Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu al'umma ke ɗari-ɗarin haihuwar ƴaƴa?
- Marubuci, Stephanie Hegarty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Population correspondent, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Haihuwa na raguwa sosai a duk faɗin duniya, fiye da yadda ma ake hasashe.
China na samun raguwar haihuwa da ba a taɓa gani ba a ƙasar.
A faɗin ƙasashen Latin Amurka, yawan alƙaluman hukuma na yaran da ake haihuwa na raguwa sama da yadda ake hasashe.
Hatta a ƙasashen Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka ma haka lamarin yake.
Abin da ke faruwa kenan kusan a yawancin ƙasashen duniya, inda wasu iyayen ma ba sa haihuwar yara ma sam-sam.
Isabel ta kafa wata kungiya ta rajin ragewa ko ma ƙin haihuwa gaba ɗaya, bayan da ta samu matsala a aurenta tun tana da shekara talatin da 'yar ɗoriya, abin da ya sa ba ta ma ƙaunar ta haifi yara.
Tana fuskantar suka da tsangwama kusan a kullum saboda wannan zabi nata ba a ƙasarta Colombia ba kaɗai inda take.
Ta ce: “Abin da ake yawan faɗi min shi ne, ‘Za ki yi nadamar hakan nan gaba a rayuwarki. Saboda idan kika tsufa wa zai kula da ke?’”
Ga Isabel, ƙin rashin 'ya'ya abu ne da ta zaɓa. To amma a wajen wasu abu ne da yake da alaƙa da wata matsala ta jikinsu amma ba zabinsu ba ne.
Ga wasu mutanen da dama kuma batu ne da yake da alaƙa da rashin hali na wadatar kuɗi da za su iya kula da 'ya'yan, kamar yadda wani bincike da aka yi a Norway a 2021, ya nuna - musamman ma a tsakanin masu ƙaramin ƙarfi.
Lokacin da Robin Hadley yake kusan shekara talatin ya zaku ya haihu. Bai je jami'a ba, amma kuma yana aiki a wata jami'a a ɗakin bincike ɓangaren ɗaukar hoto a arewacin Ingila.
Hadley ya yi aure tun yana shekara ashirin kuma shi da matarsa suna ta fafutukar ganin sun haihu, kafin auren ya gamu da matsala su rabu.
Yana fama da ɗawainiyar biyan bashin gidan da ya saya, saboda haka ba shi da halin da zai iya yin wata mu'amulla da mata da zai haihu.
Yadda abokansa da abokan aikinsa ke samun haihuwa, shi kuma ba shi da wannan dama sai abin ya kasance yana damunsa -yana ganin ya yi rashi a rayuwa.
Wannan ƙalubale da yake ciki ne ya sa ya rabuta wani littafi a kan matsalar maza ta rashin samun haihuwa.
Yayin da yake rubuta littafin ya yi karo da dukkanin abubuwan da ke da alaƙa da hana mutane haihuwa - matsalar tattalin arziƙi da lafiyar jiki da lokaci da kuma zaɓin abokiyar zama.
Daga nan ya lura cewa a yawancin littattafai da rubuce-rucen da ya karanta a kan yawan shekaru da haihuwa babu maganar maza da ba su da 'ya'ya - kuma yawanci babu ƙididdigarsu a alƙaluman ƙasashe.
Ƙaruwar rashin haihuwa a tsakanin jama'a
Akwai dalilai da dama da ke sa rashin haihuwa a tsakanin jama'a da rashin hali ko kuɗin da mutum zai kula da 'ya'ya idan ya haihu da rashin samun abokiya ko abokin auren da ya dace a lokacin da ya dace.
To amma abin da ke haifar da hakan wani abu ne daban in ji Anna Rotkirch, maaniya kan halayyar ɗan'Adam a cibiyar bincike kan yawan jama'a ta Finland.
Masaniyar ta yi bincike kan niyyar haihuwa a Turai da Finland tsawon sama da shekara 20.
Bayan Asia, Finland ƙasa ce da ta fi yawan rashin haihuwa a duniya.
To amma a shekarun 1990 da kuma farko-farkon shekarun 2000, ƙasar ta ciri tuta da samo hanyar da ta magance wannan matsala ta raguwar haihuwa, ta hanyar ɓullo da manufofi da tsare-tsare da ke gaba a duniya, na kyautata wa yara.
Ta waɗannan hanyoyi aka samu iyaye ko abokan zama suke haihuwa.
To amma kuma tun daga 2010, sai yawan haihuwa ya ragu a ƙasar da kusan kashi ɗaya bisa uku.
