Abubuwan da suka haifar da rikicin Sudan ta Kudu da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

Sojojin Sudan ta Kudu.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasar ba ta samu wani zaman lafiya na a zo a gani ba cikin shekaru 14 da suka gabata
    • Marubuci, Farouk Chothia
    • Marubuci, Yemisi Adegoke
    • Marubuci, Nichola Mandil
    • Aiko rahoto daga, Juba
  • Lokacin karatu: Minti 6

Fargabar da ake da ita na cewa Sudan ta Kudu - da ta kasance jaririyar ƙasa a duniya - za ta afka cikin gagarumin yaƙin basasa na ci gaba da ƙaruwa yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a jihar Jonglei, da ke arewa maso gabashin Juba, babban birnin ƙasar.

Dakarun gwamnati na koƙarin sake karɓe ikon yankin daga hannun waɗanda ke mubaya'a ga mataimakin shugaban ƙasar na farko Riek Machar, wanda aka dakatar daga mukaminsa bayan zarginsa da yunkurin kifar da shugaba Salva Kiir.

Machar na fuskantar shari'a yanzu haka a Juba, kan laifukan kisa, cin amanar ƙasa da kuma take ƴancin ɗan'adam, sai dai ya musanta zarge-zargen.

Jam'iyyarsa ta SPLM ta yi Alla-wadai da zargin inda ta ce "bi-ta-da-kullin-siyasa ne", kuma yunkuri na "wargaza" yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 da ta kawo karshen yaƙin basasar ƙasar na shekara biyar.

Me yake faruwa a Jonglei?

Jam'iyyar SPLM/A-IO da wasu ƙungiyoyin ƙawancen sun ce suna ta ƙwace yankuna, ciki har da sansanonin soji a Jonglei da kuma sauran jihohi tun karshen shekarar da ta gabta.

Sojojin Sudan ta Kudu sun mayar da martani ta hanyar kai wani mummunan hari a watan da ya gabata.

A wata sanarwa mai cike da cece-kuce, mataimakin hafsan sojoji Janar Johnson Oluny ya buƙaci sojoji da "kada su bar kowa" ciki har da "ƙananan yara, tsofaffi da kuma fararen hula" lokacin da aka aika su zuwa jihar Jonglei.

Gwamnati ta fayyace cewa wannan ba umarni bane, inda ta nanata cewa zimmar ci gaba da kare fararen hula.

Faɗan da ya ɓarke a baya bayan-nan a Jonglei ya tilasta wa aƙalla mutum 280,000 tserewa gidajensu.

An lalata tare da sace kayayyakin da jami'an ba da agaji ke amfani da shi, ciki har da asibitoci sannan an lakaɗa wa ma'aikatan agajin duka, a cewar ƙungiyar agaji ta Oxfam.

Me ya janyo rikicin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sudan ta Kudu da ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta a duniya, ta samu ƴancin kai daga Sudan a shekara ta 2011 bayan faɗa na tsawon gomman shekaru wanda jam'iyyar Sudan People's Liberation Movement ta jagoranta.

Shekaru biyu kaɗai da samun ƴancin kai, yaƙin basasa ya ɓarke lokacin da shugaba Kiir ya sallami Machar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, bayan zarginsa da yunkurin juyin mulki.

Rikicin wanda yawanci ya ta'allaka kan kabilanci tsakanin magoya bayan shugabannin biyu, ya janyo mutuwar mutane 400,000 da tilastawa miliyan 2.5 barin muhallansu - wanda ya kai sama da kashi biyar na al'ummar ƙasar.

A matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya, an sake mayar da Machar kan kujerarsa na mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin haɗin kan ƙasa wadda ake sa ran za ta bayar da dama na yin zaɓuka.

Yayin da rikici na yanzu a Jonglei ya ta'allaka kan adawar siyasa, jihar ta daɗe tana fama da rikici tsakanin al'ummomi da kabilu, musamman ma tsakanin kabilun Dinka da Nuer.

