Na kai Sha'aban kotu saboda ana shirin ƙwace min takarar gwamna - Nasiru Koguna

Asalin hoton, Other
Ɗaya daga cikin 'yan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar ADP Nasiru Hassan Koguna ya maka Sha'aban Ibrahim Sharada a kotu, inda yake zargin yana neman ƙwace masa takara.
An shigar da ƙarar ce 'yan awanni bayan Sha'aban ya bayyana fatan cewa shi Gwamna Abdullahi Ganduje zai miƙa wa mulkin Kano a Action Democratic Party (ADP) yayin hirarsa da BBC Hausa.
Cikin ƙarar da lauyansa Farfesa Nasiru Adamu (SAN) ya shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Alhamis, Nasiru Koguna ya yi ƙorafi kan abu huɗu, ciki har da neman ta hana Sha'aban bayyana kansa a matsayin ɗan takara.
Ya nemi kotu ta hana ADP ƙwace masa takara da kuma hana INEC sauya sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙshin jam'iyyar ta ADP.
Lauyan ya ce tun farko an yi wa Koguna alƙawarin za a ba shi mataimaki ko kuma ya janye baki ɗaya daga takarar, amma sai suka ji Sha'aban a BBC yana cewa shi ne ɗan takara kafin a kammala tattaunawa.
Tun a ranar 6 ga watan Yunin 2022 aka zaɓi Koguna a matsayin ɗan takarar gwamna ta hanyar sasantawa, inda jam'iyyar ta ce ta tsayar da 'yan takara a dukkan kujeru a Kano don fafatawa a babban zaɓe na 2023.
Sai dai ɓangaren Sha'aban, wanda ya nemi tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC mai mulkin Kano amma bai samu ba, ya koma ADP ne don ya yi takarar.
Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun nemi Koguna ya janye wa Sha'aban takarar kuma har ya amince ya janye ɗin, "amma daga baya ya yi shawarar fasa janyewa ," in ji lauya Nasiru Adamu.
Koguna, wanda shi ne mataimakin shugaban ADP na ƙasa kafin zama ɗan takarar, ya nemi tikitin takarar ɗan majalisar tarayya a jam'iyyar APC a 2019, amma sai a jam'iyyar PRP ya yi takarar, wadda kuma bai yi nasara ba.
'Ba zan janye wa Sha'aban takara ba'

Asalin hoton, Nasiru Koguna
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin abubuwan da Nasiru Koguna ya faɗa wa kotu shi ne cewa ba zai janye takarar ba.
Farfesa Nasiru Adamu mai muƙamin SAN, shi ne lauyan Nasiru Koguna, kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa ƙorafin da suka shigar ya ƙunshi neman fassarar wasu sassa na dokar zaɓe da suka hana sauya sunan ɗan takara idan bai janye da kansa ba.
"Mun nemi kotu ta hana ADP ko INEC sauya shi [Koguna] a matsayin ɗan takara, sannan kuma a hana Sha'aban bayyana kansa a matsayin ɗan takarar gwamna," a cewar lauyan.
"Idan ka dunƙule abu huɗu da muke ƙorafi a kai suna nufin muna neman kotu ta hana tsayar da wani ɗan takara saɓanin Nasiru Hassan Koguna. Shi ne halastaccen ɗan takara, bai janye ba kuma yana nan da ransa.
"Sashe na 31 da 32 da 33 na Dokar Zaɓe ta 2022 sun ce idan mutum bai mutu ba kuma bai rubuta takardar janye takara ba [to shi ne ɗan takara], kuma dokar cewa ta yi dole mutum ya kai takardar hannu da hannu ga hukumar zaɓe."
Kafin shigar da ƙarar a ranar Alhamis, Koguna ya rubuta wa hukumar zaɓe ta ƙasa da ta Jihar Kano da babban sufeton 'yan sanda wasiƙa cewa yana kan takararsa kuma bai janye ba.
Na koma ADP don na yi takara - Sha'aban
Sha’aban Sharada ya ce ya sauya sheƙa zuwa ADP saboda rashin adalci da jam’iyyarsa ta APC ta yi masa da kuma irin maganganun da ɓangaren Gwamna Ganduje suka dinga yaɗawa a kan sa cewa "ba gwamna ba ɗan majalaisa".
Ya kuma yi ikirarin cewa za a kafa tarihi na jam’iyyar da aka kafa kasa da wata shida kuma ta ci zaɓe a Kano.
"Ni Gwamna Abdullahi Ganduje zai miƙa wa ragamar mulki domin kafin 1:00 na ranar zaɓe zan yi nasara," in ji shi.
Ɗan majalisar wakilan ya kuma ce al’ummar Kano ce ta bukaci ya fito ya yi takara ba wai raɗin kansa ba ne.
"Babu ruwana da jam’iyya a zaben da ke tafe domin cancanta za su bi wajan zabar mutum".












