amma su 'yan ƙabilar Tsimanes ba haka batun yake ba.

A man walks barefoot across a plank
Bayanan hoto, 'Yan ƙabilar Tsimanes kan yi matsakaicin taku 16,000 zuwa 17,000 a ranafiye da taku 10,000 da ake yi a wasu manyan ƙasashe.

Kamar yadda Farfesa Kaplan ya bayyana: “lafiyar manyan jijiyoyin jinin ɗan ƙabilar Tsimane mai shekara 75 dai dai yake da na mai shekara 50 a Amurka''.

Wani sashe na binciken da aka wallafa a shekarar 2023 a mujallar 'National Academy of Science' ya nuna cewa ƙwaƙwalwar tsofaffin 'yan ƙabilar Tsimanes ba ta da rauni idan aka ƙwatanta da na sauran mutanen da ke da makamantan shekarunsu a manyan ƙasashe irin su Birtaniya da Japan da kuma Amurka

Sanin haƙiƙanin shekarun 'yan ƙabilar Tsimanes abu ne mai wahala, saboda su kansu ba su da ilimin, ballantana ma su iya lissafa shekarunsu.

Sun bayyana mana cewa suna amfani da karatun da kiristocin mishan suka koya wa iyaye da kakanninsu shekaru masu yawa da suka shuɗe.

Masu bincike na lissafa shekarun 'yan ƙabilar ta hanyar la'akari da yawan yaran da suke da su.

Hilda and Pablo sitting on a bench outside their home
Bayanan hoto, Hilda na zaune da mijinta, Pablo wanda ta aura bayan rabuwar ta mijinta na farko

Masu binciken sun ce shekarun Hilda 81, amma ita ta ce a baya-bayan nan 'yan uwanta suka yanka alade domin taya ta murnar cika shekara 100 a duniya.

Shi kuwa Juan mai shekara 78, ya fita da mu domin farauta. Gashinsa baƙi kuma idansu a tsaye suke, kamar yadda damatsantsa suke da ƙarfi.

Mun ga yadda ya tashi wata ƙaramar dabba, inda suka riƙa gumurmuzu da ita a cikin dokar daji suka kulli kurciya da juna.

Ya ce tsufa ba ya hana shi farauta, halaisa idan bai yi ba baya jin daɗin jikinsa.

“In dai ban fita ba, bama na jin daɗin jikina. A yanzu haka na da na yi kwana biyu ban fita bana jin daɗin jikina.”

Juan in a blue T-shirt, aiming a gun
Bayanan hoto, Juan na farauta da bindiga da kwari da baka

Martina ta ce mata 'yan ƙabilar Tsimane kan yi sana'ar saƙa abin rufin ɗakuna, da suka bishiyoyi a dokar daji, Martina kan yi tafiyar sa'a uku domin zuwa gonarta sannan ta y wasu sa'ao'in uku domin komawa gidanta, ɗauke da damman plantain a bayansu.

Sannu a hankali rayuwa 'yan ƙabilar na sauyawa.

Juan ya ce a wannan wata bai samu damar farautar dabbobi masu yawa ba kamar yadda ya saba yi a baya.

CT scanner with a group of people standing next to it
Bayanan hoto, Shekara shida da suka shuɗe kusan 'yan ƙabilar 1,500 aka yi wa gwaji a asibiti.

Yawan gobarar daji da aka samu a ƙarshen shekarar 2023 ya lalata kusan hecta miliyan biyu na dajin da suke ciki.

"Gobarar ta sa dabbobi masu yawa sun fice daga dajin,” in ji shi.

A yanzu ya fara kiwon dabbobin, kuma ya nuna mana huɗu daga cikinsu da yake fatan za su samar wa iyalansu abincin mai gina jikin da suek buƙata.

Dakta Eid ya ce ta hanyar mafani da ƙananan jiragen ruwa da kwale-kwale a yanzu 'yan ƙabilar sun fara samun sauyi, inda suke samun sauƙin zuwa kasuwanni , domin sayen nau'ikan abinci, kamar na sukari da fulawa da kuma mai.

Boat on the river Maniqui, laden with people and plantains
Bayanan hoto, Fara amfani da ƙananan jirage kan taimaka wa 'yan ƙabilar wajen gudanar da harkokinsu.

Shekara 20 da suka wuce ba a cika samun cutakan ciwon suga ba a yankin, amma a yanzu irin waɗannan cutukan sun fara bayyana a yankin, kuma sinadarin cholesterol na ƙaruwa a jikin matasan 'yan ƙabilar, kamar yadda binciken ya gano.

“Idan aka samu sauyi ko ya yake a abincinsu, hakan ka iya shafar lafiyar jikinsu,” in ji Dakta Eid.

Masu binciken kansu sun fuskanci abubuwa da dama a tsawon shekara 20 da suka ɗauka suna binciken, ta hanyar nazartar tsarin lafiyar 'yan ƙabilar Tsimanes kama daga basu magunguna da tiyata koma ɗora musu karaya da magance musu saran macizai.

Amma ga Hilda, tsufa ba abu ne da zai ɗaɗata da ƙasa ba. “Bana tsoron mutuwa,” ta bayyana a lokacin da take murmushi, “Saboda binneni kawai za su yi, kuma a nan ne zan tabbata”.