Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin gasa ake yi tsakanin Dangote da NNPC kan farashin fetur a Najeriya?
Kamfanin man fetur na Najeriya ya sauke farashin litar man fetur a gidajen mansa ke faɗin Najeriya kwanaki bayan matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man a gidajen sayar da mai masu alaƙa da ita.
Ɗaya daga cikin manyan dillalan man fetur a Najeriya ya tabbatar wa BBC cewa a yanzu "NNPC na sayar muna da man fetur ne kan naira 840 a Legas, sai kuma naira 875 a Calabar da kuma Fatakwal."
Hakan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man, inda mutanen Najeriya ke sayen fetur ɗin cikin farashin da ya yi ƙasa da na NNPC a gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar.
Wannan ya sanya aka riƙa ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen man fetur ɗin da ke da alaƙa da matatar ta Dangote.
Farashin da Dangote ya sanar zai riƙa sayar wa dillalai abokan hulɗarsa shi ne naira 825 daga 890, ragin naira 65 ke nan kan kowace lita.
Karo na biyu ke nan kamfanin yana rage farashin man a watan Fabrairun 2025, abin da dillalan man suka bayyana da "abin a yaba".
Rage farashin ya sa man na Dangote ya zama mafi rahusa idan aka kwatanta da wanda ake shiga da shi ƙasar daga ƙasashen waje.
Sai ga shi a ranar Litinin an ga raguwar farashin man fetur ɗin a wasu gidajen man fetur da ke da alaƙa da NNPC a faɗin Najeriya.
Duk da dai kamfanin NNPC bai fitar da sanarwa kan rage farashin man fetur ɗin nasa ba, to amma masu amfani da ababen hawa sun riƙa sayen lita ɗaya kan farashin naira 880, wanda hakan ragi ne kan tsohon farashin na naira N965.
Kamfanin ya ce yana sassauya farashin nasa ne domin ya yi daidai da abin da kasuwa ta bayar.
Tun bayan cire tallafin da gwamnatin ta yi a ɓanagaren man fetur na Najeriya farashin litar fetur ya yi tashin gwauron zabi.
Lamarin ya kai ga cewa farashin da ake sayar da lita ɗaya ya nunka fiye da sau biyu jim kaɗan bayan sanarwar da shugaban ƙasar ya bayar a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Tun daga wancan lokacin ne farashin ya ci gaba da hauhawa, yayin da aka samu lokutan da aka samu ya samu ragi ƙalilan.
Sai dai tun bayan fara aikin matatar man fetur ta Dangote, lamarin ya fara sauyawa, inda attajirin mai kuɗin ya riƙa rage farashi a baya-bayan nan.
Gasar rage farashi?
Matatar Dangote ta fara rage farashi ne a daidai lokacin hutu na watan Disamban 2024, inda ta rage naira 70.50 - daga N970 zuwa N899.50.
Shi ma kamfanin mai na NNPC ya rage nasa farashin zuwa daidai da na Dangote; daga N1,020 zuwa N899.
Sai kuma a ranar 1 ga watan Fabrairu, inda da ta bayar da sanarwar rage farashin da naira 60.00 zuwa N950 kan kowace lita ɗaya.
Kamfanonin da ke safarar tataccen mai daga ƙasashen waje zuwa Najeriya kan yi hakan a kan naira N927, bambancin naira 102 ke nan.
Sai kuma ragi na baya-bayan nan da matatar Dangote ta sanar a ranar 26 ga watan Fabarairun 2025, inda ta sanar da rage farashin man fetur da take sayarwa da naira 65.
Inda farashin ya sauka daga naira 890 zuwa 825 a kan kowace lita.
Daga nan ne kuma a farkon watan Mayu aka fara ganin gidajen sayar da man fetur masu alaƙa da NNPC sun rage farashinsu zuwa kimanin 880 a wasu yankuna na arewacin Najeriya.
A birnin Legas kuwa farashin na kamfanin NNPC ya koma zuwa kimanin naira 865.
Dama dai masana sun bayyana cewa ɗaya daga cikin alfanun da Najeriya za ta samu bayan cire tallafin man fetur shi ne gasar da za a riƙa yi tsakanin ƴan kasuwa, wanda hakan zai rage farashin man fetur ɗin.