Kuskure biyar da ma'aurata suke yi game da kudi da yadda za a fahimci juna

Tattaunawa a bayyane kan al'amurran kuɗi lamari ne da ya shafi mutane da yawa, kuma su ma ma'aurata ba a bar su a baya ba game da magana kan kuɗi.

Idan aka duba tarihinmu, matsalolin kuɗinmu da ɗabi'unmu da alaƙarmu da kuɗi, na iya haifar da abubuwa daban-daban ga mutane daban-daban, abin da ya zama mai wahalar tattaunawa.

Tattalin arziki na mutum abu ne mai wuyar sha'ani - wani lokacin abin kunya ne a tattauna shi da abokan zama ko dangi, kuma wani lokacin abu ne mai sauƙi a yi watsi da shi gaba ɗaya ba sai an tattauna shi ba ma.

Yana da muhimmanci mu tattauna yadda muke sarrafa kuɗi da wuri da abokan zamanmu don kar hakan ya haifar da rigima a nan gaba. Sai dai, idan ba ku samu damar tattaunawa ba har yanzu, kuna da damar yin hakan.

Wani bincike da aka yi kwanan nan don fahimtar wasu abubuwa da ke haifar da saɓani tsakanin ma'aurata, mun gano rashin fahimta biyar da ma'aurata ke yi game da kuɗi da kuma hanyoyin da za su magance su.

1. Rashin daukar lokaci don tattauna batutuwan kuɗi a aure ko soyayya

Mukan ɓata lokaci mai yawa wajen yin muhimman abubuwa a rayuwarmu, kamar zuwa ganin likita ko likitan haƙori don duba lafiya, haka ma ya kamata mu yi da kuɗinmu.

Magana game da kuɗi na iya zama abu mai wahala, amma kuma yana da mahimmanci don samun nasara a zaman aure.

Ku tsara lokacin da ya fi dacewa kai da matarka; kar ku jira har sai wani ya kashe kuɗi mai yawa don sayen wani abu, ko lokacin da wasu lamuran kuɗi suka taso.

Abin da aka fi so shi ne ku tattauna harkokin kuɗinku cikin nutsuwa kafin a samu wata matsalar kuɗi.

Abin da kuke tattaunawa a irin wannan lokacin ya rage gare ku; yana iya kasancewa game da kashe kuɗi, biyan kuɗi, yadda kasafin kuɗinku ke gudana, ko tanadin kuɗi don wani abu mai mahimmanci.

Abu mai mahimmanci dai shi ne, ware lokaci don magana a kan kuɗi.

2. Rashin sanin tsarin abokan zamanku kan kuɗi

Yadda ake kashe kuɗi a baya zai iya shafar yadda muke kashewa a yanzu, wanda shi ne dalilin da ya sa yake da mahimmanci ku fahimci tsarin harkokin kuɗin abokan zamanku.

Tarihin yadda muke kashe kuɗinmu zai iya bayyana dalilin da ya sa muke kashe kuɗin.

Idan mijinki ya taso ne a gidan da wadatar kuɗi ke da wahala, za ki iya gane hakan ta hanyar:

Hakan na nufin za ki yi mamakin dalilin da ya sa ba ya kashe kuɗi ko kuma ba ya son zuwa otal don ya ci abinci - saboda ya girma ne a yanayi na yin taka-tsantsa da ƙididdige kuɗi don tabbatar da cewa bai faɗa cikin yanayi na rashi ba.

A gefe guda kuma, idan kin taso a inda kuɗi bai taɓa zama matsala ba, ƙila za ki ji haushin yadda yake adana kuɗi da kuma ƙin kashe su.

Fahimtar hakan daga abokan zamanku abu ne mai kyau kuma mai mahimmanci don sanin yadda za ku zauna lafiya a matsayin ma'aurata ba tare da wata rigima ba.

3. Yin watsi da kafa manufofi iri ɗaya kan Kuɗi

Da zarar kun fahimci tarihin kashe kuɗin abokin zamanku, za ku fahimci manufofinsu game da yadda suke kashe kuɗi. Kuma samun wannan fahimtar za ta taimaka muku wajen kauce wa faɗawa kan kuɗi.

Yayin kafa manufofinku kan kuɗi, yana da mahimmanci kai da matarka ku fayyace abin da kowannenku yake so.

Yawancin ma'aurata suna ɗauka cewa abokin zamansu ya yarda da ra'ayinsu kan kuɗi, amma wannan ba gaskiya ba ne.

Sanannen abu ne a samu mabambantan manufofi kan kuɗi; maƙasudi dai shi ne mu bayyana wa juna manufofinmu da nemo hanyoyin cimma manufofin tare.

Don haka ku rubuta kuma ku tsara kowane burinku na kuɗi, sannan ku bayyana wa juna manufofin naku.

Da zarar kun san abin da ke da mahimmanci ga junanku, wato saita ingantattun manufofi na ɗan gajeren lokaci da masu mahimmanci ga kowannenku.

Yarjejeniya kan manufofin juna zai sa wani daga cikinku ya rasa wasu manufofi na kashin kansa, amma mataki ne da zai jawo alheri a nan gaba.

Samun manufofi da za su magance matsalolinku duka, za su taimaka wajen kasancewarku a shafi ɗaya game da inda kuɗinku ke tafiya, kuma hakan zai ƙara muku azama wajen yin aiki tare.

4. Aiwatar da kasafin kudin da bai dace da kowannenku ba

Dukkanku kuna buƙatar sanin abin da kuke samu, kuma hanya mafi kyau don yin hakan ita ce tattauna muradai da kuma yin kasafin kuɗi.

Lokacin ƙirƙirar kasafin kuɗi, yana da mahimmanci ku ɗauki juna a matsayin abokan harka daidai-wadaida da kuma tsayawa kan tsari ɗaya na sarrafa kuɗi.

Idan albashin ɗaya daga cikinu ya zarta na ɗayan, hakan ba ya nufin yana da iko a kan kuɗi fiye da ɗayan.

Zaunawa tare a matsayin ma'aurata ku duba abin da kowannenku ke bi da abin da kowannenku ya mallaka da kuma kuɗin da kowannenku ke karɓa a matsayin albashi.

Abu na gaba, ku kasafta kuɗin da ya zama dole sai an kashe kamar haraji da biyan bashin mota da inshora.

Saboda waɗannan kuɗaɗe wajibi ne a kashe su, yana da sauƙi a fara yin kasafi a kansu.

5. Rashin ƙyale kowa ya tanadi 'kuɗinsa'

Bai wa abokin zama wani adadin ''kuɗi '' na iya yin tasiri na ban mamaki wajen rage yawan faɗa a kan kuɗi.

Rigima na iya ɓarkewa sau da yawa saboda yawan kuɗin da ɗaya daga cikinku ke kashewa daga asusun haɗaka. Don haka yana da kyau a bai wa kowa tsarin yadda za a kashe kuɗin don ya san halin da yake ciki.

Kun yi aiki tuƙuru don samun kuɗinku, don haka kar ku taɓa jin cewa kuna buƙatar izini kafin ku sayi wani ƙaramin abu ko kuma saboda ba ya cikin kasafin kuɗin.

Idan ka zaɓi samun katin asusunka kai kaɗai, hakan ba ya nufin dole ne ka ɓoye wa matarka bayanan abubuwan da ka yi da kuɗin.

Boye wa abokan zamanku abubuwa, kamar kuɗi ko katin ATM ko sabbin kayan sayayya, na da haɗari a cikin kowace irin soyayya kuma yana da kyau a samu sadarwa ta gaskiya da gaskiya.

Idan ba za ku iya bayyana wa junanku abubuwan da kuke saya ba saboda kuna tsammanin abokin zamanku ba zai amince ba, abu ne da ya kamata ku tattauna tare.