Sai kuma aka ci gaba da samun rikice-rikice da ke alaƙa da sace shanu, filaye, siyasa da kuma hare-haren ramuwa waɗanda suka ƙara taɓarɓara rikcikin na yanzu.

Jam'iyyar SPLM/A-IO na samun yawancin goyon baya daga al'ummomin kabilun Nuer, yayin da ƴan kabilar Dinka suka fi mamaye gwamnati da kuma dakarun ƙawance.

Sakamakon haka ne, rikice-rikice da ke alaƙa da siyasa ke ta da tsohuwar gaba, abin da ke ƙara barazanar yaɗuwar rikicin al'ummomi.

Me ya sa ake zaman fargaba yanzu?

Kiir da Machar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Riek Machar (a hagu) da Salva Kiir (ɓangaren dama) - suna tare tun 2020 - kuma sun kasance abokai a jam'iyyar SPLM kafin a samu saɓani

Rikicin na yanzu ya fara bazuwa ne a watan Maris ɗin bara lokacin da wasu mayaƙa da ke alaƙa da Machar lokacin yaƙin basasa, suka yi artabu da dakarun gwamnati a jihar Upper Nile tare da ƙwace ikon sansanin sojin Nasir,

Sannan ranar 7 ga watan Maris aka far wa jirgi mai saukar ungulu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke koƙarin kwashe sojoji, abin da ya janyo mutuwar dakaru da dama, ciki har da wani babban janar.

Makonni uku bayan afkuwar lamarin, aka yi wa Machar da abokansa ɗaurin talala. An zarge su da koƙarin haddasa tawaye.

"Batun samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu ya sake shiga wani mawuyacin hali," kamar yadda matamaikin shugaban jam'iyyar SPLM Oyet Nathaniel Pierino ya faɗa a lokacin.

Maimakon kwantar da hankali, gwamnati ta sake dagula lamari, inda ta zargi Machar da laifukan cin amanar ƙasa a watan Satumba.

Kwakaki kalilan daga baya, jam'iyyarsa ta sake zabura tare da yin Alla-wadai da gwamnatin Kiir da kuma kiranta "mai kama ƙarya" har ma da buƙatar sauya gwamnati.

Yaya batun yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018?

Yayin da saka Machar cikin gwamnatin haɗin kai ya kasance wani ɓangare na yarjejeniyar, sai dai ba a aiwatar da wasu ɓangarori ba.

Babban kalubale ga Sudan ta Kudu ita ce batun tsarin tsaro.

Yarjejeniyar ta bayyana yadda za a haɗa tsoffin ƴan tawaye da dakarun gwamnati zuwa wuri ɗaya a matsayin rundunar soji wadda za ta kunshi dakaru 83,000. An tsara cewa sauran kuma za a karɓe makamansu da kuma cire su a matsayin sojoji.

Sai dai, ba a yi hakan ba inda har yanzu akwai mayaƙa da dama da ke alaƙa da kungiyoyin siyasa daban-daban.

Yarjejeniyar ta kuma bayyana cewa za a kafa wata kotu tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Tarayyar Afirka wajen hukunta waɗanda suka aikata laifi. Sai dai ba a kirkiri kotun ba, saboda waɗanda ke riƙe da mukaman gwamnati na tsoron kafa abin da zai zo ya hukunta su.

Ba a gudanar da zaɓen da aka tsara yi a 2022 ba kuma babu wani kundin mulki da aka tsara.

Kenya na koƙarin shiga tsakani don farfaɗo da yarjejeniyar zaman lafiyar a yanzu.

Ana fatan cewa za a yi tattaunawa a Kenya da zimmar saka ɗamba na ganin an gudanar da sahihin zaɓuka.

Wace matsala ce ke tsakanin Machar da Kiir?

Kiir da Machar duka sun haura shekara 70, kuma suna cikin gwagwarmayar SPLM da ta samar da ƴancin kai - sai dai sun daɗe suna zaman doya da manja.

