Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko raba shimfiɗa tsakanin ma'aurata na da alfanu?
Raba shimfiɗa tsakanin ma'aurata abu ne da aka saba, musamman a lokacin da ɗaya daga ciki baya nan, ko ba shi da lafiya.
Wani bincike ya nuna cewa raba shimfiɗa ko ma kwana a ɗakuna daban-daban tsakanin ma'aurata na da alfanu kan lafiyar ƙwaƙwalwa da lafiya.
Kamar yadda aka wallafa a mujallar 'relationshipsnsw.org.au.' ga wasu alfanu biyar na raba shimfiɗa tsakanin ma'aurata.
Samun wadataccen barci
Binciken ya gano cewa raba shimfiɗa tsakanin ma'aurata zai inganta barcinsu.
Za ku samu ingantaccen barci cikin nutsuwa idan babu abin da ke damunka daga barcin abokin kwanciyarka, kamar mishari.
Wannan abu ne mai kyau, domin rashin samun barci cikin nutsuwa kan haifar da illa ga lafiyar mutum.
Rashin wadataccen barci na haifar wa mutune jinyace-jinyace, kamar matsalar ƙarin ƙiba da cutar ciwon Suga da cutukan zuciya, kamar yadda makarantar aikin lafiya ta Havard ta bayana.
Rage jayayya tsakanin ma'aurata
Raba shimfiɗa tsakanin ma'auraa ko ma kwana a daukan daban-daban zai rage yawan jayayya tsakanin ma'auratan tare da hana juna barci.
Rage damuwa kan saduwa
Ga wasu ma'auratan, saduwa kafin barci ya zame musu jiki.
Amma idan kana cikin gajiya, kuma ba ka cikin yanayin da za ka iya yin magana ga ɗan’uwanka ba, za ka ji takaicin kin amincewa da shi.
To amma idan ma'aurata suna raba shimfiɗa, buƙatar saduwa kan ɓace, kamar yadda Overstreet, masanin al'amuran iyalai ya bayyana.
Mutanen da ke son kwanciya su kaɗai
Za ka iya yin haka, ta hanyar kwanciya a shimfiɗa daban-daban, kana buƙatar ƙarin ɗaki domin yin barci kamar yadda kake so.
Wasu mutanen na son yin barci su kaɗai a shimfiɗa, don haka idan suna tare da wani ba sa samun yadda suke so, saboda suna buƙatar samun isasshen filin da za su wataya a kan shimfiɗa.
Hakan zai sa ku samu wadataccen filin da za ku wataya a kan shimfiɗunku.
Tashi da wuri don tunkarar abin da ke gabanku
Suna iya buƙatar tashi da sassafe domin tafiya wuraren ayyukansu, bayan kuwa ba su samu barci da wuri ba.
Watakila dalilin da ya sa ma'aurata ke son raba shimfiɗa shi ne yanayin ayyukansu sun bambanta, watakila wani na da aikin safe wani kuma sai da rana , kwanciya shimfida ɗaya zai sa mai aikin rana ya hana mai aikin safe yin barci da wuri.
To idan mutum ya kwanta a shimfiɗa ko daki daban, zai kauce wa wannan matsalar.
To amma kafin ma'aurata su raba shimfiɗa ko ɗakunan kwana, yana da kyau su lura da waɗannan abubuwa.
1: Idan kwanciya taren na shafar barcin ɗaya daga cikin ma'auratan.
2: Idan kuna yawan faɗa ko jayayya.
3: Idan ɗaya yana cutuwa da minsharin ɗayan.
4: Idan hakan zai iya shafar dangantakarku.