Kyaftin ɗin West Ham Zouma na daf da komawa UAE

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin West Ham United Kurt Zouma na daf da komawa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da taka leda.
Zouma na tattaunawa da ƙungiyar Shabab Al-Ahli kuma ana sa ran za a kammala cikinsa nan da kwanaki masu zuwa.
Dan wasan mai shekara 29 na da shekara guda da ta rage masa a Hammers, kuma yana daga cikin 'yan wasan da suka fi ɗaukar kudi a ƙungiyar.
Tun daga 2021 da West Ham ta ɗauki Zouma daga Chelsea kan fan miliyan 29, ya buga mata wasanni sama da 100.
Ya buga mata wasan ƙarshe na gasar Conference Lig da ta buga da Fiorentina a 2023 wanda suka yi nasara.
An bai wa ɗan wasan riƙon kyaftin ɗin ƙungiyar ne a bara, bayan Declan Rice ya bar ƙunkiyar zuwa Arsenal.
A 2022 an yi masa hukuncin sai ya yi aikin ci gaban al'umma na awa 180 bayan an kama shi da laifin marin magensa da ya yi.
Tun bayan naɗa Julen Lopetegui a matsayin kocin ƙungiyar, West Ham ta kashe sama da fan miliyan 100 a wannan kakar.










