Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane tasiri zare hannun NNPCL daga dillancin man Dangote zai yi ga ƴan Najeriya?
Da alama tsugunu ba ta ƙare wa 'yan Najeriya ba game da tsadar man fetur sakamakon matakin kamfanin mai na NNPCL na zare hannunsa daga dillancin fetur ɗin a matatar mai ta Dangote.
Wata majiya daga NNPCL ta tabbatar wa BBC cewa kamfanin ya zare hannunsa a matsayin mai shiga tsakanin 'yankasuwa da Dangote bayan yarjejeniyar da suka ƙulla tun a watan Agusta.
Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa NNPCL ne kaɗai zai dinga sayen man Dangote, inda su kuma 'yankasuwa za su saya a hannun kamfanin.
Masana harkokin man fetur sun ce an yi hakan ne da zimmar daidaita farashi, abin da ake fargabar a yanzu ba zai yiwu ba da zarar 'yankasuwa sun fara sayen man kai-tsaye daga matatar Dangote.
A watan Satumba ne NNPCL ya ƙara farashin litar man daga N617 zuwa N897 tun kafin ya fara sayen man daga Dangote, yana mai cewa yana fama da ƙarancin kuɗi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kare matakin da wanda "ya zama dole saboda a samu kuɗaɗen gina ƙasa", kodayake ya amince cewa hakan na jawo tsadar rayuwa ta hanyar hauhawar farashi.
Rahotanni sun nuna cewa tuni NNPCL ya sanar da gwamnatin Najeriya cewa ba zai samu damar biyan wasu haraje-haraje ba saboda kuɗin da yake kashewa wajen sauƙaƙa farashin man ga 'yan ƙasa - wato tallafin mai a taƙaice.
A madadin haka, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince wa kamfanin ya yi amfani da kason da ya kamata a ba ta na ribar da aka samu wajen sayar da man a rabin farashinsa da NNPCL ɗin ya kamata ya sayar wa 'yan ƙasa.
'Zai iya jawo tashin farashin mai'
Ɗaya daga cikin fargabar da 'yan Najeriya suka fi yi a yanzu ita ce duk wani abu da zai jawo ƙarin farashin man fetur saboda yadda kusan komai ya ta'allaƙa da shi.
Masu sharhi game da makamashi na cewa gwamnatin Bola Tinubu na yin iya bakin ƙoƙarinta wajen raba kanta daga biyan duk wani nau'i na tallafi a fannin man fetur.
"Gwamnati ta lura cewa idan NNPCL ya ci gaba da shiga tsakanin 'yankasuwa da matatar Dangote har yanzu kenan akwai wani tallafi da take bayarwa," a cewar Injiya Yabagi Sani - wani masanin makamashi a Najeriya.
Ya ƙara da cewa tasirin wannan mataki ba wai ƙarin kuɗin mai zai jawo kawai ba, har ma da sauran kayayyaki.
"Farashin mai zai yi sama kuma ya jawo hauhawar farashin kayayyaki kamar na abinci, wanda matsalar za ta ci gaba da shafar 'yan Najeriya."
A cewarsa, matatar Dangote ta 'yankasuwa ce saboda dole ne ya sayar da man kan farashin da zai ci riba. A taƙaice dai idan farashin ya tashi a duniya shi ma Dangote zai ƙara farashi.
Kazalika, matakin na NNPCL zai sa 'yankasuwa saka farashi daban-daban, abin da masanin ke ganin za a iya samun alfanu daga hakan.
"To kuma yana iya yiwuwa a samu sauƙi. Saboda da ma farashin yana hawa ne yana sauka a kasuwar duniya."
Ko sayar wa Dangote ɗanyen mai a naira zai taimaka?
A ƙarshen watan Yuli ne Shugaba Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da cinikayya tsakanin NNPCL da matatun mai na cikin gida a naira, inda za a fara da ta Dangote.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ya fitar ta ce matatar Dangote na buƙatar jiragen ruwa 15 kan dala biliyan 13.5 duk shekara amma NNPCL zai samar mata da huɗu daga ciki.
Ya ƙara da cewa za a ƙayyade farashin canji tsakanin naira da dala a tsawon lokacin gudanar da wannan cinikayya. Sai dai sanarwar ba ta fayyace har zuwa yaushe za a ci gaba da yin cinikayyar a naira ba.
Yabagi Sani ya ce indai za a ci gaba da yin hakan to tabbas zai taimaka wajen rage hauhawar farashin man.
"Amma idan aka ce za a sayar wa Dangote man da naira a kan farashin canjin da ake amfani da shi a lokacin, to ba ta sauya zani ba kenan, za a ci gaba da samun tsadar mai a kullum," in ji shi.