Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane hali gidajen mai ke ciki a Najeriya bayan raguwar masu ababen hawa?
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Gidajen mai da dama sun fara kasancewa fayau a 'yan kwanakin nan tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sake ƙara farashin man fetur.
Lamarin ya janyo wa ƴan ƙasar da dama wahalhalu musamman marasa karfi, a gefe guda kuma masu ababen hawa suka fara ajiye motocinsu saboda tsadar man.
Ko a ranar Talata ma 'yan Najeriya sun wayi gari da sabon farashin man, inda ya koma N1,050 a gidajen mai na kamfanin NNPCL mallakar gwamnatin ƙasar.
Yanzu dai da yawan mutane sun gwammace su hau motocin haya wajen yin zirga-zirga maimakon amfani da motocinsu, inda wasu ma suka gwammace takawa da ƙafa zuwa wuraren aiki ko kasuwanci.
Har wa yau, hanyoyi da aka saba ganin cunskoso a baya a wasu birane sun kasance fayau a yanzu, musamman a Abuja babban birnin Najeriya.
Akwai wasu rahotanni da ke cewa wasu mutane sun koma sayar da motocinsu domin maye gurbinsu da waɗanda ba su shan mai sosai.
'An samu raguwar masu sayen mai da kashi 35 cikin 100'
Yayin da ƙarin farashin man fetur ɗin ke ci gaba da wanzuwa a faɗin Najeriya, masu gidajen na kokawa game da rashin zuwan masu saye.
Sun ce yanzu abin da suke sayarwa bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da baya, lamarin ya sa wasu 'yankasuwa na barazanar rufe gidajen man nasu.
Bashir Ahmad Ɗanmalam, shugaban wata ƙungiyar dillalan man fetur da iskar Gas ta Najeriya, ya ce gidajen mai da dama na cikin wani hali maras kyau a wannan lokaci.
"Tun da gwamnati ta zare hannunta daga ba da tallafin man fetur aka shiga wani hali. Yanzu ana son ƴankasuwa su cika giɓin da gwamnati take cikawa a baya," in ji shi.
Ya ce iftila'in da masu gidajen mai suka fara gamuwa da shi shi ne raguwar jarin da suke zubawa.
"Yanayin jari babu, babu riba, dole ya sa masu gidajen mai ke rufewa. Kuma dole mai ya yi ƙasa, masu shan mai ɗin ma sun ragu.
"Mai jarin mota biyar ya koma [sayen] mota ɗaya, idan ya je ɗaukar mai dole a samu matsala. Wanda ba shi da ko mota ɗaya kuma dole ya rufe gidan mansa," a cewar Ɗanmalam.
Shugaban ƙungiyar ya ce an samu matukar raguwa ta waɗanda ke zuwa sayen mai idan aka kwatanta da baya.
"Idan mutane sun zo sayen mai a yanzu, sai mutum ya bayar da 20,000 kaɗai. A baya idan ka sha na 5,000 ya fi ka sha na 20,000 ko 30,000 a yanzu.
"Idan aka kwatanta da baya a cikin kashi 100, bai fi kashi 35 zuwa 40 ne ke shan mai ba. Abubuwa sun sauya yanzu."
Ya ce akwai gidajen mai a Abuja, babban birnin Najeriya waɗanda da wuya su sayar da ko mota ɗaya a rana a yanzu.
"A nan garin Abuja, akwai gidajen mai da ke sayar da mota biyu a baya, amma yanzu babu wanda ke iya sayar da mota ɗaya.
"Idan ka tafi irinsu Kano ko Legas za ka ga wani lokacin a sayar da mota ɗaya, wani lokacin ma ba za a sayar ba. Har ta kai wasu na kai kwanaki huɗu ko biyar ba su sayar da mota ɗaya ba saboda ga tarin kuɗin amma kayan da aka saya babu yawa," in ji Ɗanmalam.
Ya ce abin da ya janyo matsalar shi ne raguwar kuɗaɗe a hannun jama'a saboda halin matsi da ƴan ƙasa ke ciki.
'An samu raguwar yawan mai da ake shiga da shi'
Bayanai da hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta fitar, ya nuna cewa an samu raguwar yawan mai da ake shigar da shi Najeriya a 2023, wato shekarar da aka cire tallafin man fetur.
Alkaluman da hukumar ta fitar a watan Satumban 2024 sun nuna cewa man fetur ɗin da aka shiga da shi Najeriya a 2023 ya ragu zuwa lita biliyan 20.30 idan aka kwatanta da 23.54 da aka shigar a 2022.
Hakan na nufin an samu raguwar kashi 13.77 cikin 100 na man da aka saba shiga da shi.
Hakan ba zai rasa nasaba da yadda masu ababen hawa da masu ƙananan sana'o'i suka fara sauya injinansu zuwa masu amfani da iskar gas ɗin CNG da AGO ba.
Abin da cire tallafin man fetur ya jawo
Tun a ranar shan rantsuwar kama aiki, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur.
Shugaban ya ce ya ɗauki matakin ne domin magance matsalar ƙarancin mai, da zargin karkatar da shi don yin fasa-ƙwaurinsa zuwa ƙasashe maƙwabta.
Sai dai, janye tallafin wanda shugaban na Najeriya ya sanar a jawabinsa na kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, ya jefa 'yan ƙasar masu yawa cikin mawuyacin hali saboda hauhawar farashi.
Shugaba Bola Tinubu dai ya ce matakin cire tallafin man fetur ɗin ya zama dole, wanda ya janyo tsada da kuma dogayen layuka a gidajen mai da ke faɗin Najeriya.
Sakamakon haka, a farkon watan Satumba kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya sanar da ƙarin farashin litar man daga naira 617 zuwa naira 897 a Abuja kan kowace lita ɗaya.
Ya sake yin ƙarin kuɗin har sau biyu a watan Oktoban 2024: farko zuwa N1,030 a Abuja ranar 9 ga wata, sai kuma a ranar 29 ga watan ya mayar da shi 1,050.
Sabon ƙarin kuɗin man shi ne na huɗu tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.