Yadda ya kamata ɗalibai su rinƙa amfani da fasahar AI a ayyukansu

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A 'yan shekarun nan, fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI ta zama abin da ke jan hankali a fannoni da dama da suka haɗa da ilimi da likitanci da kasuwanci da nishaɗi da dai sauransu.

A da, tsarin karatu ya ta'allaka ne da karatun littattafai da zuwa ɗakin karatu da rubuta bayanai da hannu, inda ɗalibai ke dogaro da malamai da takardu kawai don samun ilimi.

Amma yanzu, zuwan fasahar zamani ya kawo babban sauyi daga yadda aka Saba karatun a da, zuwa karatun zamanin yanzu ta intanet da kwamfuta, da kuma AI, wanda ke ba da damar samun bayanai cikin sauri da sauƙi.

Yawancin ɗalibai a Najeriya da ma duniya suna amfani da AI wajen karatu da rubuta ayyukan gwaji na makaranta, da kuma gudanar da bincike. Wannan ya nuna yadda fasaha ta sauya salon neman ilimi gaba ɗaya.

Amma tambayar ita ce; ta yaya ya kamata dalibai su rinƙa amfani da AI a ayyukansu ta hanyar da ta dace?

Domin samun amsa kan wannan tambayar ne BBC ta tuntuɓi Abdullahi Musa, ƙwararre a ɓangaren basirar AI inda ya bayyana cewa AI tana da amfani sosai, amma idan ɗalibai ba su koyi yadda ake amfani da ita yadda ya dac ba, za ta iya lalata tsarin karatunsu.

"Idan ɗalibai suka dogara kacokan a kan fasahar AI wajen yin komai na karatu, to za su cutar da kansu ne kawai," in ji Abdullahi.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar makarantu su fara horar da ɗalibai kan yadda ake amfani da AI yadda ya kamata.

Ya kuma ba da shawarwari kan yadda ɗalibai za su yi amfani da basirar AI kamar haka;

  • Kada ɗalibai su dogara da AI gaba ɗaya wajen aikin karatunsu: Ku yi amfani da AI domin samun ra'ayi da fahimta.
  • Ku tabbatar kuna tantance gaskiyar bayanan da AI ta bayar kafin amfani da su.
  • Kada ku yi amfani da AI wajen rubuta cikakken aikin karatu ba tare da kun fahimci abin da ke ciki ba.
  • Ku koyi yadda ake tambayar AI cikin hikima domin samun amsar da ta dace.
  • Ku tuna cewa AI tana taimaka muku wajen sauƙaƙa muku fahimtar abu, amma ku ne ke da alhakin fahimta.
  • Kada ku kwafe amsar AI kai tsaye: Idan AI ta ba da amsa, ku sake rubutawa da gyarawa, da kuma ƙara ra'ayinku.
  • Ku yi amfani da fasahar AI don horar da kanku, ba wai ku maye gurbin malamai ba
  • Ku kula da sirrinku: Kada ku saka bayanan sirrinku ko na makaranta cikin manhajojin AI ba tare da izini ba.
  • Ku kasance mai koyon sabbin dabarun AI: Fasaha tana canzawa koyaushe, saboda haka ku kasance mai sabunta iliminku akai-akai.

Koken malamai

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malaman jami'a da makarantun sakandare da firamare sun bayyana damuwa kan yadda ɗalibai ke ta dogaro da ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen karatu da rubuce-rubuce.

Wannan na zuwa ne yayin wani taron ƙasashe da cibiyar bunƙasa karatu da bincike ta Najeriya da ke Jami'ar Bayero Kano ta shirya.

Ga wasu muhimman damuwar da malamai suka bayyana a taron:

  • Ɗalibai sun dagora sosai kan AI wajen yin ayyukansu na karatu

Daraktar cibiyar, Farfesa Amina Adamu, ta ce yawancin ɗalibai yanzu suna ɗebo bayanai ne daga AI su miƙa a matsayin nasu aikin.

"Suna tunanin malamai ba za su gane ba, amma da zarar ka karanta, sai ka gane ba fasaharsu ba ce," in ji ta.

  • AI na neman maye gurbin basirar ɗan Adam

Ta ƙara da cewa ya kamata ɗalibai su haɗa amfani da AI da tunaninsu, maimakon su dogara gaba ɗaya da ita.

  • Canjin tsarin karatu da koyarwa

Shugabar cibiyar horas da malamai ta NTI, Farfesa Sadiya Sani Daura, ta ce tsarin karatu ya canza sosai.

"A da gwamnati da malamai na mai da hankali kan ingancin koyarwa, amma yanzu abubuwa sun koma kan amfani da fasaha," in ji ta.

  • Ƙirƙirarriyar basirar AI na rage ƙoƙarin ɗalibai

Shugaban Jami'ar Maiduguri, Farfesa Muhammad Aminu Bele, ya bayyana cewa AI na da fa'idodi wajen sauƙaƙe karatu, amma kuma yana rage ƙoƙarin ɗalibai.

"AI yana taimaka wa wajen fahimta, amma mutane na guje wa wahala suna barin komai a hannun AI," in ji shi.