Kafin 12 na rana zan lashe zaɓen gwamna a Kano - Sha'aban Sharada

Yayin da zaɓukan Najeriya na 2023 ke kara karatowa, masu neman takara na ta bayyana aniyarsu ta fafatawa da su a zaɓukan da ke tafe.
Kamar sauran jihohi, a Kano ma masu neman takarar kujerar gwamna na ta kara kaimi wajen jan ra’ayin magoya baya su mara musu a zaɓukan da ke tafe a cikin kasar.
Hon. Sha’aban Sharada na daga cikin wadanda ke neman tsayawa takarar kujerar gwamna a jihar Kano, ya kuma bayyana ficewa daga jam’iyarsa ta APC zuwa ADP wacce a ciki zai yi takarar gwamna na Kano.
A wata tattaunawa da BBC, ya ce ba gudu ba ja da baya kan aniyarsa ta yin takara.
‘Za a yi tarihin kafa jam’iyya kasa da wata shida da za ta zo ta ci zaɓe’

Asalin hoton, OTHER
Sha’aban Sharada ya ce ya sauya sheƙa ne saboda rashin adalci da jam’iyyarsa ta APC ta yi masa wanda kuma bai ji dadin abubuwan da suka faru ba.
Ya kuma yi ikirarin cewa da yardan Allah za a yi tarihin kafa jam’iyya kasa da wata shida, ta kuma zo ta ci zaɓen gwamna a Kano.
"Ni gwamna Abdullahi Ganduje zai miƙawa ragarmar mulki domin kafin 12 na ranar zan lashe zaɓe".
Ɗan majalisar wakilan ya kuma ce al’ummar Kano ce ta bukaci ya fito ya yi takara ba wai raɗin kansa ba ne.
"Babu ruwana da jam’iyya a zaben da ke tafe domin cancanta za su bi wajan zabar mutum".
‘Ban ci amanar shugaba Buhari ba’

Asalin hoton, OTHER
Hon Sha’aban Sharada ya ce matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar APC ba ya na nufin ya daina mu’amala da ‘yan jam’iyyar ba ne, illa ya yi hakan ne domin cika burinsa na siyasa a wata jam’iyya.
Ya ce barin jam’iyyar ba alama ba ce ta cin amanar shugaba Buhari ba, saboda a cewarsa cin amanarsa shi ne ka ki zabar ɗan takararsa na shugaban kasa.
Ɗan siyasar ya ce har gobe ba shi da wani mai gida da kuma ya ke jin maganarsa kamar shugaban kasa.
Ya kuma ce Buhari mutum ne da baya katsalanda a harkokin mutane kuma da ke ganin idan ba a yi maka adalci ba ka nemi hakkinka.
Sha'aban Ibrahim Sharada, ya sha kaye a zaɓen fitar da gwanin gwamna a hannun mataimakin gwamna mai-ci, Nasir Yusuf Gawuna.