Lokacin da Kiir ya tuɓe Machar daga mukaminsa a 2013, abin ya janyo yaƙin basasa, inda Machar ya yi Alla-wadai da Kiir da kuma kiransa "mai mulkin kama ƙarya".

Abin da ya ƙara dagula alaƙa tsakanin mutanen biyu shi ne ɗage lokacin zaɓe da aka yi ta yi.

An ɗage lokacin zaɓe har sau huɗu, inda lamarin ya sa Machar kasa cika burinsa na zama shugaban ƙasa yayin da ake ci gaba da yayata cewa Kiir na son dawwama kan mulki har karshen rayuwarsa.

Wanene Riek Machar?

An haife shi ne a shekara ta 1953, kuma mai shekara 73 ɗin shi ne ɗa na 27 ga sarkin Ayod da Leer, kuma ya tashi ne karkashin koyarwar cocin Presbyterian.

Ya karanci fannin injiniyanci na sinadarai a Jami'ar Khartoum sannan a 1984 ya kammala digiri na uku a ɓangaren falsafa da tsare-tsare daga Jami'ar Bradford ta Birtaniya.

Ya sauya ɓangare a lokuta da dama lokacin gwagwarmayar ɓallewa daga Sudan, yayin da yake koƙarin ƙarfafa matsayarsa da kuma ta kabilarsa Nuer.

Ya zama mataimakin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu a lokacin samun ƴancin kai a 2011.

An kori Machar a 2013 sannan aka sake mayar da shi kan mukaminsa a wani ɓangare na yarjejeniya a 2016, sai dai ya tsere bayan sake ɓarkewar faɗa.

Wane ne Salva Kiir?

An haifi Kiir ne a shekara ta 1951, yana kuma da shekara 74 a yanzu - ya tashi yana zuwan cocin Roman Katolika.

Mahaifinsa ya kasance makiyayi kuma shi ne ɗa na takwas cikin yaran mahaifinsa tara.

Ya shiga ƙungiyar ƴan tawaye ta Anyanya da ke fafutukar samun ƴancin Sudan ta Kudu lokacin yaƙin basasar Sudan na farko a 1967, yana shekara 17.

Shekaru 16 bayan nan - lokacin yaƙin basasa na biyu - shi ne ɗaya daga cikin mutum biyar da suka kafa gwagwarmayar SPLM.

Tsohon shugaban ƴan tawayen, wanda yake da ƙwarewar tattara bayanan sirri, ana kallonsa a matsayin jajirtaccen mutum a tsakanin SPLM kuma ya zama shugaban ƙungiyar a 2005 bayan mutuwar John Garang a wani hatsarin jirgin sama.

Ya zama shugaban Sudan ta Kudu ranar samun ƴancin kai kuma ya ci gaba da kasancewa kan mukamin na tsawon shekara 14 saboda babu wani zaɓe da aka gudanar har kawo yanzu.

Ta yaya al'amura za su yi muni?

A bara, shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu, Nicolas Haysom, ya yi gargaɗin cewa ƙasa na daf da "komawa babbar yaƙin basasar", wanda zai ɗaiɗaita ƙasar da ke ci gaba da farfaɗowa daga rikice-rikicen da suka gabata.

Ana nuna damuwar cewa komawa faɗa zai janyo shigar wasu "ƙungiyoyin mayaƙa a yankin", a cewar wani masani Daniel Akech.

Duk wani irin rikici da za a samu zai haifar da abubuwa biyu, in ji shi. "Na farko, zai ƙara ruruwa rikicin kabilanci... yayin da ɓangarori za su tattara magoya baya da kuma shirya su don gwabza faɗa. Na biyu, ɓarkewar rikici a Sudan ta Kudu zai iya janyo makwabtan ƙasar ciki."

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen yankin wato Igad - ciki har da Uganda - na cikin waɗanda ake ganin za su taimaka wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018.

An aika wasu sojojin Uganda zuwa ƙasar a matsayin wani ɓangare na abin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce daɗaɗɗen yarjejeniya ta taimakawa sojojin ƙasar.

Taswirar da ke nuna Sudan ta Kudu.