PSG ta bai wa Juventus aron Kolo Muani

Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Randal Kolo Muani ya tafi Juventus zaman aro har zuwa karshen kakar nan da ake ciki.

Dan wasan na Faransa mai shekara 26 ya taka wa PSG leda sau 14 a kakar nan, to amma rabonsa da shiga wani wasa tun ranar 6 ga watan Disamba.

Kungiyoyin Premier da suka hada da Tottenham da Manchester United na sha'awar sayen dan wasan.

PSG ta kulla yarjejeniyar shekara biyar da shi a lokacin da ta saye shi daga Eintracht Frankfurt ta Jamus a kan fam miliyan 76 da dubu dari hudu a watan Satumba na 2023.

Muani wanda ya taso a wajen birnin Paris ya fara sanarsa ta taka leda ne a kungiyar Nantes kafin ya tafi gasar Bundesliga da kungiyar Eintracht Frankfurt.

Dan gaban ya kasa gamsar da kocinsu na PSG, Luis Enrique, a bana saboda haka ya ajiye shi.

Ya ci wa PSG kwallo takwas a wasa 27, kuma a 2022 kiris ya rage ya ci Argentina a wasan karshe na cin Kofin Duniya ana dab da tashi.

Juventus ta yi maraba da zuwansa kasancewar tana ganin zai zama karin karfi ga kungiyar ta Thiago Motta a matsayin kwararren dan gaba - a tsakiya ne ko a gefe.