Farfesa Rotkirch ta ce kamar yin haure haka ma haihuwa ta kasance wani babban abin buri ga wanda ya kama hanyar rayuwar zama babba a da.
To amma yanzu wannan ya kau, inda haihuwar ta zama wani ƙalubale - inda mutum ke ganin cewa, me kuma zai yi bayan ya cimma wasu buƙatunsa.
Masaniyar ta ce mutane a dukkanin mataki suna kallon haihuwa a matsayin wani ƙarin ɗawainiya da za ta sa su kasa cimma burinsu a rayuwa.
A bincikenta ta gano cewa a Finland da wuya matar da tafi yawan dukiya ta gama rayuwarta ba tare da ta samu haihuwa ba, yayin da a ɗaya ɓangaren abu ne mawuyaci namijin da ba shi da hali sosai (talaka) ya yarda ya haifi yawan 'ya'yan da yake so.
Ta ce wannan saɓanin da kenan, inda a baya mutanen da suke talakawa suke yin aure da wuri - su bar makaranta kuma su samu aiki kuma su fara tara iyali tun suna matasa.
Matsalar kasancewa namiji
Ga maza, rashin tabbas kan hanyoyin samun kuɗi na da babban tasiri da ke iya sa su haifi 'ya'ya.
Wannan ne ya sa masana halayyar ɗan'Adam ke nuna cewa shi ya sa mata suke neman wanda yake daidai da matsayinsu ko wanda ya fi su idan za su yi aure ko zaman tarayya.
Bincike ya nuna cewa a kashi 70 cikin ɗari na ƙasashen duniya mata na zarta maza a ilimi.
Wannan ne abin da masaniyar halayyar ɗan'Adam a Jami'ar Yale, Marcia Inhorn ta danganta da yadda ake samun bambanci tsakanin mata da maza wajen zaman tarayya (mating gap).
Wannan ya sa a Turai mazan da ba su da digirin jami'a suka fi kasancewa cikin rukunin mutanen da ke kasancewa ba su da haihuwa.
Ɓoyayyun maza
Yawancin ƙasashe ba su da cikakkun alƙaluma na maza da ke haifar 'ya'ya saboda suna ɗaukar bayanan tarihin haihuwar mata ne kawai a lokacin rijistar yawan haihuwa.
Wannan na nufin mazan da ba su da 'ya'ya ba sa cikin rukunin mutanen da aka san da su.
To amma wasu ƙasashen suna ɗaukar bayanan mata da maza duka. A hakan ne binciken da ƙasar Norway ta yi ta gano cewa akwai bambanci sosai wajen haihuwar yara tsakanin maza masu arziƙi da kuma talakawa, inda aka gano cewa ana barin maza da ba su da iyaka wajen haɗa alƙaluman haihuwa.
Yawanci ana kawar da kai wajen rawar da maza ke takawa a raguwar haihuwa, in ji Vincent Straub, wanda ya yi nazari a kan lafiyar maza da haihuwar yara, a Jami'ar Oxford.
Takaicin da maza ke ji na yadda mata ke samun cigaba a rayuwa inda suke samun dukiya ko matsayi a yau da kuma nauyin da ake ganin na kan maza da ya kamata su sauke da kasancewar namiji gaba a kusan komai duka wannan ya sauya.
“Mazan da ba su da matakin ilimi babba ba sa haihuwa sosai idan aka kwatanta da gomman shekarun baya,” in ji Straub a tattaunawa da BBC.
Haka kuma matsalar shan miyagun ƙwayoyi da ke ƙaruwa a duniya wadda kuma ta fi yawa a tsakanin maza waɗanda ke cikin shekarun da za su iya haifar 'ya'ya, it ma tana taka rawa.
Straub da Hadley sun gano cewa kusan kacokan ana mayar da hankali kan mata ne kawai idan ana magana kan haihuwa.
Kuma duk wani tsari ko manufa da za a kawo ana mantawa da rabin matsalar.
Masanan na ganin dole ne idan ana magana kan wannan matsala a shigo da lafiyar maza da kuma amfanin bai wa maza damar reno.
''Namiji ɗaya ne kawai a cikin 100 a Tarayyar Turai ke dakatawa da aiki ya kula da ɗa, su kuwa mata ɗaya ce a cikin uku,'' in ji Straub.
Wannan fa duk da tarin shedar da ke nuna cewa reno yana da amfani ga lafiyar iyaye maza.
Shigo da wannan rukunina ɓoye (maza) cikin matsalar raguwar haihuwa na ɗaya daga cikin hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar.