Libya za ta shigar da Super Eagles ƙara

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar kwallon kafa ta Libya ta yi Allah wadai da matakin da Hukumar kwallon Kafa ta Najeriya ta ɗauka na fasa buga wasa na biyu na neman gurbibn gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Ta yi ƙorafin hukumomin Najeriya ba su nuna musu dattaku ba a wasan da suka yi a Najeriya, tare da cewa halin da 'yan waswan Najeriya suka shiga bai kai kwatankwacin wanda 'yan wasanta suka shiga ba a Najeriyar a makon jiya.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ɗau alwashin shigar da ƙarar Super Eagles kan matakin da ta ɗauka na komawa ƙasarta da fasa buga wasan.

Ta ce Najeriya ta ja ta sabawa magoya bayanta da suka shirya ganin wasan da aka tsara yi a yau, hakan ya sa ta baiwa magoya bayan Libya hakuri cikin sanarwar.

Sai dai hukumomin Najeriya sun musanta duka zarge-zargen da humumar kwallon ƙafa ta Libya ta yi.

Tace ita aka hana duk wata dama da 'yaci da take da shi kama daga yanci fita su kama otel da na yawo da na cin abinci.

A daren jiya hukumar kwallon kafa ta Libya ta wallafa hotunan 'yan wasanta a filin atisaye, tana cewa hakan wani ɓangare ne na shirin tunkarar wasan Najeriya a yau Talata.

Yayin da ita kuma tawagar Super Eagles ta koma Najeriya, bayan yanke hukuncin da ta yi na fasa buga wasan.

A gefe ɗaya kuma tuni Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa ta samu bayanai kan abin da yake faruwa tsakanin hukumomin kwallon kafa na Najeria da Libya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin ƙasashen nahiyar ta 2025.

CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin kwallon kafar ƙasashen Najeriya da na Libya domin jin abin da yake faruwa game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin sama da ke Libya awanni masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.

A yanzu dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika ta gabatar da wannan matsala ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗaukar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.